Sashe 4
Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read
zuwa yanzu, se naman dawisu yanaso sosai,. Se 11:10am ya bar part din hajiya Aisha sbda se jansa da hira takeyi, irin hirarnan ta nishadi har ya cika tumbinsa taf, sannan ta kula baya mood, dan haka shiyasa tadinga jansa da hira har tasamu ya dan saki ta sako hijjabi ta rakosa har compound din gidan, hannunta rike da wayoyinsa, tana masa hira yana murmushi amma fa a zuciyarsa cunkus take bawani armashi. Ba karamin girma gidan garesa ba, kusan get uku ne a gidan kafin suka karaso packing spaces, tako ina gidan ya tsaru , Gashi katoto, se shuke-shuke tako ina ga wasu part part wanda shi kansa me gidan be taba shigarsu ba. Ma’aika maza se garzayowa suke suna zubewa suna gaidasa, a kallah ma’aikatan dake gidan maza sunfi su dari. sbda shide namiji ne me masa gyara part dinsa, sbda hajiya Zulaihat bata gyara masa, se hajiya Aisha ke gyara masa tasa masa turaruka, shima se ranar girkinta, inko ba ita ke girkiba bata zuwa part dinsa, se tayi luf a dakinta tayita wayace wayacenta, daga ita se ubangiji sukasan dawa take wannan wayar, Gashi kullum wayarta na hannunta, ko ajiye waya batayi seda babban dalili, 24h takeyi a daki tana waya, wayar daseta kule a bedroom dinta take yinta.