Sashe 16
Fil'azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
akansa…inaji ajikina akwai nasara awannan karan…” malam wanzan yace “Toh ranki ya dade, Nima inaji ajikina akwai nasara, amma sede da wahala JAROOD ya amince da Karin Aure, kawai de dan Allah Giwar Sarki abisa a hankali… abinda kwanciyar hankali be badasa ba akasin hakan baze bada ba..” hajiya Fatima data zauna Akan lallausar kujerarta tace “Toh shikenan, kaje seda safe ka kawosa da wuri nasan da wuya ma na iya bacci sbda damuwar wannan lamarin..,” malam wanzan ya rissina yace “Toh shikenan ranki ya dade, ki kwantar da hankalinki komi na Allah ne…” hajiya Fatima tace. “Allah ya mana me kyau, zuwa dasafe zan sanar dame martaba wannan maganar…” malam wanzan yace “Amin..Amma dakin dakata da sanar dame martaba ranki ya dade ki bari zuwa goben muga shi JAROOD din ze amince..” hajiya fatima ta amince da abinda malam wanzan yace. “Shikenan toh se goben…” sukayi sallahma ya fice a falon ya dawo motar cikin sauri. “Ka barni a car tin-tini, kanacan kuna shiryamin wani abu Kaida Amour kou? Ka barni a mota sekace ba mutum ka bari ba, bayan kasan kaina namin ciwo…” JAROOD ya fadi mgnr yana kallon malam wanzan. “Yi hakuri, bani nakar zomonba..” kawai malam wanzan yace dashi danya kula da yadda yake mgnr a hasale yake kmr irin shiya sashi yin Auren. Ba tare da JAROOD yace komi ba, malam wanzan yaja motar sukabar gidan. “Me kukace Kaida Amour ?” JAROOD ya jefowa malam wanzan tambayar. “Ba abinda mukace…” Cewar malam wanzan. “Shine kuma kaje ka dade…” malam wanzan ya masa shiru kawai ya riga yasan baya mood, yau mutumin se ahankali mulki ya tashi. Suka İsa gidan dai-dai ana kiran isha’i a masallacin gidan suka tsaya sukayi sallar isha’i, JAROOD ya tsa yayi sallar Shafa’i, beyi wutiri ba sbda yana sallar dare. seda ya gama laziminsa sannan ya fito a masallacin wuraren 9;pm. Yana fitowa daga masallacin ya shigo cikin gidansa ya baro inda masallacin yake, akwai get a tsakanin masallacin da cikin gidan. dai-dai hajiya yaga motar hajiya Zulaikha tashigo gidan,ta gansa amma se tayi kmr bata gansa ba, tayi packing a packing space, ta fito sanye doguwar rigar Atamfa ba karamin amsarta atamfar tayi ba, dinkin ya amsheta Abinka da Dirarriyar mace nonuwannan sun kuma cika kmr zasu fashe, ta yafa mayafi dai-dai da kalar kayan jikinta. Hannunta rike da karamar hand bag. kalar skin dinnan nata na zallar Hutu da kudi, se sheki takeyi ga haske tako ina a gidan se hasketa yakeyi Kai bakace dare bane inka shigo gidan sbda haske ne tako ina fauuuu!. JAROOD ya kalleta ya kalli dankareren watch din dake hannunsa. “Ke da izinin wa kika fita a gidannan!?” JAROOD ya tambayeta cikin tsawa,. Mamaki ya rufe hajiya Zulaikha ganin yadda yake mata magana, be taba mata tsawa ba se yau, aiko Seda kunnenta ya amsa, da gangar jikinta. Ta kallesa kawai seta daskare anan tsaye, har hannuntama rawa ya somayi sbda tsoro, car key dinta seda ya subuce ya fadi kasa, ta kasa tsugunnawa ta dauka sbda tsoro, batasan tana tsoronsa ba se yau. Çıkın tsananin matsifa da jaraba yaci gaba dacewa “Wallahi daga rana me kamar ta yau in kika kara fita agidannan batare da izinina ba, sekin gane waye ni a ranar, saboda raini duk kinbi kin raina mutum, zanyi maganinki tinda bake kike auren kanki ba ni nake aurenki!!!” Yana gama maganarsa çıkın fushi ya juya ya nufa hanyar get din daze kaisa part dinsa. Bayan wucewarsa hajiya Zulaikha tafi 5mnt a tsaye ta kasa ko kwakwaran motsi batasan shi jarababbe bane se yau, ashe ya iya fada? Duk bata sani ba se yau. “Ko uban me yasha?” Take tambayar kanta da kanta, se kuma taja dogon tsuki tace. “A banza de tinda baka da katafus bura kamar lagwani acıkın kerosine…ka tara mata baka musu komi se borin kunya…mtwsssss!!‘’ takara Jan wani tsukin. Ta tsugunna ta dauki car key dinta, tasa acıkın hand bag dinta, ta nufa part dinta tana tafe Tana tsuki ita kadai, tasan wannan fadan daya mata yau duk na borin kunya ne.