Sashe 8
Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
This book is 1k 08101626484.
Free page3
Malam wanzan ya kalli JAROOD yasan dalilin dayasa ya masa wannan tambayar. “Zanje gun uwata ne nima mu gaisa ,ko angaya maka kai kadai keda Giwar ne…” cewar malam wanzan. JAROOD yayi murmushi yace “Ku tsaya a gaisuwar, wlhi karka sake ka gayama Amour naki shiga gun me maganin…” “toh..” kawai malam wanzan yace da JAROOD, amma badan ya dauka ba. Suka isa falon da sallahma Hajiya fatima na kasa tana zaune da charbi a hannunta sanye da maroon hijjabi har kasa, dagani yanzu ta idar da sallah tana lazimi. wani sabon kamshi ke tashi a Falon da Sassanyar sanyin AC. Tin shigowarsu ta washe baki hadi da Amsa sallamar tasu tace tana kallon JAROOD. “Sannu Vie moi…” “Yawaah Amour…” JAROOD ya fadi yana karasowa gareta ya tsugunna ya gaidata ta amsa kana ta dawo da dubanta ga malam Abdullahi wanzan wanda shima ya zube se kwararo mata gaisuwa yakeyi. Ta amsa fuska sake tace “Ga kauna, ga kaunah…” JAROOD yayi murmushi shima malam wanzan din murmushi yayi, sun fahimci me take nufi, daman hakan takece Musu inta gansu tare. “Zauna mana malam wanzan kabani bayanin yaya ake cikin Yanzu kuka dawo daga gun maganin? Ina fatan de a dace?” Hajiya fatima ta fadi mgnr tana kallon malam Abdullahi dake tsugunne tinda ya gaisheta be zaunaba. Zaunawa yayi Akan lallausar carpet din dake falon yana facing hajiya Fatima ya kalli JAROOD yaga shima shi yake kallo ya wani hade rai. Amour ta kalli Wanzan ta kalli JAROOD ta kula da irin kallon da yake ma wanzan. “Inajinka bani bayani nana, kasan wannan Karan bazanbar kasar nan ba insha Allahu se naga ya Ake ciki?” Hajiya fatima ta kara fadin hakan tana tsare malam wanzan da idanuwa. Yayi shiru ya kasa magana saboda ya rasa meze ce. “Ya kayi shiru kuma inata magana ko kana tunanin wani abunne??” Hajiya fatima ta kara jefo wa Malam wanzan tambayar ganin yayi shiru tanata mgna shiru. Malam wanzan ya dauke idanuwansa Akan JAROOD ya dake ya fara magana cikin girmamawa kansa kasa yace “Ranki ya dade Allah ya kara Miki lafiya, wallahi munje gun maganin amma JAROOD yaki shiga, kuma munasa ran maganinsa zeyi aiki amma nayi-nayi JAROOD yaki shiga wai gun tsafine, wallahi ranki ya dade seda na tabbatar da inganci gurin me maganin sannan na kaisa…” nan da nan hajiya Fatima ta hade rai jin bayanin malam wanzan, ta kalli JAROOD Wanda ya hade rai sam beso wanzan ya fadama Amour abinda ya faru ba. “Kai haka akayi?” Hajiya fatima ta taare JAROOD da ido hadi da jefo masa tambayar ranta a matukar baci. Kallonta yayi yaga bacin ran dake kan fuskarta yayi hanzarin sauke idanuwansa , yayi kasa da kansa. “Kiyi hakuri dan Allah Amour…” JAROOD ya fadi cikin kankan da murya. “Hakurin me? Meyasa zakayi haka ? Waishin ko zugaka akeyine? Yaya kakeso amaka ne wai? Atunaninka Wanzan ze kaika inda za a cuceka ne? Dashi me cutarwa ne, da tini mu iyayenka baka taso ka ganmuba! Wani irin rashin tunani ne wannan ka farayi JAROOD? wannan ai rashin mutimcine ana fafutukar lafiyarka kanawa mutane wulakanci da rashin mutumcin, wannan Ai tsantsar wulakancine,,” hajiya fatima taketa fadin hakan cikin fada. JAROOD ya jima bega fushi da fadanta ba se yau, tadinga masa fada ta inda take shiga bata nan take fita ba. Shi kansa malam wanzan yayi nadamar gayamatan da yayi ganin yadda taketa fada, tamaki bari JAROOD din ya bude baki ya mata bayani, se fada take masa, shi kanshi malam wanzan be taba ganin fushinta irin na yau ba. “Dan Allah ranki ya dade Kiyi hakuri wlhi bansha zakiyi masa fada haka ba, nasha natsiha zaki masa Dan Allah ki masa natsiha kawai ranki ya dade, yafimu damuwa da abinda ke damunsa, abunne da gajiyawa ranki ya dade…” malam wanzan ya fadi cikin kidimewa bakaramin kidimasa fadan da takeyi yayi ba, sam ma besha haka take ba se yau. Nan da nan JAROOD ya shiga hayyacinsa ganin yadda taketa fada, se yanzu yake nadamar rashin shigarsa gun me maganin, danma Allah yasa wanzan ya d’an mata magana dan yaga ta d’an sassauta fad’anta. “Kiyi hakuri Amour dan Allah, zamu koma gobe insha Allahu, Dan Allah baba malam ka bata hakuri Gobe da sassafe zamu koma insha Allahu…” Cewar JAROOD daya fadi cikin kwantar mata da hankali. Se yanzu Hajiya fatima tadanji sanyi aranta jin yace ze koma gobe. Ta kalleshi tace “Kamin Alqawari zaka koma goben?” JAROOD yayi hanzarin cewa “zan koma wallahi insha Allahu Amour, bansan abinda ze bata ranki wlhi…” d’an sakin ranta tayi tace “Yawwa ko kaifa Allah yamaka Albarka JAROOD wlhi ina tsananin san inga ka warke, shine burina na duniyarnan dani da Sarki, Allah ya nunamin randa zanga ka warke, wlhi duk Akan lafiyarka naketa wannan fadan, gobe in Allah yakaimu dani za Aje insha Allahu…” malam wanzan yajin dadin mgnrta t karshe yace “Yawwah Ranki yadade kwara aje dake din..” JAROOD ya kallesa ya masa wani kallo, malam wanzan yaki yadda ya kallesa. “Wai sekace dole zuwa gun maganin…” JAROOD ya fadi aransa cikin gajiyawa, tinda ya taso yake zuwa gun neman magani ina zakaje neman magani daga ina kake neman magani, yana çıkın jarrabawa. Anan gidan sukayi sallar isha’i a masallacin wajen gidan. Ranar a nan sukaci abincin dare, sukasha hira su ukun se sha biyu nadare Sukabar gidan zuwa gidan JAROOD. A hanya JAROOD ya dinga kunkunan meyasa Malam wanzan yagaya ma Amour yaki shiga gun me maganin. Malam wanzan najinsa bebi takansa ba harya gama kunkunan nasa.
Suna dawowa gidan. direct JAROOD ya nufa part dinsa yasan yau ranar girkin Hajiya Zulaikha ne bazuwa zatayi ba. Bedroom dinsa ya nufa wanda yayi kyau ya gaji da kyau. Ya fada bathroom yayi wanka ya dauro alwala ya shirya cikin lallausar kayan bacci Se sanyin AÇ da AÇ kawai ke Aiki a dakin. Ya fara jero sallolinsa na dare kmr yadda ya saba, ya sallame. Ya zauna yanata lazimi, har zuwa lokacin sallar Asubahi, seda yayi sallar asuba 6:30am ya kwanta bacci haka yakeyi akullum baya bacci se yayi sallar asubah,. Juyi ya dingayi akan makeken dankareren gadonsa na alfarmar komi a bedroom dinsa green ne da milk color. Juyi kawai yakeyi timeis to time yanata tsuki ga bacci cike da idonsa amma ya kasa yinsa sbda tunanin dake cike fal da zuciyarsa, gaba daya tunaninsa ya ta’allaka ne dazuwa gun amsar maganinnan shifa harga Allah besan zuwa amsar maganin wallahi, amma ba yadda ya iya kodan Amour yazaman masa wajibi yaje. Se wuraren 8:30 yasamu bacci ya fara figarsa. Yajawo wayarsa yayi typing message ma Lambar malam wanzan ya tura masa kamar haka. “Se 2:pm inna tashi a bacci zamuje amsar maganin in case in Amour takiraka kace mata se 2:Pm zamuje gun amsar maganin kaddarar.” Ya tura masa malam wanzan naganin karashan abinda yace asakon yayi murmushi kawai. abangaren jarood yana tura masa sakon ya kifa kai nan da nan bacci me nauyi yayi Awan gaba dashi.