Sashe 23
Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Free page9
Malam wanzan shi Sam Yama mance yanada diyya mace, saboda tsabar kad’uwar da yake ciki ta damuwar da hajiya fatima tasasu aciki, na mgnr Aurennan. sannan beyi tsammanin hajiya Fatima zataso ta hada jininta da nasa ba kasancewarsa kaskancinsa. “Tuba nike ranki ya ranki dad’e, eh inada yarinyar me shakara goma sha hudu,,,Amma sede…” se kuma ya dakata be karasa ba. Hajiya fatima dake kallonsa tace “Amma me? Baza ka bamu ba kou?” Malam wanzan kansa na kasa yace “Aah wane ni, ba haka bane ranki ya dade, ko bana raye ku
Masu bada Auren yarinyar nan ne, kawai de ina ganin kaskancina yayi kasa dayawa ace za a hada jini dani da gidan sarauta…” malam wanzan jinsa yakeyi kmr a mafarki ace waishi yau za a hada JAROOD da yarsa, amma sede kuma a kasan ransa yana tsoron Mezeje ga JAROOD. “Damu dakai duk daya ne Agun ubangiji Kaida kanka kasan mu ba irin mutanennan bane, kasanni kasan me martaba kasan JAROOD toh me yayi saura? Sede ko in bazaka bamu bane shiyasa tin tuni muketa nema kayi shiru baka tunasar dani kanada shuka a gida ba muke bid’ar iri…” hajiya Fatima ta fadi cikin kankar da murya, ta numfasa bata bari malam wanzan yayi mgna ba taci gaba da magana. “Amma bazamu maka dole ba dan kana karkashinmu, in baka
Aminta kabamu yarka ba,
Mun hakura, wallahi daganan inda akayi maganar nan ba wanda zejita insha Allah…” malam wanzan yayi hanzarin cewa “Wallahi aah ko daya, na Amince ranki ya dade, Ai da JAROOD da BATOOL yar wajena duk mallakinkine se yadda kikaso dasu, na Amince wallahi Niko yanzu a daura…” wani irin farin ciki ya lullube hajiya Fatima wanda ta jima batayi irinsa ba, nan da nan fuskarta ta rikide da zallar Madarar nishadi. “Nagode sosai da wannan karramawar, amma ni a shawarata atumtubi yarinya bata da wanda takeso, ? Sannan mahaifiyarta zata amince? Danginka zasu amince,?” Malam wanzan yace “duk ba matsala ranki ya dad’e, ita yarinyar bata farama tsayawa da samariba, ita kuma mahaifiyarta ai a karkashina take, dangina duk ba matsala ranki ya dade, na Amince Dari bisa Dari ko yanzu a daura Aure…” hajiya Fatima tayi murna sosai kuma taji dadin karamcin malam wanzan agareta. Godiya tashiga masa sosai kamar zata tsugunna masa har seda ma malam wanzan yaji kunyar irin godiyar dataketa masa yace “dan Allah ranki ya dade, kibar godiyar nan kina sani jin kunyaku, ni nasan ba abinda zanyi in biyaku da Alkhairanku gareni, kuma ni na yarje in JAROOD yazo yaga bata masa ba kawai ya saketa wallahi na Amince bakomai…” hajiya fatima tace “Waneshi, Ai insha Allahu ma mutuwa ce zata rabasu, fatanmude Allah ya bashi lafiya, wannan mutumtawar da darajawa haka, daka mana, kai masha Allahu… bari in kira me martaba in shaida masa wannan abun farin cikin,,,” takai hannu zata dauki wayarta, daya aje agefenta, malam wanzan shima se murmushi yakeyi besan dalilin dayasa ba yake jin kansa a farin ciki sosai. “Ranki ya dade agayama me martaba ya wakilta koma wanene yazama waliyinta ita BATOOL, komi na damka muku ahannunku, duk yadda kukayı dai-dai ne…” farin ciki ya kuma lullube hajiya fatima Lallai se yau ta yadda malam wanzan cikakken dattakone, wanda babu irinsu sosai a duniya se dai-dai. “Wannan karancin daka mana ubangiji ne kawai me iya biyansa,,,” hajiya fatima ta fadi tana kokarin dannama lambar me martaba kira, bugu daya biyu ya daga, cikin murna ta sanar dashi yadda ake ciki, aiko shima yayi murna sosai, yasan hajiya fatima nada hankalin da bazatayi abinda be dace ba. Nan suka gama tsaida maganar in aka sauko daga sallar la’asar Ayau za a daura Auren, batare da dogon bincike ba me martaba ya kara aminta, ya kuma jinjinama malam wanzan da mutumcinsa, yaji dadih sosai. malam wanzan yace ya wakilta waliyin BATOOL. Seda yasa aka bashi waya domin ya masa godiyar wannan shatara ta Arziki ga bada diyya kuma ga karramawa, beyi mamakin halaccin malam wanzan ba domin duk cikakkin dhiyyan Niger 🇳🇪 yan halak ne wallahi. Bayan malam wanzan ya amshi wayar, Me martaba ya dinga masa godiya da karamci, ya masa godiya sosai, malam wanzan ma rasa meze ce masa yayi, ganin babban mutum kamar Sarkin Agadez na masa godiya. Ya rasa meze ce kawai ya mikawa hajiya fatima wayar kunya gaba daya ta rufesa. Sukayi sallama dame martaba da hajiya fatima. Sunayın sallamar hajiya fatima ta Kai goshinta gabas tama Ubangiji sujjadar godiya, farin ciki ya lullubeta, bata taba shiga yanayi me dadih a Auren JAROOD da yayi ba guda biyun kmr na yau, ji takeyi Ayau hankalinta har wani kwanciya yayi sbda farin Cikin nishadi. Tajima a sujjadar tanama Ubangiji kirari da godiya hadi da dumbin gaisuwa ga Annabi Muhammadu SAW Annabin da Ubangiji da kansa ke masa kirari, d’an gatan Allah kenan, duk wanda ya rikesa bashi ba asara. . Hajiya Fatima ta dago harda hawayenta na farin ciki, ta karama malam wanzan godiya, mikewa yayi domin ya gaji da godiyar kunya yakeji, sekace ya basu wani abu, shi yadace ya musu godiya basu zasu masa ba, sbda hada jini dasuma Alkhairi ne, ga Tarbiya ga sanin sanin darajar d’an adam ubangiji ya musu. “Zan tafi ranki ya dade…” hajiya fatima dake kallonsa cikin dattako tace “Toh ina kara godiya,,sannan dan Allah inaso karka kara kiran JAROOD, ka kyalesa har sanda yaga dama ya dawo, tinda za ayi Auren Ai shikenan…sanda yaga dama ya dawo se yaji kawai daga bakina…” malam wanzan yace “Toh insha Allahu… yadda kikace haka za ayi ranki ya dade…” ya juya ya fice a falon, cikin farin ciki da murna yau yake jinsa. hajiya fatima ta gyara zamanta se murmushi takeyi, ta jawo carbinta dake gefenta tashiga zikirin Ubangiji, se kallon time takeyi ta koşa taga la’asar tayi. Tana nan zaune Tana lazimi har aka kira la’asar ta tashi tashiga bedroom dinta ta dauro alwala tayı sallarh la’asar tana idarwa tayı Adduah ta jawo wayarta zata kira Me martaba seta fasa sbda tasan kila yanzu ba a daura Auren ba in aka daura ze kirata ya sanar da ita. Har wuraren 5:pm be kirata ba, ta jawo waya zata kirasa , sega kiransa yashigo. Dagawa tayi, ya sanar da ita an daura Aure akan sadaki 3m (duk wanda yasan Niger yasan sadakinsu da tsada harga Allah , so kar ace karyata tayi yawa, kafin kuyi korafi ku dinga duba yanayin rayuwar labarin da akeyi, da rayuwar da masu kudi keyi a gidajensu, inhar kana zuwa gidan masu kudi kasan abinci-abinci da ake musu yanakaiwa kala 20 wallahi tallahi sede inba gidan masu kudi ka taba zuwa ba, so haka a Niger Aurensu da tsada wasu, bansande al’adar wasu ba a Niger din balle ma a Agadez kudin Auren sadakinsu da tsada, masu kawomin mgnr reni ku dinga gyara harshenku) a sadakin da aka bada 3M hajiya fatima gani takeyi yayi arha da yawa kawai de batace komi ba, shi kuma me martaba yayi hakan ne dan asamu albarkar aure. Hajiya fatima Da kanta ta fito farfajiyar gidan çıkın murna, neman malam wanzan bayan sun gama waya dame martaba. Aiko can ta gansa zaune kusa dame gadi suna hira. Yana ganinta ya iso inda take hadi da rissina mata, tana murmushi tace “Kadena rissinamin yanzu Kai sirikinane, an daura Aure Akan sadaki 3M a kudin Nigeria …” malam wanzan ya zaro ido waje yace “kai! Sekace de a banza kuke samo kudin kuma Ranki ya dade kudin yayi yawa, albarkar Auren kawai muke nema base anyi al’adar Niger ba ranki ya dade, dubu Dari ma yayi sadakin base an tsawwalaba, Allah de ya basu zaman lafiya…” hajiya Fatima ta karajin dadin kawaicin malam wanzan duk da yanada bukatar kudin domin ba wanda zece baya bukatar kudi a wannan rayuwar, amma malam wanzan be nuna kwadayinsa a fili ba kuma daman shi ba mutum bane me kwadayin, haka akeso mutum ya kasance ya dinga boye kwad’ayinsa. Hajiya Fatima na murmushi tace “Masha Allahu AlhamduLillah dasamun mutum dattijo kmr kai a matsayin sirikinmu, Allah ya kara maka girma da karamci malam …” malam wanzan ya amsa da “Amin, tare daku Giwar sarki me takun kasaita…” hajiya fatima ta kara fadada murmushinta tace “Yawwa yanzu ita yarinyar da mahaifiyarta suna Agadez ne ko suna nan Nigeria ?” Malam wanzan yace “Kin manta ranki ya dade suna can Agadez, amma suna zuwa garinnan ai suyi yan watanni sesu koma, amma zamansu din-din-din a agadez ne…” hajiya Fatima tace “Toh su dawo nan nigeria da mamanta duka, daman ita kadaice yarka kou akwai wasu?” Malam wanzan yace “Aah ita kadaice ranki ya dade…” “toh shikenan acikin gidajen JAROOD wannan da mukaje last Awani anguwa ma yake?” Malam wanzan yace “Eh a can cikin anguwar dosa ne…” hajiya fatima tayi shiru Tana nazari se kawai tace. “Su dawo nan nigeria da zama ku zauna a wannan gidan, kafin muga yadda ubangiji zeyi, se yarinyar ta tare anan gidansa tinda Akwai part part a gidan, zuwa gaba insha Allahu…” malam wanzan ya zaro ido waje sbda mamaki yace “Ranki ya dade wannan gidan yayi girma dayawa, zan kama hayar ko wani karamin gida ne semu zauna acan kawai, kafin aşan yadda za ayin…” hajiya Fatima tace “Aah baza ayi haka ba, kawai de tazauna a nan gidan, kar kace komi, ai yanzu an zama daya insha Allahu zuwa sanda suka shirya zasuzo se insa me martaba yase musu ticket din fly insha Allah…” malam wanzan yadinga godiya cikin farin ciki suka rabu, ranar har karfe tara na dare suna tare a compound suna hira, hajiya fatima farin ciki ya isheta, Daren ranar batayi bacci ba, sbda murna seda tayi sallar asubahi ta kwanta nan da nan bacci me ddh na nishadi ya dauketa, da kwanciyar hankali.