← Book details Exiled Prince Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 27

Sashe 7

Exiled Prince Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da rudu TESNIM ta ce " Abbi wane irin tarko kuma "
" na soyayya " ya fada a takaice
Yar karamar dariya ta yi kafin ta ce mishi " haba Abbi, wannan babyn ? Ko ni fa na girme mata ba ma ita ba duka su biyu "

" TESNIM ba ki san soyayya ba ne , ba ruwan ta da shekaru , amma za ki gane hakan duk ranar da ki ka fada soyayya ke ma "
Dan tabe baki TESNIM ta yi ta na girgiza kan ta ba tare da ta ce komai ba

Bangaran Inaya kuma , ta na fitowa ta zauna saman Waiting chair da ke bakin kofar dakin
Ta na zama Nesrine ta karaso gaban ta ta tsaya ta na kiran sunan ta
Kamar da ga sama ta jiyo Muryar Zayd ya na fadin " Cutie are you okay ? "

Slowly ta dago kai ta kale shi , ya na tsaye geffen Nesrine
Dan karamin murmushi ta saki kafin ta jinjina mishi kai, ta mayar ta sunkuyar da shi
A hankali ya kira sunan Nesrine
" na'am " ta fada ta na juyawa ta kale shi
Da kai ya yi mata allamun ta koma cikin dakin , ba musu ta juya ta koma cikin dakin ta ba su waje

Da kallo ya rakata har sai da ta shiga dakin sannan ya tako a hankali ya zauna saman chair din da ya ke geffen ta
Cikin sanyin murya ya ce mata " cutie fada min me ya ke faruwa , ko yanzu kin daina so na ne tun da kin ji ko ni wanene ? "

Murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " soyayyar ka ta zama wani bangare na cikin zuciya ta , mutuwa ce kadai za ta iya fitar da shi , kawai dai na ji dalilin da ya sa ba za ka iya so na ba , ni ba ajin ka ba ce , sai dai na zama mai maka shara da wanke wanke , ka fi karfi na yaya Zayd , don Allah ka yi hakuri ka yi tafiyar ka , ka bar mu a nan , ko ba komai zan rage radadin soyayyar da ba zan taba samu ba "

A hankali ya lumshe idanun shi ya bude su sannan ya ce mata " ba zan iya tafiya na bar ku a nan ba gaskiya , inda ma a ce malam na raye , amma ba ya nan , ban san irin abun da zai faru da ku bayan tafiya ta ba , ni fa ba shawara na ke ba ki ba umarni ne "

Yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " nan fa ba masarautar ta ka ba ce , ba ka da ikon ba ni umarni "

Cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " amma ina iya ba ki umarni a matsayi na na mijin ki "

Wani cool murmushi ta saki ta dago kai slowly ta kale shi ba tare da ta ce komai ba
Sai da ta gaji da kallon shi sannan ta meda kan ta , ta sunkuyar
A hankali ya dan sunkuyar da kai ya leko face din ta ya ce " Wannan murmushin kuma na meye , ko ba za ki bi mijin ki ba "
Kauda kai gefe ta yi ta na ci gaba da murmushin ta wanda ita kadai ta san na minene
Ta na haka kawai ta ji ya rungumota ya hada kan ta da kirjin shi cikin sanyin murya ya ce " na ji dadi da babu abun da ya same ki , ba ki san irin sanyin da na ji cikin zuciya ta lokacin da na bude ido na gan ki "
Dan karamin murmushi ta saki ta na kara lafewa a jikin shi

Sai da su ka dauki lokaci a haka kafin ya sake ya tashi ya ce su koma ciki
Noke mishi kafada ta yi cikin shagwaba ta ce mishi " ni ba zan koma ba "
A hankali ya koma saman chair din ya zauna ba tare da ya ce mata komai ba ya san bai wuce ta ce ta na jin kunyar Malik ba

A haka su ka zauna a wajen ba wanda ya sake cewa uppan har sai da Diya da Abdoul su ka dawo su ka same su a nan

A tare su ka saki wani kyawatencen murmushi kafin Diya ya ce " AMIR za mu iya tafiya ko sai ka ida hira da babyn ka ne "

Dan karamin tsaki Zayd ya yi kafin ya mike tsaye ya fara takawa ya yi gaba
Ya na barin wajen Diya ya kali Inaya ya ce " Gimbiya , tashi ku je "
Jinjina mishi kai kawai ta yi kafin ta mike a hankali ta bi bayan shi , ta na fitowa ta hango shi tsaye wajen wata dankareriar mota fara kal , mama na ciki zaune ya na yi mata magana ,
Wajen su Inaya ta karaso , ta na tsayuwa wajen ya ce mata ta shiga motar
Ba musu ta bude ta shiga motar , shi kuma ya juya ya nufi wata motar daban ya shiga
Abdoul da Diya kuma su ka nufi cikin dakin , Diya ya ce wa Malik za su iya tafiya yanzu

Ba musu duka su ka tashi su ka fito dakin su ka baro Hospital din , cikin wasu irin manyan motoci ma su nunfashi
Inaya da Nesrine su ka shiga mota guda tare da mama
TESNIM da MALIKAT su ka shiga mota guda
Abdoul shi kuma tare da Diya
Sannan Malik da AMIR su ka shiga mota guda su ka bar Hospital din
Kai tsaye airport su ka nufa cikin konciyar hankali
Su na isa ko ten minutes ba su yi ba jirgin su ya daga dama cikin private jet din su Malik su ka zo , to cikin shi kuma su ka bar Nigeria

* AFTER SOME HOURS

* SAUDI ARABIA

Misalin karfe 9 na dare jirgin su ya sauka a kassar Saudiya
Airport din cike ya ke da ga Sojoji da dogarai , duk mutanan wajen da idanun su su ka sauka kan AMIR sai da su ka sha jinin jikin su
Shi kuma AMIR ko a jikin shi , ko kallo ba su ishe ba kai tsaye ya nufi wajen motocin da a ka tanada musu , kowa ya shiga su ka bar airport din da mugun gudu kamar za su tashi sama

Cikin abun da bai fi ten minutes su ka iso Daular saudiya
Ba su Inaya kadai ba , har shi AMIR sai da ya yi mamakin ganin irin gyaran da a ka yi wa Daular ta zamo mishi kamar sabuwa
Har building din Malik da ya kone , an meda shi sabo amma wannan karan mai hawa hudu a ka yi ya ni ka farko kyawo da girma

Kamar ko Malik ya san abun da ke cikin tunanin yaron na shi sai ya yi dan karamin murmushi ya ce ma driver din su ya kai su building din
Building din tun da a ka gena shi har yanzu babu wanda ya taba shigar shi , dan musaman Malik ya sa a gena shi saboda AMIR na shi ne na musaman , shi kuma Malik a ka yi mishi wani part din daban

Sai driver ya iso bakin kofar part din sannan ya yi parking din motar
Da sauri dogarai da ke tsaron part din su ka karaso gaban motar su ka budewa Malik kofa
Ashe AMIR ne ke zaune a bangaran su na ganin shi su ka yi baya da sauri su na karanto kalmar shahada

Ya na fitowa ya tsaya ya na karewa building din kallo nan take abun da ya faru tsawan shekaru ya dawo mishi sabo

Ya yi nisa cikin tunanin shi ya ji Malik ya dafa kafadar shi ya na fadin " mu shiga ko "

Dawo da kallon shi AMIR ya yi kan Malik cikin nitsuwa ya ce mishi " ka sa a kai matan nan wajen MALIKAT INAS " ya na gama fadar hakan ya daga kafa ya na taku cike da izza ya shiga cikin ginin

Ya na shiga Azim ya karaso wajen ya Zube saman guyiwowin shi ya na gaishe da Malik ya na yi mishi barka da zuwa

Amsa mishi gaisuwar shi Malik ya yi kafin ya ce " akwai wasu mata da ke tare da mu , yaran ka sa a kai su wajen MALIKAT INAS , matar kuma a isa da ita wajen MALIKAT HOUDA " ya na gama fadar hakan ya shiga cikin building din shi ma

Ba musu Azim ya mike dan cika umarnin Malik
Abdoul da Diya kuma ba su ma shigo Daular saudiya ba , Kai tsaye Daular Ottoman su ka nufa

Bayan AMIR ya shiga building din kai tsaye wajen lift ya nufa ya Haye hawa na uku
Kai tsaye lift din da parlourn ya ke sada ka , ya na shigowa ya ji zuciyar shi ta buga da karfi
Cak ya tsaya waje guda ya na karewa wajen kallo , ya na nan kamar yadda ya bar shi , duk kayan da a ka saka mishi sak irin na farko

Ya na a haka ya ji Malik ya dafa kafadar shi
A hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce " zan shiga wanka ba ni son kowa ya dame ni " ya na gama fadar haka ya nufi wani corridor da ke saman damar shi
Da kallo Malik ya raka shi sai da ya ga ya shiga bedroom guda da ga na cikin corridor din sannan ya saki wani kyawatencen murmushi ya nufi sofa ya zauna

Ya dauki wajen good 30 minutes a haka kawai ya ji kofar lift ta bude , RIANNA ta fito da ga ciki da gudu ta na hawaye ta nufi Malik ta Zube kassa kussan kafafun shi ta na kuka ta ce " Abbi wai AMIR ya dawo , tun dazu na ke ji cikin masarauta wai sun ga AMIR ya shigo nan , Abbi wai da gaske ne , AMIR di na ne ya dawo , Abbi ku fada min "
Chapter 7 · 0% Book details