← Book details Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 29

Sashe 21

Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

This book is 1k direct to me 08101626484.Insha Allahu a page 10 free page ze kare, wani games din na paid group, wasu zantukan bazasu fadu ba se a paid group dan haka ku hanzarta biya.
Free page8
“Ranki ya dad’e, ina zamuje?” Malam wanzan ya tambayeta ganin sunata shawagi a ti-ti batace masa komi ba, se kallon ti-ti kawai takeyi Tana tunani tunani, gaba daya ma ta rasa yaza tayi dabararta ta gudu. “So nakeyi ka kaini inda zanga yammata, yara haka, in Zaba masa wadda ta dace dashi wallahi yau yarannan be isa ya kara kwana ba ba tare da yayi aurennan ko waye ubansa a kasar nan wallahi, bade beda mutumci ba yarannan, ni nasan ma yana garinnan kawai boyewa yayi, jikina nabani yana garinnan yarannan kawai nayi shiru ne na kyalesa, so yakeyi yacimin mutumci, kuma hankalinsa ya kwanta…” çıkın makurar bacin rai take maganar. malam wanzan ya numfasa shima wallahi yanaji ajikinsa JAROOD na garinnan ba inda yaje kawai de sbda mgnr Auren da Amour keta masa yasa ya gudu ya bar gidan., yaje gidajensa da dama inda yasan ze samesa amma be samesa ba, kawai de yasan da wuya inya bar garin, shida ba fita yakeyi wasu garuruwan sosai ba, anan kadunar ma seya jima beje offishin kasuwancinsa ba, amma de yakan fita ya dawo, sometimes yana zuwa su hadu da abokansa ne na kasuwanci a Hamdala hotel suyi hirar kasuwancinsu , su danyi ciye-ciye yadawo, yana fita kullum duk ranar Saturday ne da sonday yake Hutu a gida amma sometimes ba gün kasuwancinsa yake zuwa ba sbda duk kasuwancinsa yanada me kula masa dasu wani Amintaccensa Sadiq dashi sukayi karatu. Se malam wanzan ma yakan dubo masa wasu abubuwan, kudi ne ya tarasu ya rasa yazeyi dasu wai danma a haka yana taimako sosai, kudinne an gajesu, sannan ga Albarkar kasuwanci ubangiji ya masa. “Abi komi ahankali ranki ya dade ki masa hakuri dan Allah, tinda ya muna bayaso , a hakura ni aganina Kinsan uban dakina in yaki abu se ahankali…” hajiya fatima tayi hanzarin cewa “Ai barinsa gidannan da yayi shiyasa ma dole se yayi aurennan wallahi ko wayeshi garinnan, yanaso ko beso se yayi, zan nuna masa yara basa girma inde suna gaban iyayensu, in ina raye ko yakai shekaru darı in nace masa yayi abu dole yayi, kaide ka kaini inda zanga yammata yau ko yan tallah ne se yaronnan ya auresu yau dinnan base gobe ba wallahi….zan nuna masa d’a be girma gaban iyayensa…” malam wanzan yayi packing a gefen hanya ya juyo ga hajiya fatima cikin nutsuwa da fahimtarwa ya fara magana “Ranki ya dade inso samu ne, be kamata a hadasa dako wacce yarinya ba, kwara a nemo Wacce aka aminta da tarbiyarta, uban dakina ma bazeso mace mara tarbiya ba, Kodan yaran daza a haifa da ita in Ubangiji ya yarje mana, ya kamata a bincika kar a hadasa da kowa ranki ya dade, aduba tagari kmr yadda Annabi SAW ya umarcemu damu nemawa y’ay’anmu uwa tagari, dan Allah ranki ya dade kar Ayi gaggawa, gaggawa Aikin shedan ne, amma in ranki ya baci da mgnata ayafeni tuba nakeyi…” hajiya Fatima tayi shiru hadi da nazarın maganganun malam wanzan kana tace “Haka ne kuma, wallahi bakayi lefi ba, ai gaskiya ce ka gayamin aiko kaga daga kin gaskiya se bata…toh yanzu yaza ayi? Ya kake ganin za’ayi, yarannan de insha Allahu baze wuce yau beyi aurennan ba ko in gayama me martaba ya nema mana yarinya ta kirki açan Agadez acıkın yaran abokansa ko jikokin abokansa…” malam wanzan yace “Eh haka ne ma yayi ranki ya dade,,,Amma ni aganina a fara bari JAROOD din ya dawo inyaso se ayi duk abinda ya kamata, cikin dadin rai…” hajiya fatima tace “Ta Ina ze dawo ayau dinnan? Yarannan beda niyar dawowa wallahi yanzu ya zanyi dashi bayan ko wayata baya dagawa? Yaufa yarannan baze wuce yauba seyayi Aurennan,…ja motar mu tafi ka kaini kaf gidajensa na garinnan in dubosa…inde yana garinnan yau sena nemosa, aide nasan kasan duk gidajen nasa na garinnan ko?” Malam wanzan ya tada motar yana fadin “Eh nasani ranki ya dade…jiyama Naje gidajen nasa dayawa, inaga befi saura gidaje biyar a gidajen nasa banje ba..” “muje sauran da bakaje ba…” malam wanzan yace toh ranki ya dade. Ya saka motar kan kwalta. suka hau ti-ti cikin sauri yake tafiya da motar sbda hajiya Fatima tace yayi sauri. Acikin lokaci kankani sukaje gidaje biyar din duk baya nan. “Duk munje gida biyar din benan Anya inaga da gaske baya garinnan? Kuma jikina na gayamin yana garinnan…” Amour ta fadi cikin gajiyawa tana me duba agogon wayarta kirar Samsung, taga wuraren 1:pm ake nema. “Su kenan gidannasa kenan?” Cewar Hajiya fatima. Malam wanzan yace “Eh ranki ya dade wlhi duka gidan kenan..” be mance da gidan JAROOD dake hayin dan bushiya ba, sede yanaji Ajikinsa bayama gidan, sbda Sam be zuwa gidan tin can ba zuwan yakeyi ba, kuma duk shine karami a gidajensa yanada tabbacin da wuya yaje wannan gidan nasa ya zauna for good 3days. “Maidani gida…” hajiya fatima ta fadi tana jingina kanta da jikin motar ita kadai tasan me takeji a zuciyarta, burinta daya Rakk aduk duniyar nan shine taga JAROOD yasamu lafiya, in ubangiji ya yarje mata ta goya jikanta a bayanta. Bawanda ya kara ce da wani uffan har suka iso gidan, kowa nata saka sa warwara a zuciyarsa ba kmr ma hajiya fatima. A tare suka shigo falon hajiya fatima da Malam wanzan duk suka zube akan carpet hajiya fatima ta mance when last tasawa cikinta aminci, tinda mgnr Aurennan na JAROOD ya kama bata sama cikinta abinci me nauyi ba sede abubuwa liquid take iyasha, damn can ita ba ma’aciyar Yawan cin abinci bace Amma takanci jifa jifa, sbda batasan kiba.
Tana zama a falon ta
rafka uban tagumi. Malam wanzan dake kallonta yace “Ranki ya dade karkisa damuwa dan Allah, komi yayi farko zeyi karshe…” hajiya fatima ta sauke ajiyar zuciya cikin jin dadin kalaman malan wanzan tace “Haka ne,, malam wanzan amma yarannan yana sane yabar garinnan, kilama yana hotel , duk dan sbda Aurennan ne, kuma ko mu dade komu jima seya dawo yasamu matar Ayau dinnan inde ni na haifesa Sena masa Auren ko yanaso ko bayaso wallahi,,yanzu kana ganin menene mafita? Dan Allah acikin abokanka babu me yarinyar mace Wacce bata wuce shekarun dame maganin ya fadi ba…” malam wanzan yayi shiru yana nazari can seyace “Aah gaskiya babu a yaran abokai na sede in tambaya ko za a samu a jikoki, ko dangi, wlhi dayake abokannawa yawanci duk sun girmeni…” hajiya fatima tace “Eh yawwah ka lalubomin, yanzu dan Allah, bari inje inyi sallah kaima kaje kayi sallar, İnka dawo seka gayamin ya ake ciki, in ba asamu se in kira me martaba ya duba mana acan, amma karka nuna Musu JAROOD za a bawa yarinyar, sbda nafiso a samo masa, wadda zata auresa dan Allah badan kudi ko mulki ba…” malam wanzan yace “Toh ranki ya dade, Allah yasa adace, zan bincika sosai kuma zanyi duk yadda kikace ayi..” ya karashe maganarsa hadi da mikewa. Hajiya fatima itama mikewar tayi. “Ka dawomin da magana me dadih dan Allah ko zanji sanyi a zuciyata…” Cewar hajiya fatima. Malam wanzan yace “Insha Allahu…” ya fice a falon zuwa masallaci se kiran sallar juma’ah akeyi a masallatan dake tin sallar karfe biyu. Yana fita hajiya fatima ta nufi dakinta domin tayi sallah, zuwa yanzu tadena kiran JAROOD kuma tasa a ranta bazata kara kiransa ba, duk daran daddewa zezo yasameta sede yazo ya tarar da Amarya ta kudirta hakan aranta.
Chapter 21 · 0% Book details