← Book details Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 29

Sashe 26

Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Malam wanzan ya kalli BATOOL wadda kanta ke kasa, ya kalli hassana wadda itama shi take kallo. Yayi gyaran murya hadi dacewa “Duk kubani hankalinku nan,…” cikin ladabi BATOOL tace toh. Hassana ma tace “Toh malam…” malam wanzan ya fara magana çıkın nutsuwa. “Inaso kusan cewa komi kukaga ya faru toh daga Allah ne, hatta da motsa d’anyasanka wannan in ubangiji beso ba baka isa kayi ba, kuma kome kukaga yasamu bawa insha Allahu Alkhairi ne, ita kaddara da jarrabawa masu kyau ko akasin haka duk na muminine, ubangiji baze tabayin bawa ba tare daya jarabceshi ba, alhamdulillahi wani abu ya faru kuma na Alkhairi ne insha Allahu..”yayi shiru for some seconds, falon ya dauki shiru , duk sun kosa suji me malam wanzan zece, BATOOL kam tinda ya fara maganar kirjinta ke dukan uku-uku, ta kosa taji Ainifin maganar da yaketama wannan shimfidar sharar fagen ta mecece. Malam wanzan yaci gaba da magana idanuwansa nakan BATOOL “ita rayuwa ako wani Hali inka tsinci kanka anaso ne kayima ubangiji godiya,,sannan ke BATOOL ubangiji ya umarceki dakiyima iyayenki biyayya, inhar ba asabama mahalicci bane kinsande bazan cucekiba bazan ha’inceki ba, sannan bazan bari a cucekiba , BATOOL kasancewarki dhiyyata tilo aduniya, ina sanki so me tsanani, ina kaunarki kauna irin wadda uba na gari keyima yayansa, ina fatan kmr yadda kika sabamın biyayya kiyimin awannan karan, ke dhiyyace me tarbiya kin kai kin İsa ahanaki ki hanu BATOOL, saboda haka na bada Aurenki ga JAROOD d’an gidan me martaba Sarkin agadex, Aranar juma’ar data gabata aka daura miki Aure, yanzu ke matar aure ce ba budurwa ba…..” ba BATOOL ba hatta hassana seda ta zaro ido waje sbda mamaki, ganin yarinyarta karamace amma a haka malam ze bada Aurenta,ita Sam ba mace bace mesan duniya, Sam bata duba kudinsu ko sarautarauba. Abangaren BATOOL wani irin mummunan yanayi tashiga daga nan datake zaune, daman tini jikinta ya hau bari aiko ya kara daukar bari, nan da nan idanuwanta farare tass dinnan suka kad’a sukayi red sosai, ita ko sanin waye JAROOD dinma batayiba, bata taba ganinsaba, a razane ta dago ta kalli mahaifin nata shima ita yake kallo, ta rufe idonta ta bude akansa danta tabbatar, tabbas da gaske ba mafarki take ba mahaifintane agabanta yake gaya mata ya mata Auren dole. Ta maida kanta kasa, rawar da jikinta keyi ya kara yawaita, ji kake Fatt fatt! Heart beat dinta nata bugu kmr zata fito fili, amma sede ba daman magana ko uwarta bata İsa tayı musu da abinda malam ya fadi ba balle ita yarshi. Kuka kawai takeso tayi ko zataji sanyi amma ta kasa, khalid ne kawai yake yawo asararin birnin zuciyarta, ji tayi tamkar an rabatane da Khalid, rabata da khalid tamkar rabata ne da ranta. “Daman bazan auri khalid ba?” Ta fadi a zuciyarta, nan da nan kawai se hawaye sharrrr saman fuskarta. Mahaifinta ya kula da yanayin data shiga sannan yaga hawayen dake zirya akan kuncinta, har azuciyarsa yakejin zubar hawayen nata amma sede ba yadda za ayi bakin alqalami yariga ya bushe. Har hassana ya kula tashiga yanayi mara dadih sbda harga Allah ita bata da burin yarta tayi aure yanzu, shiyasa ta tsananta tsaro akanta kan karta kula wani. Hasan’a taso ace BATOOL takai 18yrs zuwa 20yrs se amata Auren kuma ita asan samunta so takeyi yarta tayi karatun likitanci, batasan a mata aure da wuri, ita in ita keda iko da itama takai 25yrs ma agida badamunta zeyiba, kunsan zuciyar uwa. “Ina me umurtarki dakimin biyayya, insha Allahu baza kiyi nadama ba domin babu wanda yakeyin nadama bayan Yama iyayensa biyayya…” BATOOL na kuka tace “Insha Allahu daadah zan maka biyayya har karshen rayuwata, duk abinda kayi dai-daine akaina saboda ka isa dani, kasameni me biyayya insha Allahu…” ciki kuka da sanyin murya take mgnar. Tausanta ya ratsa zuciyar malam, hassana kam ji takeyi kmr itama tayi kukan ko zata samu sauki, tausan yarta ya rufeta, kallon karama take ma yarta sosai, tayi kankanta da daukar d’ana miji a mararta yanzu, Sam batasan JAROOD din bashi d lafiya ba, ko a labari bata tabaji agun mijintaba. “Allah ya miki Albarka, Allah ya baki masu miki biyayya kamar yadda kikamin,,,” Cewar malam wanzan BATOOL ta amsa da amin hassana kam sede ta amsa a zuciya, da kyar ta iya cewa. “Allah yasa hakane mafi Alkhairi ya basu zaman lafiya,,,” malam wanzan ya amsa da Amin daman yasan hassana bazata masa gaddama ba sbda tanada gudun zuciyar mijinta sannan akwaita da ladabi tafi duk sauran matan daya aura. Har zuwa yanzu kuka kawai BATOOL keyi kasa-kasa tasa hannu ta datse bakinta, Malam wanzan baze jure ganinta a wannan halin ba, dan haka ya tashi ya dauki mukullin motar ya fice agidan zuwa gidan hajiya fatima. Yana fita BATOOL kmr tana jira ta tashi aguje ta İsa jikin mahaifiyarta ta fada jikinta tana kuka,abinka da shagwababbiya daman surin kuka ne da ita tin tini ita ko fada ka mata se tayi kuka, hawayenta a kusa süke,. Tana fadawa jikin mamanta ta fashe da kuka me tsanani tana fadin “Ammuh, wallahi banasan Aurennan dan Allah ki gayama daadah ya barni inada wanda nakeso khalid Ammuh ni khalid nakeso in aura, ban gaya muku bane amma mun jima muna tare makarantarmu daya, dan Allah Ammuh ki gayama daadah ni Khalid nakeso inma aure yakeso inyi abari muyi aure nida khalid inya gama makaranta, dan Allah Ammuh mutuwa zanyi inna rabu da khalid!!!” Seda hassana Tayi hawaye ganin yadda taketa kuka kmr ranta ze fita, se sambatun maganganu takeyi kmr zatayi hauka. Rarrashinta tashiga yi da kalamai masu dadih abinka da Uwa, nan ta dan fara sassauta kukanta amma tayı 1H tana kukan duk tabi ta fice a hayyacinta, idanuwanta sun kumbure süntum. Ganin ta dan fara dawowa hayyacinta yasa hassana tambayar BATOOL din waye khalid, sbda daman tasaba jin BATOOL na kiran sunansa in tana çıkın bacci batare da sanintaba, tanataso ta tambayeta waye khalid amma seta dauka ko mafarkine na shirmen yarinta. BATOOL ta bedema mahaifiyarta wuka da wutsiya kan wanene khalid. Mahaifiyarta ta numfasa tace “Toh wallahi tin kuna shaida juna keda mahaifinki karki sake yaji maganarnan abakinki. Yanzu kikace zaki masa biyayya, toh inaso ki masa biyayya, kibarwa ubangiji komi, wlhi inya rubuta sekin Aure khalid toh tabbas seshi d’an sarki ya rabu dake kin auri khalid din, karkisa damuwa aranki ki fawwalama ubangiji komi, sallar darennan kici gaba dayinta nima zanta tayaki ina miki Adduah dhiyyata ta gari kinji kou??” Nan de tayita lallaminta da ban baki harta tasamu tasaki ranta azahiri abadinima taji zuciyarta ta mata sanyi amma data Tuna da khalid setayi kwallah, data shiga dakinta ta dauki photon khalid tayita kallo, khalid kyakyawa ne black beauty cikakken buzu ne shima ga kyau ga aji, Gashi matashi a SS3 yake ba babba bane yarone sosai danye sharaf, irin wanda sam iyayensa ko giyar wake sukasha bazasu masa aure yanzu ba. Ranar yini da kwana BATOOL na kallon photon khalid dataji mahaifitarta zata shigo dakin seta boye photon.

Abangaren matan JAROOD bawacce tadamu wai dan benan musamman hajiya zulaikha harkar gabanta kawai takeyi, tinda hajiya aisha tace mata yayi tafiya kawai tace Allah tsare ko kiransa batayiba. Kwara ita hajiya aishar takirasa daukane kawai beyi ba, itama tafijin dadih da baya nan, seda tayi 2days ma bata kwana agidan ba, tana gün d’an boy yana gargasa mata duri da Jelah, data dawo ma washe gari takoma ya kuma ci, taciyu a kwanakinnan amma dayake hajira ce Kawai kari take nema kullum setaje d’an boy ya gargasa mata duri, ba abinda ya dameta ita bata cikin tension din shaawah, hajiya zulaikha ce ke ciki.
Chapter 26 · 0% Book details