Sashe 15
Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*Free pege*
*10*
*@Arewa books*
*Bintuumarabbale*
Lokacin da muka isa station din yaran suna cikin cell a rufe. Wani d'an-sanda ya ce maza a sayo musu abinci domin tunda aka rufe su da asubahin babu wani abu a cikinsu.
Na fito da dubu d'aya na ba wa wani 'karamin ma'aikaci daga cikinsu ya je ya sayo musu abinci da ruwa ya shiga ya kai musu.
wanda case din yake hannunsa ya yi mana bayanin duk yadda suka yi da mutanan unguwarmu. Shi ma ya so maganar ta mutu ganin yaran kananu ne amma wasu daga ciki suka ce ba su yarda ba, kamar dai yadda Usaini ya fad'a suna cewa an jima ana yi musu sace-sace a cikin unguwar.
Babanmu ya ce bari ya je ya samu mai unguwa zai dawo yanzu. Ya tashi ya fita da saurin gaske. Ina zaune ina kallo ana ta shigowa da masu lefi har da mata daga cikinsu akwai wadda na kusa zubarwa da hawaye budurwa ce duka bata wuce shekara sha shida ba take sace-sace. Matar da suke zaune a gidanta haya tana sana'a idan ta fita unguwa yarinyar sai ta shiga d'akinta ta k'asan 'kofa da yake akwai rara ta sace mata kud'i sai yau da dubunta ta cika ta kamata. Da aka tambayeta tana kuka tace Mamanta ce take turata ta d'auko kudin sai su sayi abinci. Koda aka tambayi uwar ba ta yi jayayya ba tace hakane.
Ita kuma matar da suke zaune a gidan nata tana ta rantsuwa wallahi sai ta yi 'kararsu a kotu tunda duk abinda take yi musu basa gani sai sun cutar da ita.
Dubu hamsin da biyu ta d'auke mata Allah Ya sa ba su ci da yawa ba. Aka lissafa dubu hud'u suka ci, na zaro a jakata na bata. Na ce. " Don girman Allah ki dubi maraicin yarinyar nan ki rufa mata asiri, kada ki fitar da maganar nan, wanda ya suturta wani Allah zai suturta shi. Dan kuskure ta yi, haka nan mahaifiyarta amma ki yi hakuri, idan ya so sai ki tashe su daga gidanki, Amma dai maganar nan ta mutu anan."
Ta yi shiru sai huci take yi. Uwar da d'iyarta Kuma sai kuka suke yi. Na ce." Ke kuwa baiwar Allah ba kya jin tsoron ranar da Ubangiji zai tuhumeki akan abinda ya baki kiwo. Kada fa ki manta yarinyar nan amana ce a wurinki ki bar ganin ke ki ka haife ta, tana da hakki a kanki, haka zalika ma Allah Yana da hakki a kanki, me yasa za ki dinga tura ta tana yi sata, ki lalata mata rayuwa. Ba zaku nemi taimako ba? Ke me yasa ba kya yi sai ita, ki ji tsoron Allah, kuma ki yi nadama akan abinda ki ka aikata."
Ta share hawayen da yake gudana a fuskarta tana fad'in." In sha Allahu zan kiyaye wallahi rashin yadda zamuyi ne ya sanya shaidan ya ribaci zuciyata, amma na yi alkawarin hakan ba zata sake faruwa ba.
Na ce." To Ubangiji Allah Ya yafe mana gabad'aya, Allah Kuma ya shirya mana.
Jami'in ya gama rubuce rubucensa ya tura su wurin d.p.o domin ya sake yi musu sulhu. Ina nan zaune suka shiga suka fito. Muka yi sallama suka fita.
Jin shiru Babanmu bai dawo ba ya sanya hankalina ya tashi. Don ba na k'aunar yaran nan su kwana a wurin nan, ina so a samu maslaha. Na kira Usaini a waya domin jin Ina aka kwana nan yake tabbatar mini da cewa suna nan tafe gabad'aya har da mai unguwa."
Na kashe wayar zuciyata gabad'aya babu dadi.
Koda suka so station din zama aka yi sosai a office din D.P.O aka fito da yaran gabad'aya sun firgice yini daya da suka yi a rufe. Har da yar rama a tattare dasu. Gefan idon Kamalu ya dan tasa kamar duka kamar kuma alamun kuka.
Kallo daya na yi musu na kawai kawar da kaina. Da 'kyar aka samu sasanci. Amma dukda haka d'angaruwar nan sai da aka biya shi kud'in taya da wili acewarsa ba a haka ya ajiye kurar ruwansa ba.
Kudin beli dubu talatin. Suka buk'ata Kowanne dubu goma gabad'aya kudin hannuna basu wuce dubu sha uku ba. Babu yadda za a yi na yi belin mutum biyu na bar dayan. Tare suke shashancinsu, bayan haka ma iyayensa ba su da wani karfi ta abinda za su ci suke yi. Na bada abinda ya rage a hannuna na fita na ciro sauran na na cika musu sannan suka ba mu yaran muka kama hanyar gida lokacin tara saura na dare.
Lokacin da za mu shiga gidan ne na lura da dinginshin da Kamalu yake yi shi da Saminu sai ra'be-ra'be suke yi suna bin bango.
Usaini kuwa sai talle musu keya yake yi. A haka muka shiga gidan duk suna tsaye cirko cirko. Na bude d'akin na shiga na zauna 'kafafuna har yanzu ba su daina rawa ba.
Tun ina jin hayaniyarsu har na daina ji tabbacin kowa ya watse ya kama abinda yake gabansa. Na tashi na le'ka tsakargidan ta tagar dakina. Sai na gansu su biyu a zaune a tsakargidan su kad'ai. Shi Kamalun Yana ra'kube a kuskurwa ya rungume gwiwarsa. Yusi din yana gurfane a gabansa Yana kuka. Na daure zuciyata sosai na ce." Kai Yusi kukan me kake yi ku taso daga nan ma."
Ya kalleni da sauri yana cewa." Mama don Allah ki yi hakuri kada ki dake shi, jikinsa da ciwo da kafarsa ta kumbura, ya ce ba zai sake yi ba."
Na ce." Ai ba zan dake shi ba, ku taso ku dawo d'aki."
Ya riko hannunsa yana cewa." Yaya ta so mu je, ta ce ba zata dake ba." Ya dago kansa ya kalleni. Na ce." Ta so ku shigo ba zan dake ba." Sai hawaye shaaa! suka fara zubowa daga idonsa. Na d'auke kaina da saurin gaske na bar jikin tagar.
Rigijib haka na zube kan tabarmar duk ko'karin da nake yi wurin danne masifaffan kukan dake ta damuna kasawa na yi. Ya kufce da karfin gaske na sanya hannu na toshe bakina. Na silale na kwanta ina kukan haikan tare da tunanin ranar da Allah zai yaye mini k'uncin dana ciki tunda ga kuruciya.
MAFARI
Malàm Salisu mai hula shine mahaifinmu. Mutum ne mai ha'kuri da sanyin hali. Uwa uba kuma mara son hayaniya domin da wahala wata hatsaniya ta tashi a cikin unguwarmu ka ji sunansa a ciki. Ya kan kokari wurin ganin ya kama girma da mutumcinsa. Yadda ake fad'a tun yana k'arami ya tashi da zuciyar neman na kansa . Dalilin da ya sanya ma kenan ya fara fatauci zuwa gari gari kai huluna. Sai da Iya mahaifiyarsu ta nuna rashin yardarta da hakan tukkuna ya ha'kura. amma dukda hakan fataucin ya janyo masa alherin arzikin had'uwa da uwargidansa wato Mamanmu kenan mai suna Saratu. Asali Maiduguri kowa ya san gari ne da ake sana'ar huluna irin daban daban. A nan garin Allah Ya had'a shi da Mamanmu a kasuwa ta je sayayya kusa da shagon da yake zama ya gudanar da sana'arsa. Ba a ja dogon lokaci ba da suka aminta da junansu soyayya ta kullu sai iyaye suka shiga cikin lamarin aka gudanar da bincike ta kowane bangare babu wata matsala waliyan Babanmu suke shige gaba har garin borno aka dauro aure.
Babanmu bashi da matsalar wurin zama tunda mahaifinsu su uku kacal ya haifa kuma kafin rasuwarsa sai da ya bawa kowa wurin zama. A gidansa da yake unguwar kabuga cikin kwaryar birnin Kano Mamanmu ta tare da komai na al'adarsu. Sun yi farinciki sosai a lokacin da suka ga wurin zamanta ya yi kusanci da gidan aminiyar Dada wato mahaifiyarta. Suka dinga godewa Allah da ya sanya akwai wadda za su barwa amanarta a garin.
To Gwaggo maihaifiyarsu Yaya Aminu itace ta zama uwardakin Mamanmu kuma uwa a gare ta.
Mamanmu ta jima bata haihu ba. Hankalin Babanmu ya tashi don ganin yadda 'kaninsa Sule daga yin auransa har ya haihu. Kun san dai zama irin na Malam bahaushe. Babanmu ya fara wasu dabi'u. Ya canza gabad'aya. Gashi dai bashi da wani karfi kullum da 'kyar suke kai labari amma a hakan ya fara fafutukar kara auran wata bazawara. Ashe a lokacin Mamanmu tana da ciki ba ta sani ba, Shima bai sani ba. Tsabar tashin hankalin da take ciki ya gigitata ta kasa gane halin da take ciki. Ita macece mai bala'in kishi. Dalilin da ya sanya ma kenan ta figale ta lalace koyaushe ita da mijinta babu zaman lafiya. Shi kuma a lokacin idonsa ya rufe da son haihuwa.
Sai ta tattara kayanta ta gudu gidan Gwaggo da kudirin ba zata koma ba ta gama auran gabad'aya. Ita ba zata zauna da kishiya ba. Gwaggo ta dinga rarrashinta Amma fafur ta ce ba zata koma ba.