← Book details Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 29

Sashe 15

Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

This book is 1k 08101626484. Free page5 “What!!! In Aura yar 12yrs, yar cikina kenan fa? Ni JAROOD in Aure yar 12yrs Impossible, Ko yar 20yrs bazan iya Aura ba yanzu wallahi, ko yar 30yrs gaskiya bazan iya aura ba….y’ay’an cikina kenan fa!” JAROOD ya fadi cikin zabura, nan da nan zufa ta kara keto masa. Ya zubawa me maganin ido kallon mara hankali yake binsa dashi, wato ko acikin masu bada maganin wannan babban mahaukacine, se yanzu ya fara Tunanin babban ciwon hauka nadamun tsohonnan Me maganinnan jin irin kalamansa waishi ze kara aure, ga bura ba lafiya. wato da gaske ne da ake cewa akwai mahaukacin cikin riga, be yadda da wannan maganar ba se yau Akan tsohonnan, shifa wallahi beji ajikinsa ma ze samu saukin wannan Abar ba. “Sekace agarin mahaukata ni JAROOD zan aura wata wai yar 16yrs…” JAROOD ya fadi azuciyarsa ya bude baki ze karayin magana Amour ta watso masa wani kallo dole ya dakata da mgnrsa, kawai yabi Amour da ido yana jiran yaji mezata ce, shide wallahi kome za ayi baze kara aure ba danshi ba mahaukaci bane, ko ajalinsa za ayi baze kara aure ba, ya kudiri hakan azuciyarsa, harga Allah kwara ya mutu yabar duniyarnan da ace ya kara aure. “Kayi hkri da abinda yaron yace malam. Ai bashi yayi kansa ba dole ma ya kara Auren, Amma kana ganin inya kara Aurennan Akwai waraka kuwa?” hajiya fatima tayi maganar Tana kallon tsohon, ita kanta fa ta kad’u dajin mgnr Karin Auren domin tasan da wahala d’an nata ya yarda da wannan tsarin, maganar data fadima ta fadeta ne kawai. malam wanzan kam shiru yayi yanaji ajikinsa inde se JAROOD ya kara Aure ze samu lafiya toh lallai baze samu ba, domin yasan mawuyacin Abu ne JAROOD ya karo aure. JAROOD yabi Amour da kallo jin tace wai dole ya kara Auren. Malam Aliyu me magani yayi murmushi irin nasu na dattako kana yace “bakomai hajiya ai yaro yaro ne, insha Allah batun warakarsa Munasa ran hakan, in har kikaga ya kara Aurennan yadda nace masa yar 12yrs zuwa 16yrs, be warke ba, toh ku hakura da neman magani domin bashi da waraka in har besamu lafiyar ananba…”. 100% Hakiya fatima ta yadda da abinda malam Aliyu yace, taji wani sanyi ya ratsata. JAROOD naso yayi magana Ta hanasa magana da idanuwanta, dole yasama bakinsa key, zuwa lokacin nan har kansa ya fara ciwo jin maganar Karin Aurennan da Akeso a kagaba masa sbda rashin imani acewarsa. Malam wanzan yayi shiru shide kmr ruwa yacishi, kawai yariga ya sadakar ba sa’ah, sbda yasan JAROOD baze yadda ya kara Auren yar 12yrs ba , sbda JAROOD nada mugun san girma gani yakeyi kmr ya girmi kowa a duniyarnan. “Shikenan malam badamuwa, ka bamu maganin kasa mana ranar dazamu dawo,…” Cewar hajiya Fatima. JAROOD ya kalleta yaga da full confidence dinta, wato harma sa ran dawowa wannan mugun gurin Amour keyi. JAROOD ya fadi aransa. Yanaso yayi magana ba damar yinta, amma ya kara kudirta aransa wlhi baze kara Aurennan ba, wannan ne karo na farko dazeyima Amour gardama. Malam Aliyu ya gama hada maganin ya mikawama Amour ya mata bayanın duk yadda za ayi da maganin, wani rubutune har jarka daya, se wasu kulli kulli. JAROOD yanaji de ana mata bayanı, ya kudirta aransa ko maganin bazesha ba. wallahi. Amour ta amsa maganin da malamin ya gama hada mata. Hajiya fatima se godiya takema malam Aliyun shi kuma JAROOD ya kosa su tashi su fita daga bukkarma baki daya ga mugun zafi agurin, kuma ga mugun zafin bakin cikin da kalamansa suka dasa masa na maganar Karin Auren, se yanzu yake nadamar daman yasani da jiya da basu taho da Amour ba yashiga gun me maganin, yasan in yace da Malam wanzan karya gayama Amour ba gaya mata zeyi ba, amma yanzu ai yasan bame kwatarsa se Allah. “Nawa ne kudin dazan biya?” Amour tayi tambayar da malam Aliyu. Malam aliyu yayi murmushi kawai yace “Sadaka zaki bada kawai ba a yankewa, ki bada Abinda ya sawwaka, sannan bazaku dawo ba harse kunga biyan bukata…” cikin farin ciki da murna hajiya Fatima ta bude bağ dinta ta ciro kudi bandir, bandir, na yan 1k ta fiddo bandir biyar ta ajiye agaban malamin ta kara da kwararo masa godiya. “Kayi hakuri da wannan malam insha Allahu zan dawo bada jimawa ba, ko iI kadaice…nagode nagode, ubangiji yayi sakayyar Alkhairi Allah ya bamu nasara…” Cewar hajiya fatima. JAROOD de se kallon bakinta yake tayi, tanata godiya kmr a bata kyautar wani abun. Malam Aliyu yaji dadin yadda take masa godiya hakan ya basa tabbacin ita din macece me dattako da sanin yakamata. “Toh shikenan bakomai Allah ya bamu nasara…” cewar malam aliyu. hajiya Fatima ta amsa da Amin çıkın jin dadih, nishadi ya cikata tako ina , ta jima bataji nishadi irin na yau ba da take ciki. Malam aliyu ya hada mata magungunan tsarin jiki, sbda itama ya fahimci akwai sihirce sihirce ajikinta na shekara da shekaru. Hajiya fatima tayi godiya sosai ita da Malam wanzan JAROOD ma yayi godiya se dole, Amour ce tasashi godiyar dolen da beyi niya ba. Suka fito daga bukkar suka Amshi lambar wanda ya musu jagorancin zuwa gun malam din, hajiya fatima ta kara masa Alkhairi ta kara masa 10k tace yasa card, ya amshe se kara kwararo Musu godiya yake . JAROOD kam tini ya amshe car key ahannun malam wanzan yakosa iya isa motar yasha AÇ, sbda zafi yakeji kmr zeyi hauka, shi sam be tabayin 10mnt bama baya çıkın AÇ se yau yayi har 40mnt yana çıkın azaba, Gashi yau ana Rana sosai kasancewar lokacin zafi ne, se zufa kawai ke diga ajikinsa kmr an masa wanka da ruwa. Hatta toilet dinsa fashi akwai AÇ, be çıka wanka da ruwan zafi ba, komin sanyin da akeyi sbda shi din mutum ne mejin zafi sosai ya saba da rayuwar turai, sanyi da sanyi. A mota suka samesa, Hajiya fatima tashiga gidan baya, malam wanzan yashiga dreva side ba bata lokaci yaja motar suka bar gurin, agurguje sbda ganin yadda time yatafi kusan 5:40 ake nema yanzu. Satar kallon JAROOD malam wanzan yayi yaga rannan nasa hade, dukda uban sanyin AC dake motar Amma JAROOD zufa yake tayi. Hannu yakai ya kara sanyin AÇ, hadi da karkato AÇ garesa sosai. “Kayi gudu sosai pls…” Cewar JAROOD da yayi mgnr ba tare daya kalli malam wanzan fa, dukya kagu yaje gida ji yakeyi kmr ya tashi sama, kawai so yakeyi yajisa atsakiyar gadonsa, yana juyi. “Vie moi…” Amour ta kira sunansa çıkın sanyin murya tin Dazu take kallonsa duk taga yanayinsa ya canza, se tausansa ya rufe mata zuciya abinka da zuciyar uwa akan d’anta, tasan duk maganar Karin Auren ce ta canza masa yanayi. “Na’am Amour..” JAROOD ya amsa hadi da juyowa ya kalleta çıkın girmamawa. “Dan Allah kar kasa damuwa kaji akan mgnr Aurennan,,,”amour ta fadi masa cikin kwantar da hankali dan tasan d’an nata dasa abu a rai. Jinjina mata kai JAROOD yayi Alamar toh ya numfasa se kuma yaci gaba dacewa “Amour dan Allah bazanyi Aurennan ba gaskiya wallahi ayi hkri abarwa Allah lamarinnan kawai, karmu fada harkar matsafa, na bayama dana auri har mata biyu Akan tsarin bokaye Allah ya yafemin, gaskiya yanzu ba Kari…” JAROOD ya fadi kmr ze fashe da kuka. Hajiya fatima dake kallonsa tace “Baze yuba, ni inaso kayi, naji yazamana wannan ne Karin aurenka na karshe inaji ajikina akwai nasara awannan Karan insha Allahu…” JAROOD ya maida kansa ga kallon hanya ba tare daya ce komi ba, shide yasan wallahi kome za ayi baze kara Aure ba, wani kuna ma yaji aransa da Amour ta masa maganar. Çıkın zafin da yakeji a zuciyarsa yace “Amour shekaruna hamsin fa yanzu aduniya, ace in auri yar 12yrs kamar ni JAROOD? Sekace de karamin yaro dan Allah Amour Karki dauki mgnr matsafinnan, asani in Auri yarinyar mutane in cutar da ita…” malam wanzan nata kallon JAROOD ta gefen ido, daman shi yasan za a rina, kwanta-kwata ma beji ajikinsa JAROOD ze amince da mgnr Karin Aurennan ba, mutumin dake maganar ma ze saki sauran matan nasa. Hajiya fatima ta sauke Gwauron numfashi kawai for some seconds se kuma tace “Bari mu İsa gıda se muyi magana…” ba tare da JAROOD yace komi ba kawai ya kwanta Akan kujerare hadi da hadiyar wani mugun yawu mara dadih, ji kake kuuttt. “Nasan zansha fama Da Amour akan Aurennan, Allah ya daurani a nasara wlhi banasan kara Aurennan…” JAROOD ya fadi aransa, besan mgnr ta bayyana ba amma malam wanzan ne kawai yaji, amour ma hankalinta nacan kan dogon tunani akan kara Auren, sam bataji me yace ba. Suna isa kaduna, dai-dai ana sallar magriba, bakaramin gudu Malam wanzan yayi da motar ba. suka tsaya a wani masallaci A kawo, sukayi sallar magriba, harda Amour ita ta shiga masallacin mata, tayı sallar sannan suka iso anguwar sarki. Acikin gidan malam wanzan yayi packing Giwar sarki ta kalli JAROOD wanda taga beda niyar fita daga motar tace “Ka fito mu shiga çıkı inaso muyi magana…” “Kaina na ciwo amour pls, zuwa gobe zanzo se muyi mgnr insha Allahu…” badan hajiya fatima taso ba tace “toh shikenan Allah sawake yanzu bari in baka magungunan naka…” ta karashe mgnrta tana miko masa ledar maganinsa dake hannunta. Ba tare daya kalli ledar maganin ba yace “ki bar maganin anan Amour goben innazo zan amsa insha Allahu…” “shikenan Allah ya kaimu goben, inka isa gida se muyi waya inji ya ciwon kan, ka tabbatar kasha magani…” JAROOD yace “Toh insha Allahu…” hajiya Fatima ta fita daga motar malam wanzan ya bude mata murfin motar. Ya amshi ledojin hannunta har falonta ya rakata. Bayan sun shigo tsakiyar falonta Ta juyo kalli wanzan tace “kana ganin Anya JAROOD ze yadda yayi Aurennan kuwa?” Malam wanzan yace “ wallahi da kamar wuya ranki ya dade…” hajiya fatima da jikinta yayi sanyi karai zuwa yanzu tace “Toh Allah ya taimakemu , Ubangiji ya dubemu, Allah ya daurani akansa ya amine, ni araina gaskiya inaso ya kara Aurennan wlhi inaso ya warke…” malam wanzan ya amshe da “Amin ..” yana me ganin damuwa kwance akan fuskarta. “Dan Allah kadan tayani yakın hakan
Chapter 15 · 0% Book details