← Book details Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 29

Sashe 3

Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fashe da wani irin kuka, ita kadai tasan me takeji, ba karamin cutuwa takeyi ba da Auren Jarood, gata irin matannan ne harijai masu tsananin bukatuwa, kullum se tayi mafarkin ta rabu da jarood ta auri namiji me lafiya. Bayan shigarta toilet din. JAROOD dake tsaye yayi shiru, yana kallon gefe guda a dakin, almost 5yrs yana cikin wannan halin da ita, a fari ba haka takeba yanzune ta fara gajiya, kusan 15yrs lafiya sukayi shida ita, Tana ganin girmansa ynzuko ko girman nasama bata gani, sbda becinta. Inda sabo yaci ace yasaba da halin hajiya Zulaihat amma Sam ya kasa sabawa, wasu abubuwan nazuwa masa sabbi. Wasu irin hawaye masu azabar kuna tafasassu masu turiri suka fara safa da marwa akan kuncinsaaa!.,. A rana yanayin kuka fin a kirga musamman in Hajiya Zulaihat ce da girki, ita macece Wacce bata da juriya, bata controlling magana, Sam bata iya danne abinda ke ranta. A wasu lokutan jarood baya ganin lefinta, ai tayi hakuri, hakurima me tsanani, amma de yasan be kamata tadinga gaya masa irin wad’annan kalamanba, kodan darajar girmansa, a banza ya bata 10yrs. da’ace tasan irin kunar da kalamanta ke masa a zuciya data rage musu tsauri garesa. Shimafa abun na damunsa kuma bashi yasama kansa ba ubangijine ya jarabcesa badan yana soba, bashi da yadda zeyi sede hakuri, a kullum yana rokon ubangiji ya sassauta masa wannan jarabawar yasan insha Allahu ze samu sassauci komin Daren dadewa saboda ubangiji maji rokon bawansa ne. Yafi 5mint tsaye kmr mutum mutumi yana kwallah, kana ya ciro wani kyakyawan farin kyalle daga aljihunsa se kamshi yake zubawa ya goge hawayensa. Jiki ba laka ya juya zebar dakin hajiya Zulaihat ta fito daga toilet din bayan taci kuka ta koshi ta wanke fuskarta a zatonta zuwa ynzu ya fice a dakin shiyasa ta fito. Dai-dai yana shirin fita tabi bayansa da kallo, ta saki wani tsuki ciki-ciki, batasan meyasa ba inde tana ganinsa se tayita Jin bakin cikin dake sata dole tayita tsuki, itafa wallahi daza a bata abun bugu zata iya masa bugun tsiya. Dai-dai Ya kai hannunsa handle din kofar dakin yaji fitowarta a hankali ya juyo, ya zubo mata idanuwa, a kallo daya ya fahimci kuka tayi data shiga toilet din, besan meyasa ba yana tsananin Jin tausanta sbda tayi hakuri, hakuri me tsanani dashi ba duk mace bace zata jure, amma ita ta jure saboda umarnin iyaye, shiyasa be tabajin haushinta ba a kan duk kalamanta garesa, Ada batayi masa wadannan kalaman a shekaru biyar dinnan ne ta fara masa wannan kalaman yasan hakurinta ne ya kare, kuma Gashi ba yadda zeyi sbda wannan Auren nasa da ita rabuwarsa zeyi wahala. idon Zulaihat dana Jarood suka sarke cikin na juna, Zulaihat Tayi hanzarin dauke idonta a kansa sbda bata jurar kallonsa eyes to eyes duk rashin kunyarta, sbda idanuwansa nada tsananin kwarjini. , ta karasa drawer din bedside ta zauna ta daura kafa daya kan daya, tana karkada kafa. “Zan fita..” Cewar jarood da yayi mgnr a gajarce murya babu karsashi. “Ina ruwana da fitarka ko inada case da fitarkane ni zulaiha? Me fitar Taka zata tsinana min? Abu daya nasani, nagaji da ganinka a dakina na kosa ka ficemin a daki malam.. mara Amfani kawai!” Ta fadi Cikin tsiwa, tana wani yatsuna baki. Ba tare da JAROOD yace komi ba, amma kalmar ta, ta karshe ta bugesa, inda sabo yasaba. , ya juya ze bar dakin a karo na biyu, ubangiji ne kawai yasan me yakeji a zuciyarsa, samshi daman magana bata wani damesa ba, yanada miskilanci me tsanani irin na yayan gidan sarauta, sannan shi mutum ne me tsananin hakuri da danne abu a rai. “Uhm Daman ka dena wahalar da kanka a banza, dannasan bako Ina zakaje ba se gun neman magani…kayi hkri kawai ka dena wahalar banza saboda alamu ya nuna a haka zaka mutu…” jarood dake niyar fita ya tsinkayo muryar hajiya Zulaihat na fadin wannan kalaman, ba tare daya juyoba ya fice a dakin, wani dumi ya kuma lullubesa na zallar bakin ciki. Dabadan yanada karfin imaniba ya tabbatar da tini ya mutu da bakin cikin duniya. Direct ya nufa dayar kofar dazata kaisa part din hajiya Aisha jiki da zuciya ba laka. Tinda ya sako kansa babban falon hajiya aisha yaji wani kamshi me sanyaya zuciya ya cika masa hanci, se yaji kwatan bakin cikin daya kwaso a part din hajiya Zulaihat ya ragu a ransa. daman ita hajiya aisha yar kamshi ce ba’a rabata da turare ako wani lokaci, domin itadin cikakkiyar yar medugurice kuma cikakkiyar yar duniya ce. Sak komi dake part din hajiya aisha haka yake a part din hajiya Zulaihat hatta da labulayyartama irin na part din hajiya Zulaihat ne, komi nasu iri daya haka Alhaji Jarood ya zuba musu ko ze chanza musu hk yake musu a tare yake musu komi hatta da motocinsu na hawa iri daya ne sak. “Ko ina tsaf-tsaf amma babu flower masu kayata guri…” jarood ya fadi a ransa se kara bin ko ina yake da ido kmr ya warke makanta, a zahiri ni senaga ko ina akwai flowers amma de bansan wani irin flower yake nufi ba bayan wadannan da Nike gani. “Inasan yara, dazan samesu sunfimun kaf dukiyarnan da Nike dashi…” jarood ya sake fadi a ransa, se kuma zuciyarsa tace “Kaida baka da Abunda za Asamu yaran ta sanadinsa? Kama denasa rai da samun yara…ka dauki kaddara, haka ubangiji ya tsara Maka rayuwarka tin FIL’AZAL…” zuciyarsa ke basa wannan shawarwari….. Hajiya aisha ce ta fito daga bedroom dinta, hannunta rike da wayarta, ita ta katse masa , shawarar da zuciyarsa ke basa. Tin shigowarsa taji, domin akwai abinda ke kara yana sanar dasu duk wanda yashigo part din, sannan ita hajiya aisha tasa wani abu da in jarood ya shigo zeyi kara, kara ta musamman. Hajiya aisha nada d’an tsayi kadan tafi hajiya Zulaihat tsawo, sannan batada kiba kmr hajiya Zulaihat, ita hajiya aisha kibarta a kasa take, tanada mulmulallan duwawuka cikakku masu ban shaawa ga duk d’ana miji. Bata da wani kyau a fuska itama harma hajiya Zulaihat ta dan fita kyau a fuska, hancinnan nata d’an dus kmr an dasasa, Gashi tanada wawakeken baki, itama hajiya Zulaihat tanada babban baki amma sede na hajiya Aisha yafi nata girma,. Kwata-kwata ita hajiya Aisharma ko matsakaicin Kyaun a fuska bata dashi, zan iya cewa de ita mummunace ta karshe, qualities dinta daya, tanada mazaunai manya manya, shima dan tana Shan magani ne sukayi wannan uwar girman daman de akwai su ammafa ta kara dana shago, bakace waluk amma sede Tana bleaching na Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un, wai Danma akwai Hutu da an samu matsala, ga kirjinnan nata a shafe, se d’an kan nono tsuit ake gani ta cikin riga, kwata kwata bata da Nono, Kasancewar sanye take da doguwar Riga ta bacci red, wadda ta kwanta jikinta ya bani damar kare mata kallo. kanta babu dankwali, amma sede Tanada suma balefi, tadanfi hajiya Zulaihat suma da kadan. Ada tana Karin Gashi seda Alhaji jarood ya taka mata burki shine tadena, ta tsayawa gashinta, bleaching ma dan besan tanayi bane da tini ya taka mata burki, a haka yaganta fara ya aura, beyi tsammanin bleaching take ba, Kodan mashi baya wani kallonta sosai,.Hajiya Aisha nayin 2eyes da JAROOD ta washe wagegen black mouth dinta, labbannan nata baki suduk irin de yadda labban yan meduguri yake, amma ita nata bakin se naga yayi yawa. A kallah hajiya Aisha bazata wuce 33yrs ba amma Ido sekasha kota girma Hajiya Zulaihat sbda gabaki daya zubin tsofaffi gareta, ga bleaching ya cinye mata fata sosai. Tinda ta fito daga dakinta taketa bin jarood da ido Tana sakar masa murmushi irin na shu’uman mata makirai. shima jarood yabita da ido , yayinda fara’arta tasa yaji sanyi a ransa, Gashi data fito yaji wani uban kamshi ya doshesa.shiko a duniya yanasan kamshi ita kuma hajiya Aisha bata rabo da kamshi. Akasin hajiya Zulaikha da Bata da tunani Sena acita dan haka ko kamshinma bata damu dashiba. “Barka da safiya Ranka ya jima, Alhajin Allah…” Cewar hajiya Aisha datayi maganar cikin iya magana, Sam muryarta bata da dadih, hasalima tanada babbar murya amma ta iya sarrafa harshenta, shiyasa A wasu lokutan take zama tauraruwa ga Jarood, Sam baya iya hanata abinda takeso garesa. “Barkade Hajiya Aisha yakike? Bade wata matsalar kou ?” Cikin kissa Hajiya Aisha tace “eh babu ranka ya dade, tako ina a wadace muke a gidanka sede fatan Allah ubangiji ya kara arziki duniya da lahira…, ba abinda zamuce dakai se dumbin Adduah ,,Allah de ya kara maka lafiya…” jarood ya amsa da Amin, çıkın Jin dadih. “Mu karasa ka zauna ranka ya dade, mu karasa dinning dan daganinka kanajin yunwa.…” Hajiya Aisha ta fadi cikin ladabi kamar zata kwanta masa a kasa sbda kissa da kisisina da iya tafiyar da namiji. “Wlhi zan fita ne ina sauri,…daman nace bari in shigo ne in ga lafiyarku..” Cewar jarood daya karashe mgnr yana duba watch din hannunsa, yaga time ya tafi sosai. “Duk muna lafiya ranka shi dad’e Dawisun Hajiya Aisha,,,amma se naga kmr bakayi break ba? Ko kayi de idonane be ganemin dai-dai ba?” Ta karashe da tambayarsa cikin kulawa. “No, amma ba damuwa kawai zan wuce inna fita zanyi break a waje…” marairaicewa hajiya Aisha tayi tace “habade! Kanada mu kuma kayi break a waje? Meye amfaninmu? Gaskiya ka tsaya kayi break ko ba yawa kasa wani abu a cikinka, sbda nasan inka fita be zama Lallai ka tsaya ka kulamin da cikinka ba, nikuma Banasan ka azabtarmin da kanka da yunwa,,,” nande ta dinga kanalnayesa da zancen kulawa, har tasamu ya amince suka isa dinning daman ta shiryama kanta abinda zatayi break dashi sannan tasan daman wasu lokutan a gunta yake break Tana sane da irin rikon sakainar kashin da hajiya Zulaihat kema Jarood ita kam sam bazata iya masa hakanba ko ba komai tana sanshi kuma ga daula Tana Ciki, taci hansin ta wanke dari tasaka. Seda tacika masa ciki taf da abinci, daman tasan yanasan dumamen tuwo shine abinci. Daya fiso yaci da safe, ita ma kuma tanaso sbda shi. Yaci dumamen Tuwon da farfesun kazar hausa, Sam bayacin kazar turawa kazar hausa kawai yakeci tin yana karami har
Chapter 3 · 0% Book details