← Book details Exiled Prince Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 27

Sashe 14

Exiled Prince Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya mika mata wayar ta , Sannan ya shiga latsa ta shi ya ce mata " Idan na tafi zan dinga kiran ki ga number ta na saka miki , ko ki na bukatar wani abu sai ki kire ni "

" shikenan yaya Zayd " ta fada ta na ajiye wayar saman bedside drawer

meda wayar shi shi ma ya yi cikin Aljihu kafin ya ce " ki dai na kira na da yaya Zayd ba shi ne ba sunana "

a hankali ta matso kusa da shi ta ce " to minene Sunan ka "
" Nawfel " ya fada mata a takaice
" Zayd ba sunan ka ba ne , kuma ai na ji yaya Moussa ya na kiran ka da Amir "

" Zayd sunan kaka na ne , Shi ya sa Diya ba ya iya kira na da sunnan sai dai ya ce Amir "

ya na gama rufe bakin shi ya ji ta zagayo da hannayan ta ta baya ta rungume shi , ta kontar da kan ta saman bayan shi ta na fadin " ni dai da yaya Zayd zan ci gaba da kiran ka , ni da wannan sunnan na san ka , kuma , shi zan rike "

hmm ita ba ta san Amir ya riga da ya bar duniyar mutane
ya na jin ta zagayo da hannayan ta ya dauke kamar wutar nepa

cen cikin zuciyar shi ya ce " yarinyar nan ta na shirin kashe ni wlh "
[16/09 à 09:57] M.N.M:

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤

(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

💔🥀 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) 💔🥀

👑❤ MALLAKIN MEERAH ❤👑

【THE ROYALTY LOVE 👑🕊💖】

Marubuciyar littafin
【TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺】

【 BOOK …………………………… 2 ❤ 👑✌】

____________________🕊🌹🕊🌹🕊🌹🕊🌹🕊🌹🕊🌹🕊🌹🕊🌹___________________

{PAGE _______7 ❤🔥}

yar karamar dariya Abdoul ya yi kafin ya ce " mama ni fa ba tsoron shi na ke ba , kawai dai yanzu ya fi karfin na je a na kiran shi , sai dai shi ya kira mu "

shiru mama ta yi ba ta ce komai ba ta na ci gaba da shafa kan Nesrine da barci ya dauke

▪AFTER SOME HOURS

▪AMIR

zaune su ke shi da Malik a cikin parlourn su da ke hawa na uku
su na zaune bakin Glass su na kallon Masarautar
su na a haka kawai su ka ga Inaya ta fito da ga part din MALIKAT INAS , ta na sanye da wata gown fara kal mai mugun kyau ba ta daura Alkyaba ba , ta saki wannan lalawsan gashin kan ta ya zubo mata har tsakar baya ta na tafiyar ta cikin konciyar hankali

tun da ta fito AMIR ya tsare ta da wadanan hazel eyes din na shi har maganar da Malik ke yi mishi komai bai ji ba

a hankali Malik ya juya kan shi ya kali saitin da AMIR ke kallo
nan ya ga Inaya ta na tafiyar ta a hankali cikin masarautar gwanin burgewa

dan karamin murmushi Malik ya saki kafin ya kai hannun saitin fuskar AMIR ya kyasta mishi yatsun
a hankali AMIR ya lumshe idanun shi kafin ya bude su ya juya ya kali Malik ya na daga mishi gera guda allamun minene

" me ka ke kallo ne haka tun dazu na ke yi maka magana amma hankalin ka ba ya tare da ni "

juya kan shi AMIR ya yi ya na fadin " nothing " a takaice
" shikenan fada min me ke tsakanin ka da yarinyar cen da ka tsare da ido " Malik ya fada ya na daga mishi gera kamar ya na kallon shi

dan jinkirtawa AMIR ya yi kafin ya bude bakin shi murya kassa kassa ya ce " She is my wife , your daughter-in-low , ko ka na da ja ? "
a dubu dari Malik ya mike tsaye ya na fadin " what , Matar ka fa ka ce min AMIR , yaushe hakan ta faru "

ba tare da ya juyo ya kale shi ba ya ce " two years , Tsawan shekara biyu yanzu da yin auren "

wani kyawatencen murmushi ne Malik ya saki ya na komawa ya zauna saman chair din shi ya ce " ba banza ka ki dawowa , ashe yarinyar mutane ka samu "
shi dai AMIR shiru ya yi bai ce mishi komai ba ya ci gaba da kallon Inaya

" Bayan dawowar mu da ga Makka za ta dawo part din ka da zama " Malik ya fada ya na kallon AMIR

a hankali AMIR ya juyo ya kali Malik ya ce " Makka kuma ? "
" eh , ko ka manta tafiyar da mu ke yi duk watan azumi ? "
dan lumshe idanun shi AMIR ya yi shi ya ma manta da wannan tafiyar da su ke yi shi da Malik , shi gaskia ba ya jin zai iya yin tafiyar nan ya bar Inaya a cikin masarautar nan ita kadai

a hankali AMIR ya bude idanun shi , har ya bude baki zai yi magana , ya rufe bakin shi ya tashi a hankali ya bar wajen
da kallo Malik ya raka shi har sai da ya fice bai ce mishi komai ba

▪INAYA

a hankali ta ke tafiyar ta cikin masarautar , ga wani kyawatencen murmushi konce saman fuskar ta , ta na tafe ta na dube duben ta , har ta karaso cikin garden

ta na tsaka da tafiyar ta kawai ta ji ta buge mutun
a hankali ta dago kai ta na kallon ta Rouksar ta na saki wani cool murmushi ta ce mata " Yi hakuri ban gan ki ba ne "
ta kai karshen ta na shirin rabawa ta geffen Rouksar za ta wuce

ba shiri ta ji an riko hannun damtsen ta
cak Inaya ta tsaya ta juyo ta na kallon Rouksar
a hankali Rouksar ta dawo Gaban Inaya ta tsaya sannan ta fara yi mata kallon wulakanci

ita dai Inaya shiru ta yi ba ta ce komai ba
sai da ta gama kallon na ta sannan Rouksar ta ce mata " kar na sake ganin kusan AMIR "
cikin rudu Inaya ta ce mata " wanene AMIR kuma ? "

wata yar karamar dariya Rouksar irin ta rainin hankali kafin ta ce ma Inaya " kin ma raina min hankali yarinyar nan , ki na nufin ba ki san wanene AMIR ba "

a hankali Inaya ta girgiza mata kai allamun a'a
" shikenan tun da ba ki san shi ba , amma zan fada miki wani abu , kar ki kuskura ki ce za ki shiga gona ta , Idan kuma ki ka shiga , za ki iya rasa rayuwar ki , idan kunne ya ji , jiki ya tsira "
ita dai Inaya da ido kawai ta ke bin dan ba ta ma san maganar me ta ke yi ba

Rouksar kuma ta na gama fadar haka ta raba ta geffen ta ta wuce
har ta yi taku biyu ta tsaya cak , a hankali ta juya ta ga ita ma Inaya har ta juya

wani murmushin mugunta ta saki kafin ta juya ta kai hannu ta tura Inaya ta fadi kassa
wata yar karamar kara Inaya ta saki ta na dago kai ta kali Rouksar

nuna ta da dan yatsa Rouksar ta yi ta na fadin " wannan kadan ma ki ka gani duk ranar da na sake ganin ki tare da shi sai na yi miki abun da ya fi haka " ta na gama fadar haka ta juya ta ci gaba da tafiyar ta

da kallo Inaya ta rakata har sai da ta bar wajen sannan ta murguna mata baki ta na yi mata gwalo kamar kamar yarinya
sannan ta fara kokarin mike wa tsaye , sai dai wajen tashi ta taka gown din ta , nan take ta yage har zuwa saman cinyar ta

nan take idanun ta su ka kawo ruwa , ta kai hannu ta matse tsagar kamar ta yi kuka ta ce " Allah ya isa , muguwa kawai "

kamar da ga sama ta jiyo Muryar AMIR da ga bayan ta ya na fadin " ke da wa kuma ? "
a razane ta juyo ta na kallon shi idanun ta cike da ruwa
da gudu ta fada jikin shi ta rungume shi ta na sakin kuka ta ce " yaya Zayd ba wacen yarinyar ba ce , ban yi mata komai ba ta tura ni na fadi yanzu ga shi riga ta ta cire "

a hankali ya kai hannu ya dago ta da ga jikin shi ya na fadin " shikenan mu je ki sauya rigar "
rage sautin kukan ta ta yi ta na fadin " yaya Zayd ta fa yage sosai , ba zan iya tafiya a haka , kuma ka na gani b...... "
ba ta karasa maganar ta ba ta ji ya sa hannayan shi biyu ya dauke ta cak kamar baby , ba tare da ya ce mata komai ba ya nufi part din MALIKAT INAS
shiru ta yi ta na kallon Face din shi , yadda ya sauya mata lokaci guda kamar ba shi ne yaya Zayd din ta ba
duk in da ya wuce sai guard sun sara mishi , in kuma dogarai ne sai sun runsuna sun sunkuyar da kai su na bin shi da kallo ta wutsiyar ido
Amir kuwa ko a jikin shi ya na dauke da babyn shi

a haka har su ka iso part din MALIKAT INAS
babu ko sallama ya shigo parlourn MALIKAT INAS , su na zaune ita da RIANNA
su na ganin shi dauke da Inaya su ka saki wani kyawatencen murmushi a tare , su ka raka shi da ido babu wanda ta ce mishi ufan har ya shige corridor

ya na shiga corridor murya kassa kassa ya ce ma Inaya " where is your bedroom ? "
da yatsa ta nuna mishi bedroom din da su ke ciki ita da Nesrine
bedroom din ya nufa ya sa kafa ya tura ta sannan ya shiga

bakin gadon ya karaso sannan ya sauke ta saman kafafun ta ya na fadin " Shikenan yanzu tafi ki sauya kayan
Chapter 14 · 0% Book details