← Book details Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 35

Sashe 16

Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shi kuma Babanmu kamar sammatace a lokacin baya ganin kowa da mutunci sai Ummansu Hadiza. Domin Iya mahaifiyarsa ma ta rasa gane kansa. Ta je gidan Gwaggwo akan Mamanmu ta koma dakinta. Gwaggo ta ce idan mijin yana buk'atar cigaba da zama da ita ya zo a samu sasanci.
Ashe Baba Sule ne yake zuga shi akan kada ya je ya rabu ma da auran Mamanmu gabad'aya tana da farar kafa ba zai ta'ba cigaba ba. Auran Murja wato Ummansu Hadiza shine alheri a tare dashi tunda yayar matarsa ce, kuma gidansu akwai arziki na dukiya da kuma na haihuwa.
Babanmu ya yarda da maganar d'an'uwansa. Ya jingine Mamanmu a gidan Gwaggwo ita ba mai aure ba ita ba mara aure ba.
Lokacin da Gwaggo take yun'kurin sanar da su Dada halin da ake ciki a lokacin Mamanmu ta dinga wani irin ciwon kafa babu tafiya sai rarrafe.
Gwaggo ta aika aka sanar da Babanmu halin da ake ciki. Ya ki zuwa tunda a lokacin ma har an d'aura aure ya tare da matarsa a daya daga d'akunan dake cikin gidan.
Gwaggo ba miji ne da ita ba, ya rasu shekaru kusan biyar kuma ya bar mata marayu hud'u itace take d'awainiya dasu a lokacin inda Allah Ya rufa asiri tana 'Yan sana'oi na hannu a lokacin shiyasa asirinta yake a rufe. Haka ta yi ta jigila da Mamanmu asibiti akayi gwaje-gwaje likita ya tabbatar da ciki na wata shida kuma har ya juya shine sakamakon ciwon kafafun da take yi.
Ba a mamaki da ikon Allah amma lamarin ya bawa kowa mamaki. Gwaggo ta sanya aka kira babamu a karo na biyu yaki zuwa. Sai ta shirya ta nufi shagonsa anan ta same shi da maganar ta kuma nuna masa sakamakon a rubuce.
Ya tsorota sosai kuma ya yi mamaki da ikon Allah jikinsa ya mutu ya gaza had'a ido da Gwaggo ya dinga kame-kame Yana ko'karin kare kansa. Gwaggo ta ce to tunda haihuwa ce matsalar sai ka zo ka d'auki matarka ka kuma ji tsoron Allah ka yi adalci da ni da kai duka amana aka ba mu. Ta kamo hanyar gida ta bar shi da alhini.
Baba Sule ya so ya zuga shi domin ya firje ya'ki amincewa da cikin akan ba nasa ba ne. Babanmu ya ki yarda da shawararsa saboda shi yafi kowa sanin yadda ya sami matarsa.

To ashe haihuwar ra'kuma daga babamu ne. Domin itama Ummansu Hadiza duk da take bazawara kuma ta haihu a wani wuri ba daga shigowarta ta haihu ba sai da Mamanmu ta haifi anti Yagana da shekara biyar tukkuna Ummansu Hadiza ta samu cikin d'anta na fari, kuma cikin ikon Allah da ya ta haife shi kwana biyu Allah Ya kar'bi abinsa. Ta dinga kuka tana cewa Mamanmu ce ta 'kona shi da ruwan zafi tunda a lokacin da ya rasu Mamanmu ba ta jima da yi masa wanka ba.

Dama zaman doya da manja suke yi. Mamanmu tana dannewa ne a matsayinta na Uwargida. Kada ace ita ce bata k'aunar zaman lafiya. Amma dai duk da haka watarana idan Ummansu Hadiza ta kai ta bango fitowa take yi su yi ta cacar baki. Tana da ha'kuri a wasu lukutan. Amma ba ta son raini. Shiyasa anti Yagana take fad'in halinmu daya da ita na rashin san wargi.

Kusan lokaci daya aka samu cikinmu ni da Hadiza a yadda Ummansu Hadizan take ba mu labari tare suka dinga laulayi har Allah ya kawo lokacin haihuwar tazarata da Hadiza ta kwana tara ce. Ita aka riga haihuwa sai ni. A lokacin ita an yi mata hakika da tinkiya katuwa. Ni kuwa Babanmu ya ce bashi da kudi sai dai Mamamu tayi ha'kuri tunda ya yi mata na fari.
Mamanmu ta dinga kuka tana fad'in ba ta yarda ba ai 'yar sunna ce, yadda aka yankawa kishiyarta tinkiya itama sai an yanka mata. Shi kuma ya ce Ai ba dole ba ne, shi dai ya rad'awa 'yarsa suna Amina. Kamar yadda ya rad'awa 'yarsa Hadiza.
Can gidansu Mamanmu da suka ji labari abin bai yi musu dadi ba ko kad'an. Da yake Dada tana kiwon akoyiyi sai tasa aka yanka guda daya. Aka soye tsaf da zasu zo duba ni suka kawo mata da sauran abin buk'ata.
Dukda haka abin bai saki Mamanmu ba, domin bambamci ko a kayan barka sai da Babanmu ya nuna na Hadiza sun fi yawa ni kuma nawa kad'an. Da ta yi magana ya ce ai ita ya yi mata ba fari.
Wannan abin ya dinga haddasa rikici a gidan. Babanmu daga ya d'auko hanyar gyara idan ya gane kuskuransa sai Baba Sule ya rusa. Ya d'ora shi a wata hanya ta daban.....✍️
*1k on talgram via 0542382124..Binta Umar gtbank*
*07084653262*
[11/20, 1:17 PM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A*

*TALLAH!*
Albishirinku mata 'Yan gayu yan gwalisa kuyi maza kugar zayo shagon
(Aysha/Addah beauty saloon and spa).
Shin kintaba zuwa ingancaccen saloon din Aysha/Addah, idan baki taba zuwa ba kiyi maza kar a barki a baya domin sun qware a wajen aikinsu Wanda suke services dinsu cikin sauki tare da annasuwa
Suna wanke kai(wash and set)
suna wanke qafa(pedicure)
And sunayin steaming iri iri suna saida (supplements)suna kitso dama duk wani abu daku so Wanda akewa mace ta amsa sunanta mace yar qwalisa
Address dinsu nanan a Federal low-cost opposite open University gombe state
Ko kuma ku tuntune mu a wannan number kamar haka,
08037925676
Or
08167764242
Whatsapp ko kuma Call we’r available 24/7..

*@Arewa books*
*Bintuumarabbale.*
*free pege*
*11*
Sanyin halin Babanmu shine ya sanya Baba Sule yake yi masa kutse a cikin duk al'amuransa . Kwata-kwata Allah bai had'a jininsa da Mamanmu ba tunda ta zo gidan gaisuwar kirki ba ta had'a su ba. A wasu lukutan ma sai ya zo ya yi abubuwansa ya fita bai kulata ba kuma tana a matsayin matarsa d'an'uwansa ciki daya sai dai ita take ture komai ta gaishe shi. Idan kuma 'yan miskilancin suna kusa da ita kuma sai ta share shi har ya gama abinda ya kawo shi gidan ya tafi yana habaice habaice sai ka ce wani mace.
To irin wad'annan matsaltsalun su Mamanmu ta dinga ajiyewa a ranta har ya haddasa mata ciwon zuciya wanda shi ya zama ajalinta duka ba a ankara ba, ta dinga ciwo a tsaitsaye har sai da ta fara kumburi tukkuna Baba ya farga suka nufi asibiti likita ya tabbatar da cewa zuciyarta ce ta ta'bu. Gwaggo ta shiga rudu sosài don har Mamanmu ta ma ta fita dauriya, ita ta dinga tausarta. A lokacin shi ma babamu ya tsorota sosai ya mayar da hankali wurin nemo mata magani na gida dana asibiti. Ya nemi alfarmar gwaggo akan kada ta sanar da gidansu halin da ake ciki.
Kulawar da take dan samu dalilin ciwon sai Ummansu Hadiza ta sanya kishi a ciki. Itama koyaushe sai ta kirkiri ciwo ta kwanta tace bata da lafiya. Haka babamu ya zama kamar zautacce a wancan zamanin ga rashin kwanciyar hankali daga cikin gidansa ga neman abinda za a ci.
Lokacin muna da shekara takwas a duniya. Ni da Hadiza tare muka tashi cikin ikon Allah suka sake samun ciki a lokaci daya. Abin ya had'ewa Mama laulayi da ciwonta da yake tashi a sa'i da lokaci don dai ma Gwaggwo da Babanmu a tsaye suke akanta duk inda suka ji magani mussaman na hausa suna ko'karin saya mata. Kuma idan an jarraba ana dacewa. Sai dai idan kwana ya kare babu yadda za a yi. Mamanmu ciwonta ya tashi da zafin gaske ga ciki na wata biyar a jikinta.
Suna zuwa asibiti aka bata gado lokacin ma ba ta gane wanda yake kanta.
Kwana biyu 'yan gidansu suka zo, domin duk abinda yake faruwa babu wanda ya sani a cikinsu. Gwaggo ganin yadda abin ya yi tsanani ya sanya ta sanar dasu. Wani d'anuwan Dada da yake da rufin asiri ya bada umarnin a d'auketa a kaita babban asibiti zai biya kudin da duk abinda aka buk'ata. Babu rabon shan wahala da asara rai ya yi halinsa a lokacin da ake yin cuku-cukun. Mamanmu ta rasu da cikin a jikinta a daran alhamis aka kaita Juma'a da safe.
Alokacin da kuruciya ban fahimci mutuwa ba. Ni dai kawai na daina ganinta idan na tambayi Gwaggo sai tace mini ai ta tafi saudiya.
Da aka share makoki Dada ta bukaci da Baba ya ba ta ni, tunda ni ce karama. Ummansu Hadiza ta ce a bar mata ni din za ta had'a ta ri'ke mu tare 'yarta idan an d'auke ni Hadiza ba za ta ji dadi ba.
Ganin yadda ta nuna damuwarta akan hakan ya sanya Babanmu ya ce Dada ta yi hakuri ta d'auki anti Yagana idan ya so ni sa'i da lokaci sai a dinga kaini garin muna gaisawa.
Haka kuwa akayi suka tafi da anti Yagana tana kuka Ina kuka haka muka rabu. Gwaggo ta rungume ni tana cewa na yi hakuri za a dinga kaini lokaci zuwa lokaci.
Chapter 16 · 0% Book details