← Book details Exiled Prince Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 27

Sashe 12

Exiled Prince Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bayan sun baro AMIR da Inaya kai tsaye part din MALIKAT HOUDA su ka nufa
A tare duk su ka yi sallama kafin su ka karaso cikin parlourn inda MALIKAT HOUDA ke zaune saman sofa ga table a gaban ta shake da fruits

a gaban ta su ka zube saman guyiwowin su sannan Diya ya ce " gaisuwa na ke ya shugaba ta "

dan karamin murmushi MALIKAT HOUDA ta yi kafin ta ce musu su tashi ita ba ta son wannan gaishe gaishen na shirme

yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya ce " An gama ran ki shi dade , dama mun zo ganin mahaifiyar su ne "

" ka ce yaran Amina ne , Masha Allah , sannun ku to , tashi ku je ta na cikin daki na uku " MALIKAT HOUDA ta fada ta na murmushi , matar nan ba ta da matsala sam ita kowa na ta ne dalilin da ya sa ma AMIR ya ce a kawo mama wajen ta

ba musu su ka tashi su ka nufi corridor din bedrooms su ka shiga ta uku
nan su ka tardo mama zaune saman gadon ta , ta kurewa waje guda ido kamar mai tunanin wani abu

Nesrine na ganin ta yi gudu ta fada jikin ta na sakin kuka
sai a lokacin mama ta dawo cikin hayacin ta , ta daura hannun ta guda saman bayan Nesrine ta na fadin " lafiya ki ke kuka tun da safe haka "

a hankali Nesrine ta dago da ga jikin mama ta kai hannu ta fara goge hawayen ta , ta saki wani dan karamin murmushi ta ce " ba komai mama kawai na yi kewar ki ne "

dan karamin murmushi ita ma mama ta yi kafin ta juya ta kali Diya da Abdoul da ke tsaye bakin kofa ta ce " Abdoul , Moussa ku nan za ku tsaya "

yar karamar dariya Abdoul ya yi kafin ya karaso cikin dakin ya na fadin " mama ba fa sunan shi Moussa , sunan shi Diya "

" Toooo , da gaske ne malam Moussa " Mama ta fada ta na kallon Diya

dan karamin murmushi ya yi kafin ya gyada mata kai allamun eh da ga haka kuma ya ce " ni zan koma , zan dawo inda na samu dama " ya na gama fadar haka ya juya zai bar dakin

sai da ya fita sannan mama ta kali Nesrine murya kassa kassa ta ce " ba za ki tashi ki raka shi ba "

turo dan bakin nan nata ta yi ta na shirin magana mama ta riga ta cewa " idan ba ki tashi ba sai na sabba miki "

ai ko ta na jin hakan ta yi sauri ta tashi ta bi bayan Diya
ta ko yi sa'a bai gama fita corridor din ba sai ta yi mishi gyaran murya sama sama

cak ya tsaya ya juyo a hankali , ya na ganin ita ce ya saki wani cool murmushi ya ce mata " lafiya ? ki na bukatar wani abu ne "

A hankali ta girgiza mishi kai kafin ta fara takowa gare shi a hankali ta tsaya gaban shi ta dan sunkuyar da kai ita ta ma rasa abun da za ta ce mishi

dan karamin murmushi ya saki kafin ya kai hannu saman habar ta ya dago kan ta , ba shiri ya kai dan bakin shi saitin kumatun ta ya yi mata kiss sannan ya ce " ni ma zan yi kewar amma ba zan jima ba " ya na gama fadar haka ya janye hannun shi ya juya ya ci gaba da tafiyar shi

ita dai malama Nesrine ta yi sumar tsaye abun da ta zo fada daban abun da ya gane daban , a hankali ta dago hannu ta daura saman kumatun ta
ba ta san lokacin da wani cool murmushi ya subce mata ba , da sauri ta kai hannayan ta biyu ta boye fuskar ta ta na ci gaba da murmushin ta wai ita ta ji kunya

( da ga baya kenan 🤣🤣🤣🤣 )

sai da ta gama tsayuwar ta sannan ta juya ta koma dakin mama
ta na shiga ta Haye saman gadon baki daya ta konta ta tada kai da cinyar mama
dan karamin murmushi mama ta yi kafin ta daura hannun ta saman kan Nesrine ta ce " ina ku ka baro min auta "

murmushi mai dan sauti Abdoul ya yi kafin ya ce " su na tare ita da Zayd "
" ina son Ganin su don Allah " mama ta fada ta na marairaice fuska

yar dariya Abdoul ya yi kafin ya ce " mama ni dai yanzu tsakani na da Zayd sai dai gaisuwa , wlh ba zan iya tafiya ba na ce ki na neman sa , karfi na bai kai cen ba , ita dai Auta ba matsala Nesrine sai ta kirawo miki ita "

" To abun har ya kai haka yaushe ka fara jin tsoron Zayd " mama ta fada cikin zolaya
[16/09 à 09:57] M.N.M:

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤

(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

💔🥀 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) 💔🥀

👑❤ MALLAKIN MEERAH ❤👑

【THE ROYALTY LOVE 👑🕊💖】

Marubuciyar littafin
【TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺】

【 BOOK …………………… 2 ❤ 👑】

____________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊___________________

{PAGE _______8❤🔥}

ta na gama fadar haka ta bace bat a wajen
( bari dai mu bi ta mu ji ina ta tafi 🤔🤔 )

sai ga ta nan tsaye ta bayan masarautar wajen da ko guards babu a wajen ita kadai tsaye kasan wata katuwar bishiya
ta na tsaye a haka wani mutun ya fito zaune a kassan bishiyar , Ya na sanye da wadanan kayan na shi bakake , kamar dai kullum fuskar shi a rufe ta ke , da rawanin nan baki , idanun shi kadai a ke iya gani

a hankali ya bude baki ya ce " lafiya ki ka kirawo ni "

cike da bacin rai Rouksar ta ce mishi " Damba , akwai matsala fa , yarima ya na tare da wata shegiyar yarinya da ta lake mishi , shi kuma ba ya ce mata komai "

cikin ko in kula Damba ya ce mata " sai me , kema ba mace ba ce ki jawo hankalin shi mana , kar ki sake kira na da wannan shirmen , ba da zama ki ka shigo masarautar nan ba , mulkin saudiya za ki amso mana dan haka ki tashi ki yi aikin da ya kawo ki , ko kuma "
ya na gama fadar hakan ya ga wani dankareren maciji ya nufo shi ya na neman ya sare shi

cikin zafin nama ya damko kan macijin nan ya na kallon Rouksar ya ce mata " ke Medusa , ki kula da abubuwan wasan ki " ya na gama fadar haka ya tila mata macijin a fuska da ga nan ya bace a wajen ya bar nan tsaye
kamar da wassa macijin nan ya koma cikin gashin ya bace bat cikin jelar , nan take ita ma ta bace , sai ga ta dawo cikin toilet

kofar ta nufa ta bude ta ta fito , kai tsaye bedroom din ta fito ta dawo cikin parlourn inda ta bar tesnim ko motsi ba ta yi ba , ko sannu ba ta ce mata ba ta nufi wajen da ta taso ta koma ta zauna ta dauki wayar ta

* AMIR

zaune su ke cikin dining room din part din Malik , kamar dai kullum abincin dare a tare su ke cin shi
tsawan shekaru yanzu rabon su da su yi diner tare da Amir , musaman Malik ya ba da umarni a shirya duk wani abinci da Amir ke so , Table din a shake ta ke kamar unguwa guda za ta ci abincin , amma su shidda ne kadai wannan uban duniyar

abincin su su ke ci cikin konciyar hankali babu wanda ya ce ko ufan
su na a haka Malik ya katse shirun su da cewa " Ina son ku ba ni hankalin ki duka , zan so na yi muku wata magana "
a tare Malikat Inas da Malikat Al'umu su ka hada baki wajen cewa " Wace magana ce wannan kuma ? "

dan jinkirtawa Malik ya yi kafin ya ce " Daya da ga cikin yaran da Amir ya dawo da su Matar shi , tsawan shekara biyu yanzu da yin auren su , ba na son jin korafin kowa a nan , Malikat Inas MALIKAT AL'UMU ku na ba wa hakin kulla da ita , ina son ku koya mata duk wani abun da ya dace , bayan dawowar mu da ga Makka za ta dawo dakin mijin ta "

baki sake Tesnim da MALIKAT AL'UMU ke kallon Amir su na zaro idanu
RIANNA da MALIKAT INAS ko sai murmushi su ke yi dama sun san da maganar auren
sarai ya lura da su amma bai ce musu ko ufan ba , Ya ci gaba da cin abincin shi
su na a haka su ka jiyo Muryar Malik ya na kiran Azim

da sauri Azim ya karaso wajen Malik ya Zube saman guyiwowin shi cike da girmamawa ya shiga gaishe su baki daya
daga mishi hannu Malik ya yi allamun ya yi shiru sannan ya ce " je ka kira min yarinyar da ke part din MALIKAT INAS , karamar "
ya na gama fadar haka Azim ya mike da gudu ya fice parlourn ya bar building din baki daya ya nufi part din Malikat INAS

ya na barin wajen Malik ya kali Amir ya ce " Nawfel ? "
slowly Amir ya dago kai ya kali Malik ba tare da ya ce komai ba
cike da zolaya Malik ya ce " Ba ka da abokin da zai raka ka dakin amaryar ka , ko na kai ka da kai na "
Chapter 12 · 0% Book details