Sashe 7
Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
“Wai har Ina ne gun me maganin?” JAROOD ya tambaya malam wanzan dake driving tin Dazu sunata tafiya har sunyi tafiyar 1H amma basu isa ba. Malam wanzan yana driving yace “Mun kusa isa, ,,” JAROOD yace “Wani irin gurine wannan amma dagani dajine kou ?” Malam Abdullahi yace “Ehe amma ba daji sosai ba, karka damu ranka ya dade mun kusa isa…” cikin gajiyawa JAROOD yace “Wallahi nagaji da zakan motarnan..gaba daya ma nagaji da yawon neman maganinnan…” ya karashe kmr ze fashe da kuka. “Insha Allahu wata rana se labari, kwanan nan zaka hau Aiki kama hajiya babba ciki ka dawo kama hajiya karama ciki…” Cikin kwarin guiwa malam wanzan ya fadi hakan. JAROOD yayi murmushi kawai. Yace “Allah amince …” “Amin..” Cewar malam wanzan. “Inka samu masallaci mu tsaya muyi sallah…” Cewar JAROOD malam wanzan Yace “Toh ranka ya dade…” tafiyar 2H sukayi suka isa wani masallaci acikin gari, sukayi packing da motar securities dinsa. sukayi sallar la’asar suka idar sukaci gaba da tafiya acikin wani kasurgumin kauye dake Cikin zariya. “Tafiya kamar ta barin kasa..” Cewar JAROOD daya gaji da tafiyar, seya kwantar da kujera ya tasar ya rasa ma yazeyi dukya gaji saboda be saba tafiya me nisa ba a mota sede ajirgi. “Mun kusa insha Allahu…” Cewar malam wanzan. Jarood yaci gaba da mita “Ai da kawai jirgi muka hau dakasan da nisa har haka…” Malam wanzan de yayi shiru se basa hakuri yakeyi danya kula yagajine. Seda suka kara tafiyar 20mnt kana suka isa wani d’an karamin gida Awani daji gabaki daya dajin gidanne kawai gida adajin, gabas da yamma bawani gida se wannan gidan, mutanen dake zaune awajen gidan sunyi layi sunfi mutane dari uku, kama daga kan jinsin maza da mata, amma gaskiya mata sunfi yawa sun baibaye ko ina ga manyan mutane tako Ina, anyi packing motoci sunfi motoci dari biyu ata farfajiyar bukkar gidan. “Wani irin gida ne wannan kamar gidan matsafa? Dan duk mutumin dake shuka alkhairi baze baro çıkın gari ba yadawo daji…” Cewar JAROOD daya fadi mgnr yana kallon gidan yana kallon malam wanzan. Malam wanzan ya bude baki zeyi mgna JAROOD yaga wani mutum ya fito daga gidan hannunsa rike da wani jan kyalle irin na tsafi. Haka kawai JAROOD yaji sam hankalinsa be kwanta ba gaskiya. “Gidan bada maganine ranka ya dade bakaga mutane tankanba…” JAROOD ya girgiza Kai yace “Gaskiya wallahi ban yadda da gidannan ba, nan gidan matsafa ne, dagani ba Aikin ubangiji ake shukawa ba a gidannan…ajuya mota kawai ka mayar dani Gidan Amour maza cikin hanzari kafin gari ya fara duhu kasarnan ba lafiya bace da ita…” malam wanzan ya kalli JAROOD yace “Haba ranka ya dade musha wannan doguwar tafiyar kuma kace mu juya? Dan Allah ka fita muje kashiga kagani bawai gidan tsafi bane gidan maganin gargajiya ne, shiga kawai zamuyi nariga naje jiya nakama mana layi yanzu shiga kawai zamuyi…” “wallahi bazan shiga ba… dan Allah mu juya kawai wallahi nagaji , bazan kara dawowa ba gun wani neman magani daga yau wallahi, nariga na hakura…@ JAROOD ya fadi. Malam wanzan yashiga lallaminsa da lallabasa kan yashiga amma JAROOD yayi fır yaki, wanzan yayi-yayi JAROOD ya tubure. Dole suka juyo da motar suka dawo kaduna ran Wanzan adagule, sam ba haka yasoba, yaso ace su shiga su amshi maganin yanaji ajikinsa za adace. Amma JAROOD yaki, hakan ba karamin batama wanzan rai yayi ba. A anguwar sarki sukayi sallar Magriba, awajen gidan kana suka nufa falon Hajiya Fatima atare shida JAROOD, daman Hajiya fatima tanata kiran malam wanzan saboda tasan inta kira JAROOD bezama lallai yana kusa da wayarsa ba, sbda shi ba ma’abocin waya bane, amma yana kiran mahaifiyarsa sede itadin tafiso takira malam wanzan, tafi sabuwa da hakan. amma JAROOD inyaga kiran mahaifiyarsa yana dauka. “Malam ina
zakaje? JAROOD ya juyo ya kalli malam wanzan ya jefo masa tambayar, ganin yanaya binsa zuwa falon mahaifiyarsa.
This book is 1k 08101626484.
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖💖
FIL’AZAL
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖💖
(Romantic and love story)
https://chat.whatsapp.com/CyBhsjJtnx7C5FWgP88xX1
SAADATUBINTUABDULLAHI✍🏽(Writer of Kyautar Allah)
zakaje? JAROOD ya juyo ya kalli malam wanzan ya jefo masa tambayar, ganin yanaya binsa zuwa falon mahaifiyarsa.
This book is 1k 08101626484.
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖💖
FIL’AZAL
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖💖
(Romantic and love story)
https://chat.whatsapp.com/CyBhsjJtnx7C5FWgP88xX1
SAADATUBINTUABDULLAHI✍🏽(Writer of Kyautar Allah)