Sashe 19
Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
'Bangaran Gwaggwo ma tana yi mini alheri sosai. Hakan nan Yaya Aminu wannan d'ari biyun da tun ina 'karama ya kafa mini adashinta yana ba ni a duk lokacin da za mu had'u.
Tafiya ta mi'ka a cikin sha'anin auran Hadiza matsaltsalu suka fara kunno kai. Ashe da manufar da ya aureta,
yana so ya mori kuruciyarta ne ba don ya haihu da ita ba. Matansa biyu na gida sun haifa masa yaran da ya 'kayyadewa rayuwarsa. Daga zarar ta samu ciki sai ya zubar dashi. Wannan shi ya fara kawo musu matsala wadda tun tana nuku-nuku har dai ta zo gida ta fad'a tana kuka, duk garin jikin nan babu ta rame saboda fargaba. Ta ji labari an ce yawan zubar da ciki ya janyo cancer da raunanar mahaifa, kuma dai zahiri itama tana so ta haihu. Suka dinga fa'di tashi a boye. Ummansu na yawon gidan malamai domin nemo mata taimako a juyo da hankalinsa. Amma a banza, idan ta yo yajin ta dawo gida baya zuwa biko da 'kafafunta take komawa dakinta.
Babanmu kuma ya ce ba zai iya ba, dama can sune suke son auran, idan ba zata iya zama ba ta nemi saki. Ko ta sanar da Baba Sule waliyyanta. Shi kuwa Baba Sule da ya ga lamarin ya kwa'be ya dinga zamewa yana fad'in sabogogi sun yi masa yawa amma zai samu Alhajin su tattauna akan matsalar. Hadiza ta dinga rama a tsaitsaye duk wannan jiji da kan babu saboda babu kwanciyar hankali a gidan mijin, domin da ta daina bin umarninsa akan yadda yake so sakinta ya yi ta zo gida da takardar tana kuka. Satinta biyu a ka samu daidaito ta koma, ta cigaba da zama. Sai ya kasance koyaushe Ummansu sai ta fita kuma ba ko'ina take zuwa ba sai neman taimakon yadda za a mallake mijin.
A haka rayuwar ta cigaba da gudana. Ni ina ta fafutukar ya za a yi rayuwata ta yi kyau. Sauran 'yan matan suna ta gasar tara samari. Karatu da koyon sana'ar da za a dogara da kai bai dame su ba, koyaushe idan sun zauna hirar samari su dai a yi musu aure. A haka wani ya fito a unguwarmu da zummar auran Fati. Yana da sana'a sosai manemi ni, Amma fa kaf gidansu basa karatu daga na boko har na addini mazansu da matansu an dai yi musu sheda wurin neman kudi. Ajinta hud'u a sakandire aka yi auran. Bata damu da guntule karatun ta ba, hakan Ummansu ma ba wannan ne a gabanta ba, a cewarta ba za ta bari dama ta wuce ta ba, tunda kaf unguwar yaron ita ya gani yace yana so karatun ba dole ba ne, auran shine yake da a hakku. Kamar dai yadda ta fada a lokacin bikin Hadiza.
Aka yi hidimar biki sosai tunda shima ba lefi yana da rufin asiri a ka kaita gidanta dake karkasara. Sai na cigaba da rayuwa ni dasu Hassana da Usaina wanda suma a lokacin sun kere mini tsawo da girman jiki. Ni ba ni da wani girma A
amma ba na cikin jerin masu tsamurmuri jiki. Daidai misali ina da tsayi da cikar kirji da baya don wuyana a cike yake kowane d'inki na sanya a jikina yana zama mussaman fittedgown da riga da siket. Irin jikin Mamanmu ne da ni, mai kyau da boye tsufa. Sannan ba ni cikin farare haka zalika kuma ba ni cikin ba'ka'ke wuluk ina tsakiya fatata tana da kyau sosai shiyasa bana Gigigin shafa mata mai in banda cocorbutter quin Elizabeth shine man shafawata har hazar yau. Su kuma suna da girman jiki kuma a sake yake sharkaf irin na Ummansu. A wasu lukutan ma mutane suna d'auka yaran duk sun girmeni ni sai dai kawai na yi ta dariya ina mamakin yaran da aka haife su a gabana ya za a yi a ce sun girmeni kawai dai idan kana da jiki mai kyau ne sai ka ci zamaninka ka ci na wasu haka abin yake.
***
Hadiza ce koyaushe take cikin matsalar aure. Ita Fati tana zaune kalau. Sai narka ki'ba take yi. kuma shekara da yin auran ta haihu lafiyar Allah aka sha shagali. Ita kuma Hadiza ga dai gidan 'kato da kuma ci da sha amma babu nutsuwa. Bata sati daya sai ta zo gidanmu sun fita da Ummansu.
A cikin wannan hargitsin Iya kakarmu ta rasu sakamakon ciwon wuya da ta kwana biyu ta na yi. Abin ya zo da 'karar kwana Allah Ya kar'bi abarsa. Muka ci kukanmu muka koshi domin ba 'ya'yanta kawai ne ba suka yi rashin har da mu. Saboda tsohuwar akwaita da dattako da k'aunar jikokinta. Kuma ba ta ta'ba nuna bambamci a tsakaninmu.
Bayan an share makoki
sosai na mayar da hankali wurin koyan d'inkin da na sanya a zuciyata. Allah kuwa ya taimaka mini na gwanance kamar wasa Maman bokola za ta yanka d'inki ta ba ni ta ce na hau keke na had'a. Duk wahalarsa kuwa haka zan hade shi tsaf. Ta dinga mamaki. Tana fadin kina da fikira da ko'kari Amina, za ki ci abinci da d'inki in sha Allahu rabbi.
Idan na had'a mata riguna sai ta d'auki kudi ta ba ni, ni kuwa naki kar'ba na ce ai bata d'auke ni aiki ba tukkuna yanzu akan koyo ne don haka ba zan kar'ba ba. Haka za mu yi ta bugawa da ita har dai ta gaji ta ce to ta d'aukeni aiki na dinga zuwa shagonta. Na ce mata tunda daf muke da zana jarrabawa hankalina zai kasu gida biyu idan mun kammala sai na kama aikin gadan-gadan, yanzu sai dinga zuwa ina taimaka mata. Ta ce Hakan ya yi, ta yi mini addu'a da fatan alheri.
Bayan mun yi jarrabawar fita daga sakandire da kwana biyu aka kawo kudin auran Sahura. Sai a lokacin ne jikina ya dan yi sanyi da abinda yake faruwa da rayuwata. Wato tunda na taso nake ganin yadda samari suke karakaina akan 'yan'uwana, amma ni babu wanda ya ta'ba sansanta da sunan so. Ban san wane irin bakin jini ne da ni ba, gashi yau an kawo kudin auran Sahura wadda muke fad'uwa tare mu tashi tare, sannan Hassana da Usaina su kansu akan hanya suke domin an gama magana da iyayen samarin da za su aure su, kudi kawai za su kawo a tsayar da magana.
Sai na ji hankalina ya tashi, na fara tunanin ko dai Ina da matsala ne ban sani ba.
Ashe irin tunanin da nake yi shi Gwaggo take yi. Watarana ta kawo mini magunguña da turare ta fad'a mini yadda zan yi amfani dasu.
Ban yi kasa a guiwa kullum da magariba zan yi turaran. Har Ummansu Hadiza ta ankara ta tambayeni na gaya mata. Sai ta kama dariya tana cewa ai dole sai da turaran a lamarinki Amina. Ko a ina ki ka gado bakin jini oho. Ta wuce ta barni tana ta dariya. Na ji Anti Sakina tana cewa ko dai ki ka jefeta ai bata da makusa yarinyar duk tafi yaranki kyau, amma kin sanya gilli da bakin kishi a ranki, kowa ya ga wannan abin ya san jifa ne.
Wannan furucin ya haddasa musu rikici a gidan suka dinga cacar baki ni dai na yi shiru ban ce musu komai ba har suka gaji suka yi shiru kowacce ta shige d'akinta.
Haihuwar Fati ta biyu ta yi daidai da bikinsu Hassana. A lokacin kuma ni da Sahura mun samu damar shiga makarantar gaba da sakandire wanda ba yadda Ummansu Hadiza ba ta yi ba akan Babanmu ya hana ni, shi kuma ya ce ba zai yiwu ba tunda babu kwabonsa a ciki, ba zai dakatar da ni ba. Na je na yi karatun tunda mijin bai samu ba. Ta dinga jifana da mugun baki tana fad'in babu abinda ake koyowa a jami'a, sai Iskanci, ita ba zata bari yaranta su yi zurfin karatu ba aure shine gaba domin umarnin Allah ne. A wannan lokacin ne Babanmu ya yi mata jan Ido akaina ya ce duk lokacin da ta sake jifana da wata mummunar kalma sai ya yi shari'a da ita. Hakan ya sanya ta ce to ta zare hannunta daga kaina. Tunda ta gama wahala da ni, na girma za a nuna mata ba itace ta haife ni ba. Hakan ya yi wa anti Sakina dadi, sai ta fara jana a jikinta. Ban yadda na janyu ba saboda na riga na san hakan duk salon makirci ne, kadaran kadahan nake zaune da su. Ina basu girmamsu daidai gwargwado amma ba na yarda su taka ni, tunda na girma na san abinda yake yi mini ciwo.
Aka yi bikinsu Hassana kowace aka kaita dakinta. Sai na zama ni kadai a d'akin, idan zan fita na kan kulle tunda anti Yagana ta saya mini keken d'inki. Akwai kayan mutane a ciki na aikatau huluna da jakunkuna. Da nake yi suna biyana. Sannan wasu lukutan na kan d'auko aikin da nake dashi a shagon Maman bokola na yi a gidan. Shiyasa na sayi katon kwad'o nake kullewa a duk lokacin da zan tafi makaranta.