← Book details Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 29

Sashe 28

Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan yayi isha’i, dağa masallaci malam wanzan yajashi zuwa gidan hajiya Fatima. A hanya JAROOD se jan malam wanzan yake da hira, amma yayi shiru yanacan yana tunani-tunanin shin ya JAROOD zeji in aka gaya masa yarsa aka aura masa a matsayin matarsa ta aure. Ya zurfafa a tunani har suka iso gidan, JAROOD ya kula da Tuna’nın da Malam wanzan yake ciki dan haka suna isowa gidan ya kallesa yace “me kake tunani babana?” Malam wanzan besan sadda bakinsa ya subuceba yace “Na maka lefi…” ya sadda kansa kasa. Çıkın mamaki JAROOD yace “Lefin meka min da har zesaka a tunani?” Malam wanzan yayi shiru. JAROOD yaci gaba dacewa “Kome kamın na yafe maka in har ba Amour da Me-martaba ka kashemunba, wlhi na yafe maka…” malam wanzan ya sauke nannauyar numfashi ba tare dayace komi ba. Suka nufa falon hajiya fatima. Bata falon kasa dan haka JAROOD ya kirata a waya batare data dagaba ta sakko daga upstairs tana dakinta na sama ne tana waya dame martaba, taji shigowarsu domin taji karar bude get din gidan kuma tasan sune. JAROOD naganinta çıkın nishadi da zolaya yace “Barka da sakkowa Giwa me takun kasaita, Giwar me martaba…” “ai yau Kaima ka Ara ka yafa kenan…” ta fadi tana murmushi hadi karasowa ta zauna malam wanzan ya juya ze fita ta dakatar dashi. ”karka fita ka zauna ai dakai za ayi mgnr…” JAROOD ya zauna kasan carpet dai-dai yana facing hajiya fatima. Malam wanzan ya dawo ya zauna a kasa shima kusa da uban dakinsa. “Yaya kasamu iyalin lafiya kou?” Cewar Amour. “AlhamduLillah amour, ki gayamin wani magana zaki gayamin pls dukna kagu…” JAROOD ya fadi cikin kosawa. Amour ta gyara zama ta sosai azuciyarta se Adduah takeyi Allah yasa d’an nata ya aminta domin tasan in be amince ba ba aure, amma inya Amince lafiya lau aurensu yake, daman tinda aka daura Auren taketa Adduah Allah sa inya dawo ya amince da duk abinda tace. “Abinda ka gudane kadawo kaga anyi makashi…” cikin rashin fahimta yace “Amour kinsani a duhu abinda na guda kamar yaya? Wallahi bangane ba…” shi sam ma ya mance da maganar Auren. hajiya fatima taci gaba da magana. “Auren dakayi gudunsa Shi aka maka,,,” a razane JAROOD ya kalli amour domin ya tabbatar da abinda tace Akan fuskarta, nan fuskarta ta bashi tabbacin kalamansa. “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un! Wani irin Aure kuma pls? ” JAROOD ya fadi yana dafe kansa, nan da nan zufa ya wankesa Tass. Gaban malam wanzan ya yanke ya fadi ganin yanayin da uban dakinsa ya shiga, yafi yanayin da BATOOL tashiga, dande kawai shi namiji ne. Cikin sassauta harshe dukda an masa abinda bayaso Amma hakan besa ya daga muryarsa sama data mahaifiyarsa ba yace “Dan Allah Amour meyasa kikayi haka? Da gaske kike pls ko wasa amour?” Hajiya fatima ta hade rai tace “Nataba wasa dakaine?” JAROOD ya kuma dafe kansa wata zufar ta kuma wankesa, ji yakeyi kmr yasaka kuka amma ba dama. yace “Yanzu Amour kuma yar 14yrs din kika auramin saboda kawai kibi maganar malami, haba Amour dan Allah Amour ki duba ki gani 50yrs nike amma a haka akamin Auren dole kamar de bansan ciwon Kaina ba Amour,…” a hasale hajiya fatima tace “Da Anyi magana kashe shekarunka hamsin shin kai ka yankewa kasa cibiya ne wai? Kasani yaro baya girma gaban iyayensa ni yanzu sam bana ganin girmanka, a girman naka in har bakama iyayenka biyayya ba yazama na banza? Da girman naka in kana batawa iyayenka rai baze hana Ubangiji ya saba maka ba wallahi, Ka ganni nan Dani da Mahaifinka me martaba? Duk bamufi karfin iyayenmu su samu abu muyishi adoleba kuma ba tare da Muşuba, ko rayukanmu sun baci bamu isa mu nuna agabansuba sbda tsantsar ladabinmu agaresu, nida me martaba hadamu Aure zakayi amma hakan be hanamu kyautatawa junanmuba kaide kana gani kai shaidane yadda muke nida me martaba, Allah yajikan iyayenmu da kaga yadda Ake ladabi da biyayya, kune yayan gata yaran yanzu da iyaye ke fadi kuke fadi…ka duba ka gani harni fatima nake fadi kake fadi JAROOD?..” tana kai karshen mgnrta kawai setasa kuka, ta Kamo gefen zanin jikinta tana share hawaye. Ganin tana kuka yasa JAROOD rikicewa , ya matso ya tsugunna gabanta. “Amour dan Girman Allah kıyi hakuri, kidena zubar da hawaye akaina, aurene tinda an Riga anyi na amsa Amour na Amince duk abinda zesaki kuka bana sanshi, dan Allah kiyi shiru karkisa fushin ubangiji yasameni Amour, wallahi na Amshi Auren na Amince, duk abinda kikeso shi zanyi Amour…” farin ciki ya lullube hajiya fatima daman tana sane ta fara kukan sbda tasan JAROOD besan yaga hawayenta. Malam wanzan yana zaune yayi shiru shide jira yakeyi kawai yaji amour tasanar dashi wa aka aura masan, yağa ya reaction dinsa ze kasance. JAROOD da kansa ya dagota ya share mata hawayenta, acan kasan zuciyarsa yanajin tana masa suya, wannan shine adakeka a hanaka kuka kuma ba yadda ka iya, iyaye Kenan. Ya fadi a ransa. Bayan ya gama share mata hawayen taci gaba da magana “yarinya me hankali da nutsuwa aka Aura maka ina fatan ka riketa çıkın mutumci iyayenta dattawa ne, mahaifinta dattijone, dukda yasan baka da lafiya amma ya baka yarsa, kawai yar ya bamu komi me martaba ne yayi, karka watsa mana kasa a ido in har kanaso kaga farin cikina, kuma ka gama da duniya lafiya…” JAROOD yace “Toh Amour insha Allah wace yarinya ce kuka samamin din? Allah ya bani ikon muku biyayya.” Haka kawai yaji yanaso yasan ko wacece dukda yasan sanın baze amfana masa komi ba, ya kudirta aransa dole seya saketa koma wacece sbda baze zauna ya dinga cutar yar mutane ba. “Takwara ta, yarinya ta wajen malam wanzan…” JAROOD yayi saurin cewa “waaaaaaaa? Wani malam wanzan Amour?” Şam shi yama mance da wani malam wanzan sbda Dimauta. “Malam wanzan babban Amininka na yanzu…” amour ta karashe Tana nuna masa malam wanzan. Ya kalli malam wanzan wanda yayi kasa da kansa yace “İn har kaga bakayi maka ba na maka lamani JAROOD ka saketa ko yanzu-yanzu bakomai ni nasan uzurinka..” amour ta amshe da “Ai in har kaga ya rabu da yarinyar nan malam toh tabbas sede in lafiya bata samu ba, gudun karya cutar da y’ar mutane seya saketa ta auri me lafiya, amma ni naga yarinya tamin na yaba da kamalar ta da kimarta, da d’a’arta uwa uba kuma da cikar zatinta…” JAROOD ya dafe kai da 2hands yayi kasa da kansa, gaba daya an dauresa da jijiyoyinsa, ya bude baki zeyi magana amour ta dakatar dashi. “Kar kace komi in har kanason farin cikina, kawai kabı abinda nakeso, zan dakko maka maganinka yau in kaje gida ka fara amfani dashi na 1week ne maganin inka gama sekaje ku hadu da Amarya, tini nasa suka dawo nigeria sbda na isa, suna gidanka dake anguwar dosa inka tashi zuwa malam wanzan yakaika, kafin muga yaza ayi adawo da ita gidanka, matanka duk zanzo in sanar dasu zuwa gobe ko jibi inme duka ya yarda sbda kar suga ana shigowa da kayan Amarya suji ba dadih,,,” JAROOD yayi shiru kawai shi kadai yasan me yake sakawa a zuciyarsa, tinda Amour tace kar yasake yayi magana beyi küskuren yin maganar ba. “So nakeyi 💯 kaji aranka ka aminta da Aurennan in har kanasan ganin nishadina…” Cewar Amour. Jiki ba laka cikin ladabi JAROOD yace “Shikenan Amour na Amince kmr yadda kikeso…” dukda tasan mgnr bata kai cikinsa ba. amma taji farin ciki ya rufeta se sa masa albarka takeyi da Adduah tsari. Wuraren 11:pm JAROOD ya nufi gidan malam wanzan ke driving dinsa kawai ya dafe kai tinda ya shigo motar, se hakuri da ban baki hadi da kwarin guiwa malam wanzan ke bama JAROOD. A hankali ya dago idanuwansa dasuka koma kananu sbda damuwa ya kalli malam wanzan yace “Yanzu Amour ta kyautamin, sbda Allah kmr ni ace Amin Aure da yar ….” Se kuma yayi shiru ya kasa karasawa tinawar da yayi yar malam wanzan din aka aura masa. “Gaskiya ba dadih ranka ya dade amma kayi hakuri komi na duniya me wucewa ne ba abinda yake dawwama,,,” bending kawai yayi Akan kujerar yana sauke numfashi öne bye öne daki-daki, gaba daya kawai zufa ke karyo masa sam yau bejin sanyin AÇ ajikinsa se axabar zafi. Suna isa gıda ya fita yama malam wanzan seda safe a daddafe sbda mugun ciwon kan daya dabaibayesa, da ya rabu da ciwon kai yanzu ciwo ya dawo, yana shiga dakinsa ya dauki magungunansa yasha,na asibiti daman dasu yadawo gidan,. Ya taho da magungunan da Amour ta bashi wanda suka amso agun me maganinnan, cikin haushi JAROOD ya kwashesu ya zubasu a bolar, ya dawo ya kwanta se juya maganar auren yakeyi acikinsa. “Namiji kamana akamin Auren dole…” ya fadi dai-dai yana kallon saman Dakin nasa, ya rasama ta ina yau ze fara da tunanin nasa, sbda tunanikan sunyi yawa sun wuce nazarin me karatu a zuciyarsa.Haka ya kwana shide gashinan kamar bashiba yau maganin da kyarma ya masa aiki sbda da kyar yasamu bacci ya daukesa, yaumade mafarkai yadingayi Gashi acikin haske da wasu fararen flowers guda biyar,duk inya yabi se sun biyosa. Ya rasa wannan wani irin mafarkaine yakeyi a kwanakinnan.

Abangaren BATOOL tashiga damuwa sosai, kullum bata da Aiki Sena zaman daki, tafiso ta zauna ita kadai adaki, saboda tasamu damar tunanin Khalid dinta, kuka yazama Aikinta, mahaifiyartace ke kusantota sosai, saboda tadinga kwantar mata da hankali, mahaifinta ma da kansa inya dawo yana samunta yayita mata natsiha da lallami hadi da kwantar da hankali.
Chapter 28 · 0% Book details