← Book details Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 35

Sashe 29

Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dariya na yi na ce.'' Ka raina wannan sana'ar da nake yi kenan, wallahi da ita na saya domin neman lada."
Ya hade fuskarsa. " Gaskiya ban yarda ba, idan kin sayi wani abu da kudinki, to za ki ta'ba nawa da nake ajiye muku idan kin yi hakuri ma ai duk shekara ina fitarwa da surukaina abin bud'e baki."

Cikin zuciyata na ce' an zo wurin' Zuciya ba ta da 'kashi zaman da ya yi, sai da na hasashi zargi a fuskarsa.
Na ce." To, Allah ne dai shahidi kuma shine zai yi mana hisabi bisa zargin da ka yi mini, ba zan yi rigima da kai a wannan watan ba, amma na barka da Allah ."
Daga haka ban sake magana ba, na d'auki almakashina na cigaba da aikin gabana.
Jikinsa a sanyaye ya tashi ya fita bai sake ce mini komai ba.
Duk yadda na so na daure zuciyata na cigaba da kyautatawa mutumin nan kasawa na yi. Da na kalleshi zan ji haushinsa ya turnukeni. Zama fa kawai nake yi dashi, har yanzu ba na jin sonsa a raina amma shine yake ko'karin gaya mini magana.
Ya dinga raragefe neman shiri, na share shi, da kyar ya shawo kaina na ha'kura na sakar masa jiki yana ta fad'in shi fa ba zargina yake ba, kawai su'btar baki ce ya yi.....✍️
*Gudun aure 1k on talgram via 0542382124...Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*

*TALLA!*
🌲🌳🌿☘️
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
[11/27, 10:17 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A*

TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay
*TALLAH!*
🛍️ “Ko ba ki da niyyar siya ba, ki zo ki shiga ki kalla kayayyaki — wallahi sai kin bude ido! Ballantana kuma nasan za ki tashi da kaya saboda kyau da araha.” ✨
🌸✨ “Shigo duniyar da kyau da jin daɗi suka haɗu — daga kyawawan laces na alfarma, Atamfa , abaya masu salo, zuwa kayan ado masu kyalli, kayan girki na zamani da sauran ƙarin abubuwa. A Meerah B Collection , muna adashen kayan kitchen daily 1k to pack 100k items weekly Monthly ✨🌸We are sale kitchen items, electronic, WE ALSO DEAL WITH CONTRIBUTE monthly weekly daily after 10 days for kitchen items or electronic gaba daya wanna package 60k nake had'a sa zaku iya mallaka ta hanyar adashi
https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t

*1k on talgram via 0542382124...Binta Umar gtbank mutanan nijar dala dari katin Airtel. Ga masu karatu a arewa book akwai more peges domin na yi nisa a can din.*
*07084653262*
*08089965176*
*@arewa books*
*Bintuumarabbale.*
*Free pege*
*18*
Wannan ya wuce da wasu kwanaki wani abu bai sake faruwa ba, tunda Ina iyakacin bakin kokarina wurin ganin na fita hakkin maigidan da abokanan zamana a duk ranar girkina. Sosai Yusura take taimaka mini da wasu ayyukan, itama Iyami tana nata bakin ko'karin. Goman karshe hada-hada ta yi yawa. Ya Falmata ta sake jibgo mini wasu ayyukan tare da sharad'in ana buk'atarsu kafin sallah. Babu abinda nake hangowa sai ruwan kudin da zan samu. Wannan dalilin ya sanya na hana kaina sukuni bacci arziki ba na yi. Yanzu haka kekuna biyu gareni ni na hau daya Yusura ma ta hau tunda ta fara iya wasu abubuwan ina nuna mata. Kamalu da Yusi suna aikin jera stone's da sauransu.
Ranar girkina kuwa Iyami na sakarwa ragama duk da na san da cewa ba haka tsarin gidan yake ba. Iyakacinta shara da wanke-wanke, sai zuwa cefena da 'yan aike aike, amma ni kam har girkina na bar mata, muka yi da ita zan dinga bata dubu biyu kullum idan zata tafi. Ita kuma Yusura la'asar ta na yi zan tashe ta ta je ta feraye doya ta soya ita na dorawa alhakin hakan.
Anti Maimuna ba ta ta'ba tankawa ba ila iyaka idan an kammala ta zo ta dibi abinci. Babu korafi a tsakaninmu tana dannewa koda taga abinda bai yi mata ba, gashi dai itace uwargida amma bata neman fitina da kowaccen mu, dalilin da ya sanya ma kenan na sayi shadda mai tsada yadi goma sha biyar na bada yadi bakwai a dinkawa Kamalu da Yusi sauran Kuma nake da kudirin yi musu d'inki na gani na fad'a ita da Yusura duk da cewa maigidan ya yi musu kala uku Yusura da su Kamalu bai bambamta da yaransa ba, hakan ya sake ba ni karfin guiwar yi wa 'yarsa duba da irin kara da kawaicin da uwarta take yi mini, uwa uba kuma yarinyar tana kaunar Yusi sosai, komai ka ji tace Yusifa.

Yau bayan shan ruwa da kadan ina bandaki na ji sautin muryar Jamila a falona.
Da sauri na cud'a jikina na zuba ruwa na fito. A gurguje nake yi komai dalili girkina ne, ba na so kuma maigidan ya shigo ya riskeni a hargitse, dama na fahimci kwana biyu a wuya yake da ni, dalilin baccin da yake riskata ina yi bayan ya gama zaman majalisarsa ya shigo, duk ranar girkina baya samun wani Abu a wurina saboda mugun gajiyar da nake yi. Shiyasa yau na sauka daga kan keke da wuri domin ina so na faranta masa.
Tana tsaye sai fad'a take yi wa Yusura. Ita kuma yarinyar ta yi shiru idonta ya ciko da hawaye. Raina ya baci ainun. Na ce." Ke kuma menene haka don Allah za ki tasa yarinya a gaba kina fad'a mata wasu maganganu ko zamanki take yi ne a gidan?"
Ta kalleni kafin ta ce." Amma dai kin san abinda ki ke yi ba kya kyautawa, ya za a yi ki dinga bawa wannan yar yarinyar aikin da bata iya ba, idan ita Maimuna ba zata iya yi miki magana ba to wallahi ni ba ki isa ba, ba zai yiwu mu dinga cin abu da 'karni ba, domin koyaushe doyar da yarinyar nan take yi ba ta soyuwa zubarwa muke yi ni da yara, wallahi ba zai yiwu ba dole maigidan ya ji abinda yake faruwa domin tun wuri ya yi wa tufkar hanci."
Na ce." To sai ki bi shi ki gaya masa ai yana waje ba nisa ya yi ba, idan ya shigo sai ki sanya ya sake ni, ko ya kori Yusura tunda ta soya doya ba ta soyuwa ba."

Ta bude baki kenan za ta yi magana ya shigo. Ganinta a tsaye ya sanya ya ce." Da azimin ma sai kun yi mini masifa a gida, menene kuma?"
Chapter 29 · 0% Book details