← Book details Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 35

Sashe 10

Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

*@Arewa books*
*Bintuumarabbale.*
*Free pege*
*7*
Ko da na shiga gidan zaman minti biyar ban yi ba. Baba ya shigo yana fad'in." Kin je kun zanta to? Na fad'a miki da gaske yake, ina fata kun fahimci juna."
Na ce." E, to Baba mun gaisa dai, amma fahimtar juna ai sai a hankali tukkuna, ina so ne komai a tafiyar da shi cikin nutsuwa Baba gaggawar auran sai ya haifar da d'a mara ido."
Ya ce." Ki dinga kyautatawa kanki zato na alheri Amina, wannan mutumin na yarda dashi d'ari bisa d'ari, domin duk wanda zai bude baki zai fad'i alherisa."
Shiru na yi ban ce komai ba. Ya juya zai fita yana cigaba da jaddada maganar. Na ce." Baba d'azu anti Yagana ta kira waya."
Ya juyo da sauri yana ce wa." To, to Ina fatan dai lafiya?
"Bikin Babandi ne ya tashi sati mai zuwa shine tace na gaya maka ko zaka samu zuwa d'aurin aure, ni ma zan yi kokarin halarta tunda an yi hutun makaranta."
Ya ce." Zan je mana Amina muddin za ki yi mini kud'in mota me zai hana ni zuwa."
Murmushi na yi na ce." To Baba zan yi maka kud'in mota sai ka zauna cikin shiri."
Ya ce." Idan da kara itama Murja ki yi mata kudin motar mana sai mu ruguntsuma mu tafi tare."
Na ce." Baba idan na biyawa Ummansu Hadiza kud'in mota hakan zai haddasa maka rikici, Ummansu Saminu za ta nuna rashin jin dadinta akan hakan, kawai dai mu tafi mu biyun."
Ya ce." Hakane kuma, to babu damuwa Allah Ya nuna mana."
Na amsa da '"Amin." Shi kuma ya juya ya fita daga d'akin.
Na dubi shimfid'ar yaran nan ga Kamalu a kwance kusa da d'anuwansa. Na girgiza kaina, wato tsoron shigowa yake yi sai da ya tabbatar da na fita tukkuna.
Na so a daran na rage d'inkunan mutanan da yake hannuna, amma damuwa da zullumin da nake ciki suka hanani katabus. Na yi zaune ina ta tufka da warwara akan lamarin da yake fuskanto ni. Na sake lissafa kudin da ya ba ni dubu goma sha uku ne, domin duntso su kawai ya yi daga aljihu bai lissafa ba ya mi'ko mini sabbi kar dasu.
Mutumin nan da gaske yake aurena zai yi. To ni ba na hangen wadatarsa yadda rayuwar aurana da shi za ta wakana nake nazari. Ya ce yana da yara shin matansa nawa? wannan amsar dole tana wurinsa. Ya zanyi rayuwa a cikin gidansa da marayun yarana? Wace rayuwar zasu fuskanta. Wannan tunanin shi ya dami k'wa'kwalwata. Dukda Babanmu ya ce na dinga yi wa kaina zato na alheri. Amma ya zama dole ne na yi wannan nazari.
Na dubi agogon da yake kafe a d'akin d'aya saura na dare. Gidan ya yi tsit. Na d'auki buta a nutse na fita Ina hirji. Na dauro alwala na ke'bance wuri d'aya domin kai wa Ubangiji kukana. Na jima Ina rok'onsa da ya kawo mini d'auki a rayuwata. Ya yi mini za'bi na gari. Na ninike daddumar cikin nutsuwa na shiga cikin net din yaran, na sanya a hannuna a cinyarsa na dan buge shi, ina kiran sunansa.
Firgigit ya tashi zaune Hakan ya tabbatar mini da cewa dama bacci da yake yi rabi da rabi ne, a tsorace yake yi. Sai hawaye shaaa! suka fara bin kuncinsa. Na ri'ke hannunsa da yake ta rawa yana so ya fita daga cikin net din. A hankali na ce.'' Babu abinda zan yi maka Kamalu, ka samu nutsuwa tambayarka kawai zan yi, ga gaya mini gaskiya, idan kuma ka yi mini 'karya da kaina zan kai ka hukuma, idan sun hukuntaka sai na kira Hamusu ya zo ya tafi da kai tsangaya almajiranci."
Hawayensa suka tsananta zuba. Ya had'a hannuwansa wuri d'aya yana fad'in." Mamanmu ki yi hakuri don Allah."

A hankali saboda ina gudun kada sautin maganarmu ya fita. Na ce." Tona mini asiri za ka yi ko? me na yi maka kake kuka Kamalu, ni ce fa zan zubar da hawaye, amma ban zubar maka ba. Kana so mutanan gidan su ji abinda yake faruwa tsakanina da kai kenan?"
Ya girgiza kansa alamun "A'a.
Na ce." To maza goge hawayenka ka nutsu sai mu yi magana."
Ya goge hawayen tare da rungume gwiwarsa da hannuwansa.
Na dube shi cikin nazari da tsantsar tausayi da fargaba. Na ce." Bayan kun ci abinci a gidan Gwaggwo da ka fita Ina ka je?"
A sanyaye Ya ce.'' bayan mun ci abinci sai Gwaggwo tace mu yi sallah. Bayan mun idar sai na ga tana gyangyad'i shine na fita. Ina tsallaka titi na ga Saminu ya ce na'ibawa zai je tsinto lemo ya siyar shine na bi shi muka tafi tare."

"Kun tsinto lemon kenan?"
"E, mun tsinto, amma ni ba'a sayi nawa ba wai duk ya ru'be ya lalace, shi kuma Saminu an sayi nasa amma ba duka ba shima akwai rub'abbu a ciki, ya samu d'ari shida, shine ya ba ni dari biyu."

Na ce." To ya aka yi aka ganka za ka 'kwacewa Yara kudi an aike su auno shinkafa, Kamalu na yi maka sheda ko ni baka d'aukarwa kud'i idan ka gansu na ajiye, a garin yaya ka ke ko'karin jefa rayuwarka cikin wannan halin. Sata fa Kamalu kasan illarta kuwa?''
Hawaye ya kwaranyo masa ya ce." Saminu ne ya ce mini na je na k'wace musu sai mu raba, amma wallahi ban ta'ba yi ba Mama."
Na zuba masa ido cikin nazari na ce.'' Kada ka yi mini 'karya fa Kamalu, ka san halin Saminu idan ya ji ka yi masa sharri ba zai yarda ba."
Ya ce." Wallahi Mama shine ya tura ni. Shi yana samun kud'i sosai, haka yake yi, ko a makaranta sai an fita break idan wasu sun bar jakarsu sai ya je ya yi ta bincike idan da kudi ya d'auka idan babu sai ya kwashi littafai da biro. Muna tashi sai ya je ya sayar.

Idona ya ciko da ruwan hawaye na yi kokarin dannesu saboda ba na son zubar masa dasu saboda kada masifar ta yi mana yawa ni dashi. Cikin wayo na ce." Yana baka kudin ne?"
Ya ce." E, yana ba ni wataran kuma baya ba ni, amma dai idan mun je makaranta yana saya mana abubuwa."
Chapter 10 · 0% Book details