Sashe 13
Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
suka amsa da “Amin…” “wai nikam Malam Wanzan iyalinka ta karshen nan daka Aura Hassana sunanta kou ? Har yanzu kuna tare? ” Hajiya Fatima tayi tambayar da Malam wanzan. Cikin ladabi malam wanzan yace “Ehe muna tare ranki ya dad’e, sunanta hassana Ai itama yar Agadez ce…” hajiya Fatima tace “Ehe nasani, yan biyu ce kou? itace ta haifi takwarata?” Malam wanzan yace “Eh itace. Ita yan uku ce matar tawa, itace ai tahaifi me sunanki Ranki ya dade…” hajiya Fatima ta jingina bayanta sosai da kujerar motar, takasance macece ita mesan hira sosai. Taci Gaba dacewa “Nagane Allah me baiwa ashema yan uku ce…Amma ita takwarar tawa itama kace kamar yan biyu ce aka haifa dayar ta rasu kou?” Malam wanzan yace “Haka ne kuwa ranki ya dade gaskiya baki da mantuwa, ai aranar da Aka haifesu aranar dayar takoma itama macece daman de batazo da rai ba…” “Allah sarki Allah yasa me ceto ce..” malam wanzan ya amsa da Amin. JAROOD dakejin me suke cewa shima ya amsa da Amin, yana jinsu Amma besa baki ba sbda shi wlhi bema taba ganin yarinyar ba, yadesan yana bada abubuwa sosai akaima yarinyar, kasancewarta me sunan mahaifiyarsa. itakam hajiya fatima taganta da tana jaririya daga nan kuma bata taba ganin yarinyar ba. “Ranki ya dade ai yanzu haka ma ita takwarar taki tana kusan shekaru sha hudu ne, tana makarantar sakandiri ne yanzu haka SS2…” Cewar malam wanzan. Hajiya fatima ta rike baki cike da mamaki tace “ ohhh Innalillahi! Girman d’an mutum ba wuya , yanzu ita wannan jaririyar da Aka kawo mana ita har gida nida Sarki muka dauketa a tsumma harta girma?” Malam wanzan dake murmushi yace “Tini ma kuwa ranki ya dade ai in kika ganta tubarkallah, kyasha yar 17yrs ce…” hajiya Fatima tace “Ahh tubarikallahu masha Allahu, Allah ya raya mana ita kace sarki ya kusan Aurar da Diyyah,,,” malam wanzan yayi yar dariya yace “Aah ranki ya dade JAROOD ne ze Aurar da ita ai shine ubanta, sarki kuma kakantane…” hajiya fatima tayi murmushi tace “Au sankaine Abun,,,Ai shikenan Allah ya fiddo mata da muji nagari ..” suka amshe da Amin. JAROOD ya kara da “Nakusa sirikai saura kiris a fara çemin grandfather…” hajiya Fatima da Malam wanzan sukayi dariya hadi dacewa “Insha Allah…” Suna tafiya suna hira yau sunyi sauri sosai , da güdü malam wanzan yakejan motar. Dan haka Awa daya da mintoci, ta kawosu. Seda suka tsaya sukayi sallar la’asar acıkın gari kana suka karaso gun me maganin . Yauma mutanen dasuke gurin tinkass sunfi na jiya. Hajiya Fatima dasuka fito daga motar su duka ukun suna tsaye suna kallon wannan uban mutanen. Tace “Wai masha Allahu, wannan mutanen duk na meye?” Tayi tambayar da malam wanzan . “Duk masu amsar maganine ranki ya dad’e…” ya bata amsa cikin girmamawa. “yanzu wannan gurin sbda Allah ace bagun tsafi bane..” JAROOD Ya fadi yana mejin haushin dawowarsa gurinnan. “Kull da mgnr tsafinnan , in kanaso mu shirya...” Hajiya fatima dakatar da JAROOD da kalamansa . Dolensa yaja baki yayi shiru. “Ranki ya dade mu karasa, shiga kawai zamuyi dayake nariga na kara zuwa na mana booking, baza mu tsaya jiraba shiga kawai zamuyi…” hajiya fatima tace “Toh Masha Allahu…bismillah…” ta karashe mgnrta da juya akalar maganarta ga JAROOD. Malam wanzan ya shiga gaba JAROOD ya mara masa baya rannan nashi baki-kirin, hajiya fatima ke binsu abaya. Wani wanda ake Kira da d’an malam shi ya musu izo zuwa cikin dakin dame bada maganin ke ciki. JAROOD se kallon ko ina dako ina yakeyi yana yamutsar baki, labulayyan gurin duka red ne, fentin gurinma red ne. Kawai de JAROOD beda yadda zeyi ne amma sam wallahi hankalinsa be kwanta ba, ya kudiri aniyar ko an amso masa maganin a mugun gurinnan bazeyi amfani dashi ba. Seda suka zauna Awani benci dake Cikin falon bukkar, suka jira wani ya fito daga wani d’an daki yamma dasu, shi kadai ne daki acikin bukkar. Mutumin na fitowa JAROOD ya bisa da idanuwa yaga hannunsa rike da bakar ledar akasin jiya dayaga jan kyalle. “Zaku iya shiga…” Cewar dan matashin daya musu iso, wanda a ido befi 30yrs ba, sanye yake da wasu tsofaffin tufafi, dagani zakasan tufafinnan yafi 3month ma ajikinsa blue din shadda ce amma ta rikide takoma color me wuyar misaltuwa, ga fuskarnan bakikirin kamar an masa fentin baki, kwata-kwata bashi da kyaun gani, gashi jibgege tarin kiba guda, uwa uba ga uban tumbi kamar me shirin haihuwa. Hajiya fatima ta zuge bag dinta , ta dakko kudi kimanin 100k ta mikawa matashin ya amshe jiki na rawa ya dinga kwararo mata godiya shi Sam be taba ganin ma 50k tashi ta kamsa ba se yau Gashi yağa har 100k kuma duk nashi. Sosai yayıma hajiya fatima godiya tace bakomai ai wani abunma se ansamu biyan bukata. Tafadi aranta. Suka saka kai çıkın dakin da mutumin nan ya fito bakinsu dauke da sallahma, tini aka amsa sallamar çıkın dattako, JAROOD se raba ido yake adan dakin, yağa nan farin kyalle ne aka zagaye ko ina dashi, akasin falon bukkar. Har Allah Allah yadingayi ya daura idonsa Akan mutumin dake bada maganin. Nan kuwa idanuwansa suka sauka akan wani tsoho tukuf wanda a kalla ze iya kai 100yrs a iya nasa tunanin, sanye Cikin manyan kaya farare soll shi kansa tsohon fari sol yake siriri, yanada gashin gemu sosai, dukya cika fuskarsa kuma gemun fari Sol (Furfura). kyakyawa ne sosai yana zaune akasa kan wani farin kyalle, yayinda wani farin fai-fai kato ke aje agabansa,. “Ku zauna …” mutumin ya fadi yana nuna Muş’u gurin zama batare daya kalli fuskokinsuba. Hajiya fatima da Malam wanzan suma se kare masa kallo sukeyi. Suka zazzauna akasa kan tafarma ita kanta tafarmar fara sol take. Cikin girmamawa suka gaidasa su duka . ya amsa çıkın kamala har yanzu be kallesu ba. “Meke tafe daku?” Dattijon ya jefo musu tambayar still ba tare daya kwllesuba. Hajiya fatima ta kwararo masa bayanin komi Akan rashin lafiyar JAROOD. Se yanzu ya dago direct yasa idanuwansa manya-manya akan JAROOD din dukda ba’a nuna masa shiba ance shine JAROOD din ba. Me maganin ya jima yana kallon JAROOD for good 25mint kana ya sadda kansa kasa, ya daura idanuwansa akan wannan faifan na tsawon 10mint, kafin dağa bisani ya fara magana çıkın sassanyar muryarsa ta dattako, still ba tare daya kallesuba. “Iskokan dake tare dakai na kirki sun tabbatarmin dayimaka wannan sihirin Akayi, kajima kana neman magani insha Allahu kazo ga waraka da taimakon Allah subhanahu wata’ala mu nan magani muke bayarwa da yardar ubangiji,…” hajiya Fatima tace Allah ya yarje mana…” duk suka amsa da Amin harda me bada maganin. yayinda hajiya taji zuciyarsa ta mata wani sanyi ajikinta kawai takejin insha Allahu sun dace da yardar Allah. Shi kam JAROOD sam hankalinsa be kwanta da mutuminba shifa se yanzuma ya tabbatar da matsafine jin irin maganganun da yayi, kwata-kwata gün be masa ba arai ba, yaje gun magunguna dayawa amma be taba tsanar wani guriba yadda ya tsani wannan gün bada mgnin dama me bada maganin baki daya. Dattijon yayi gyaran murya kansa na kasa yaci gaba da magana “Amma gaskiya matsalarka babba ce agaremu sede ga Ubangiji karama ce, a gaskiya kmr yadda akasaba gaya muku warakarka na jikin mace ne toh hakan ne, zan iya ce muku wanda ya masa wannan sihirin an masa shine tin yana jariri, sannan wanda yayi kullin ya jima da rasuwa wato bokan da yayi mummunar sihirin. saboda haka yanzu zan baka magunguna da yardar Allah , amma da sharadin gaskiya seka Kara Auro mace ta uku Akan matanka guda biyu dasuke gida, sbda Harga Allah warakarka najikin mace ne, sannan kuma anasone ka Auro yarinya karama, Wacce akallah batafi shekaru goma sha biyu ba, zuwa shekaru goma sha uku, har zuwa shekaru goma sha hudu, zuwa de shekaru goma sha shida,,,idan SO samu ne ayi Auren Acikin wannan satın zuwa ranar Juma’annan wacce take tafe.…”