Sashe 27
Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Abangaren JAROOD baccinsa yakesha yanzu sosai, yaci ya koshi ya kwanta , hankalinsa ya d’an fara kwanciya ganin amour tabar kiransa kawai yasan ta hakura ne da Aurennan na dole daza amasa, kawai kuma de dağa Ubangiji yakejin hankalinsa ya kwanta akasin ada, ya rasa dalilin kwanciyar hankalin nasa. Ranar Tuesday dayaje ganin doctor khamis ya tabbatar masa da jininsa ya fara sauka, saura kadan ya rage, yaji dadih sosai wlhi bayasan hawan jini da sugar Suna bashi tsoro, shida ake nema masa lafiyar jaruma kuma hawan jini da sugar yasamesa aiya banu. Dağa asibitin da yayi sallar azahar kawai ya nufa gidan Amour, tinda ya tinkaro kofar gidan yakejin gabansa na dukan uku-uku, daman a hanya ya tsaya ya mata tsaraba irin shi adole dağa tafiya ya dawo dinnan. Yana isa get din yaji kamar ya dawo baya, se kawai ya sadakar ya Danna hancin motarsa cikin gidan. Dai-dai malam wanzan na zaune a compound din gidan gefen wata flower suna hira da Abdul’aziz me gyaran flower, kawai idanuwansa suka sauka akan motar JAROOD,. Zumbur ya tashi cikin murna ya iso inda JAROOD din yayi packing motar ya fito, yana ganinsa ya sakar mata murmushi hadi dacewa “Nayi missing Dinka ubana…” cikin murnar Ganinsa malam wanzan yace “barka da dawowa uban dakina nima nayi kewarka..” JAROOD yayi wata yar siririyar dariya daya jima beyi irintaba yace “Barkade,,,ina Amour, tagajide ta hakura da mgnr Aurennan aini daman nasan seta gaji ta hakura tinda de ai ba a dole,, ni ba burar gwatso ba inta tara yaran mata suna tsinemin sunajin kmr su kasheni dan takaicina dake rayukansu nawa…” JAROOD ya fadi yana bude Murfin bayan motar yana dakko ledojin daya shigo dasu. Karo na farko da Malam wanzan ya farajin kunyar maganar batsar bakin JAROOD da ada ne shike tayasa maganganunnan, JAROOD besan dadin mace ba amma bakinsa akwai batsa sosai. sede malam wanzan yayi shiru bece da JAROOD komi ba, murmushi yayi kawai. Ya tayasa kwashe ledojin suka nufa hanyar zuwa falon hajiya fatima. Suna shiga falon dai-dai tana fitowa dağa bedroom dinta na dakin kasan, idanuwanta sukayi tozali da JAROOD, ta bude ido na mamaki tayi missing danta sosai yau take cewa zata kirasa idan ta tashi daga bacci toh tashinta a baccin kenan tayi sallah ta fito da waya a hannu tana shirin tazauna a falon ta kirasa. “Maraba da yan hijira..” Cewar hajiya fatima data fadi cikin murmushi ta tarı JAROOD da faraah. Nan da nan farin ciki ya kuma lullube JAROOD domin ganin murmushi mahaifiyarsa. Ta karaso tazauna suka ajiye mata ledojin a kusa da kafafuwanta kana ya tsugunna har kasa ya gaidata, cikin fara’ah da zallar farin ciki ya gaidata, ta amsa fuska sake hadi da masa barka da dawowa ya amsa da barkade. malam wanzan ya zauna akan kujera sbda hajiya Fatima tace yazauna amma ada yaso ya fita ne. “ saukar ka kenan yanzu?” Hajiya Fatima ta tambayi JAROOD, yace “Ehe Amour…” “masha Allah, kaje gida kayi sallah ka huta zuwa gobe inka huta ka dawo inada mgna dakai domin Abinda ka guda din be fasuba…” JAROOD yayi shiru yana nazarin maganarta ta karshe, be fahimci me take nufi ba, dan haka cikin kaguwa dasan yaji me takeso ta gaya masa yace “Ai nayi sallah Amour, sannan ban bukatar wani Hutu kawai ki gayamin me kkeso ki gayamin…” hajiya fatima tace “Aah kabari de seka samu nutsuwa kaje gida kaga iyalanka ko zuwa dare ne ka dawo…” Sam ba haka JAROOD yaso ba amma dole ya tafi gidan sbda ta matsa seya tafin. Malam yajasa a car, yaje gida ya kuma wanka yayi la’asar ya nufa part din matansa duka ya duba kafiyarsu. Hajiya aisha ta matukar jin bakin çıkın dawowarsa, amma ta boye sbda makirci ta nuna azahiri tayi murnar dawowarsa, kasan ranta ji takeyi kamar ta mutu dan bakin ciki in yana gida bason adinga Yawan fita yakeyi ba. Ita kam hajiya zulaiha azahiri ta nuna masa tayı bakin cikin dawowarsa babu boye-boye ita Sam bata iya makirci da munafunciba komi nata a free takeyi ba tsoro ba gudun zuciya. Daya shiga part din aisha seda yayi 30mnt tana jansa da hira, daya dawo yashiga part din Zulaikha 10mnt yayi ya fito a daddafe, da kyar ma ta iya gaidasa, ita ko miskhala zarratin bata iya makirciba, in kana neman Wacce tafi shedan kisisina da makirci kasamu Aisha magana ta kare, kuma JAROOD be isa ya gano halintaba sbda tasan hannunta.