← Book details Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 29

Sashe 5

Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

This books is 1k 0542703718 Saadatu Abdullahi GT bank. 08101626484. Banda card VTU pls.
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖💖
FIL’AZAL
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖💖
(Romantic and love story)

SAADATUBINTUABDULLAHI✍🏽(Writer of Kyautar Allah)

This book is 1k 08101626484.

Free page2
Seda ta rakosa har bakin motarsa dazasu fita a ciki. yayinda motocin dake jere a packing space din sukeda Yawan gaske, duk iya bin kwakwabina nakasa kirga motocin dake packing space din, yawansu yayi daga-daga da brain dina. Inada tabbacin acikin motocin akwai Wacce ba’ataba hawanta ba. Abu daya na iya ganewa shine Yawancin motocin dake packing space din duk green da White se black, whites da black’s din basufi a kirga ba. hakan ya kara tabbatarmin da yanasan green arayuwarsa. Tin kafin su karaso Malam Abdullahi wanzami ya isa inda suke, ya zube ya fara kwararoma JAROOD da hajiya Aisha gaisuwa. Kin amsawa JAROOD yayi , sede ita hajiya aishar ta amsa cikin isa, tanada mulki sosai, yan aiki nashan wahalarta, inda suke samun matsala kenan da JAROOD, Akasin hajiya zulaikha ita Sam bata da wulakanta d’an Adam, kuma ita yadace tayi wulakancin sbda ita jinin sarauta ce, bayan haka kuma daga gidan masu Arziki ta fito,akasin hajiya Aisha wadda tafido daga gidan malam shehu, bahaushe yace dan talaka be iya samun guriba. hade rai JAROOD yayi yana kallon malam Abdullahi wanzan wanda yasha manyan kaya da nadin buzaye, hakan ya tabbatarmin dashi cikakken buzu ne, baka ganin komi a fuskarnan tasa se farar fatar idanuwansa kawai, ganin çıkın idanuwansa ya tabbatarmin dashidin ba yaro bane, Akalla ze iya kai 65yrz abunka da jikin buzaye sam baza kace yayi wannan shekarunba sannan yana tare da manyan mutane yanacin Arziki, shi kansa daka kallesa zakasan baya çıkın wahala yana çıkın daula jikinnan nasa ya kwanta luf-luf. “Baba banace maka dan Allah kadena tsugunnaminba, daga yau yazama rana ta karshe dan Allah ka girmeni ni yadace in dinga tsugunno maka bakai ba…” Cewar JAROOD dake mgnr rai abace, yafi sau akirga yana cema malam wanzan wato wanda yake kira da Baba yadena tsugunno masa amma sam yaki denawa,. Ganin ransa yabaci yasa Wanzan mikewa cikin hanzari hadi dacewa “Allah ya huci zuciyarka ranka ya dad’e, baza akaraba…” hajiya aisha tayi caraf ta amshe da “Ai dole ne ya tsugunna maka ranka ya dad’e saboda shima ai yasan matsayin ba daya ba…” wani wawan kallo JAROOD yabita dashi nan da nan kuwa ta shiga hayyacinta tayi kasa da kanta. “Agurinkine matsayinmu ba daya ba, agurin ubangiji ba wanda yafi wani, se wanda yafi tsoronsa, wallahi matsayin Baba agurina ya wuce tunaninki, dan haka kar in kara Jin maganar nan abakinki…” JAROOD ya karashe mgnrsa da muryar gargadi, idanuwansa nakan hajiya aishar. Hajiya aisha ta matukar jin zafin yadda JAROOD ya wulakantata agaban wanzan, daman itafa wallahi tincan ta tsani malam Abdullahi wanzan, ko anguwa zataje bataso JAROOD yace shi ze kaita, gaba daya ta tsanesa, bata taba tsanar wata halitta kmr shi ba aduniya, ta rasa dalilin dayasa ta masa wannan muguwar tsanar, amma ta danganta hakan da yanayin yadda JAROOD ke tsananin sanshi ya basa mukamin dakosu matansa be basu wannan mukaminba. Da Anyi magana kuma yace wai tinda yataso yaganshi Agidansu , tin Malam Abdullahi wanzan nada 7yrs yake tare da iyayen JAROOD A Agadez , kuma yakema mahaifin JAROOD me girma sarki hidima, har JAROOD ya girma ya mallaki hankalin kansa yazamana bashi da wani babban abokin dayafi Abdullahi wanzan, agidansu aka koya masa tuki, har yazama dreva din JAROOD yanzu, kuma babban Amininsa yafi kowa sanin waye JAROOD, ko iyayen JAROOD basusan wani abu akan JAROOD ba yadda Abdullahi wanzan yasani, iyayen JAROOD suna tsananin san JAROOD hakan ne yasa suke san Abdullahi wanzan. “Bazan karaba insha Allahu Ranka yadade…” Cewar Hajiya Aisha data danne bacin ranta ta fadi hakan cikin kwarewa a kissa. Batare da JAROOD yabi takanta ba sbda ta bata masa rai, ya mika hannu kawai ya amshi wayoyinsa a hannunta,. Wanzan ya amshi wayoyin a hannunsa shima beji dadin yadda JAROOD din yayıma matarsa ba agabansa. Suka isa gaban dankareriyar motar dazasu fita da itan sabuwa dal kalar green se sheki takeyi tana walwali me kashe ido. Tasha bakin glashi. Wanzan na kokarin bude masa gaban motar JAROOD da kansa ya bude yashiga sam baya zama abayan mota inde malam din kejansa sede yazauna agaba saboda tafiya suke suna hira shida babban Amininsa. “Adawo lafiya ranka ya dade…Allah ya tsare…” Cewar hajiya aisha daketa sadda kai tanaso ta wanke lefinta. Ciki-ciki JAROOD ya amsa da “Ameen..” malam wanzan ya rufe masa kofar, ya zagaya ze nufi gefen dreva hajiya aisha ta watso masa wani kallo na kiyayya tanaji yanace mata “Semun dawo ranki ya dade…” ta masa banza ta juya ta nufa part dinta, tana tafe tana tsuki tana fadin. “Dreva yafi matanka na sunnah inba JAROOD ba an ina ake wannan gangancin… Mtwsss Allah de ya kyauta…” tana tafe tana matsifa ita kadai harta shige part dinta.
Chapter 5 · 0% Book details