← Book details Exiled Prince Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 27

Sashe 11

Exiled Prince Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru ya yi na dan lokaci kafin ya ce " na san malam ya fada miki auren da ke tsakanin da Diya kafin ya rasu "

Sunkuyar da kai ta yi kafin ta ce " Eh ya fada min , ranar da wadanan mutanan su ka zo gida su ka tafi da shi "

Gyada kan shi ya yi a hankali kafin ya ce " ina fatan ba ki da matsala da hakan "
Girgiza mishi kai ta yi allamun babu
" okay , Gabe za ki bi shi masarautar su ya gabatar da ke ga Familyn shi , Idan kuma a nan ki ke son zama ba matsala za a ware muku part "

Da sauri ta ce mishi " ni a nan zauna tare da Mama da Inaya , ba zan iya yin nesa da su ba " ta kai karshen kuka ya na kubce mata

A hankali AMIR ya hannu ya janyo ta jikin shi ya rungume ta dan ya san ba komai ba ta ke yi wa kuka ba face malam , ko shi hakan ya ji cikin zuciyar shi da ya kira sunan shi amma ba yadda zai yi dole ya danne

Sai da ya ji ta yi shiru sannan ya sake ta ya ja hannun ta su ka koma cikin runfar nan
Ya na zuwa ya mikawa Diya hannun ta
Murmushi Diya ya yi kafin ya riko hannun ta ya janyo ta ta zauna tsakiyar su shi da Abdoul ta na sunkuyar da kai

Shi kuma ya koma geffen Inaya ya zauna ,
Ya na zama Azim ya karaso wajen ya Zube gaban AMIR ya na fadin " gaisuwa na ke ya shugaba na , mai martaba na son ganin ka a Fada yanzun nan "

Shiru AMIR ya yi na dan mintina kafin ya ce " za ka iya tafiya "
" godiya na ke ya shugaba na " ya na gama fadar haka ya tashi da sauri ya bar wajen

Ya na barin wajen AMIR ya daga kan shi sama ya lumshe idanun shi
" AMIR ba za ka je ba ne " Diya ya fada mishi dan ya ga allamun ba ya da niyar tashi
Shiru AMIR ya yi bai ce mishi komai ba , bai kuma saukowa da kan shi ba
Ya na a haka ya ji kawai an kontar da kai saman cinyar shi
Slowly ya sauko da kan shi ya bude idanun shi , ya na kallon ta
Allamun barci ta ke ji dan har ta lumshe idanun ta , ta daura kafafun ta saman Sofar
Bai ce mata komai ba ya daga kan shi ya lumshe idanun shi

" Rouksar tashi mu tafi ko ? " TESNIM ta fada ta na mikewa tsaye
Karewa AMIR da Inaya kallo Rouksar ta yi kafin mike ta bi bayan TESNIM su ka bar wajen
Su na barin wajen shi ma Abdoul ya mike ya na fadin " Diya ina mama ta ke ina son ganin ta "

Cikin nitsuwa AMIR ya riga Diya cewa " ta na part din MALIKAT HOUDA "
Gyada mishi kai Diya ya yi kafin ya mike ya riko hannun Nesrine ya ce su tafi Abdoul na biye da bayan su , su ka bar AMIR da Inaya a wajen

sannu sannu har AMIR da Inaya su ka share wajen good on hours a haka
ita ta yi barci shi kuma ya tafi duniyar tunanin shi , Allah kadai ya san abun da ya ke tunani

ya na a haka kawai ya sake jiyo Muryar Azim ya na yi mishi sallama
Dan karamin tsaki ya yi kafin ya sauko da kan shi , shii ya ma manta da cewa a na jiran shi a Fada

gaishe shi Azim ya yi kamar yadda ya saba sannan ɗaura da cewa Malik na son ganin shi a part din shi
"Okay " ya fada a takaice kafin ya sa hannu a hankali ya sauke kan Inaya da ga saman cinyar shi ya mike tsaye

sannan ya juya ya dauke ta cak kamar baby ya juya ya fara takawa ya bar wajen Azim na biye da bayan shi dan wannan karan Malik ya ce kar ya dawo ba tare da AMIR ba

shi kuma AMIR kai tsaye part din MALIKAT INAS ya wuce da Inaya
da sallama cen kassan makoshi ya shigo parlourn MALIKAT INAS
nan ya tardo ta zauna ita da RIANNA su na hirar su

su na ganin shi dauke da Inaya su ka mike su ka nufe shi a rude su na tambayar me ya same ta
bai bi ta kan su ba ya wuce ya kontar da ita saman Sofa sannan ya juyo ya kale su ya ce " barci ne ta ke yi " ya na gama fadar haka ya raba ta geffen su ya wuce ya fice part din

wani cool murmushi RIANNA ta yi kafin ta tako ta zauna kusan Inaya ta ce " Ammie , ina ji a jiki na yarinyar nan she is so special for AMIR , duba ki yadda ya ke kula da ita kamar baby "

ita ma MALIKAT INAS wani dan karamin murmushi ta yi kafin ta koma inda ta taso ta zauna ta na fadin " dole ya kula da ita saboda ya na son ta , zalar so ya ke yi mata amma har yanzu ya kassa yarda da hakan , Idan har AMIR ya bude baki ya ce ya na son yarinyar nan zan fi kowa farin ciki , she is so innocent , abun da na lura da shi ta fi yar uwarta nitsuwa , za su dace sosai da juna , Sai dai kashh ya ki karbar soyayyar da ke cikin zuciyar shi "

" To yanzu Ammie ya ki ke so mu yi "

shiru MALIKAT INAS ta yi na dan lokaci kafin ta ce " ba abun da za mu yi , kawai za mu sakawa ikon Allah ido , Tun da har ya hada su , Haka zalika zai sa soyayyar da ke cikin zuciyar AMIR ta fito fili , na mu kawai mu taimaka musu idan za mu iya "

kara fadada murmushin ta RIANNA ta yi ta na fadin " Ammie Allah ma ya ce tashi na taimake ka , dole sai mun saka Hannu cikin lamarin su "

" To ya ki ke so mu yi , ni fa ban taba jin AMIR ya bude baki ya ce ga kalar matar da ya ke so bare har mu yi wani kokarin sauya ta "

" no Ammie ba wani sauyawa , a hakan ma ta yi , ni dai na san AMIR ya na son mace mai kwaliya , ba ki lura da irin kallon da ya ke yi mata dazu da safe , ni dai na san ko bai fada ba , kwaliyar ta ta burge shi "

yar karamar dariya MALIKAT INAS ta yi kafin ta ce " Oh dama kin san da wannan shi ya sa ki ka shirya ta tun da safe haka "

" me ki ke tunani na sani mana , ai duk fadin masarautar nan babu wanda ya san AMIR sama da ni , ke dai ki sha zama kawai za ki sha kallo " RIANNA ta fada cike da kwarin guyiwa allamun ta shirya wata a kassa

ita dai MALIKAT INAS ba ce komai ba kawai ta zuba wa Inaya idanu

▪AMIR

bayan ya fito part din MALIKAT INAS kai tsaye part din Malik ya wuce , kafin ya shiga sai da ya cire Alkyabar shi ya mikawa Azim da ke biye da shi sannan ya shiga building din
kai tsaye hawa na biyu ya nufa , nan ya tardo Malik tare da wasu manyan mutane biyu

ko gaishe su bai yi ba , sallamar shi ma shi kadai ya ji abu ne
kai tsaye ya nufi wata sofa ya zauna , zaman nan irin na gasaita

sai da ya zauna sannan Malik ya ce mishi " AMIR , Azim bai fada maka ka same ni a fada ba "

cikin ko in kula AMIR ya ce " ya fada min "
" Me ya sa ba ka je ba to , saboda kai musaman na shirya zama amma ba ka zo ba " Malik ya fada ya na nuna bacin ran shi
a hankali AMIR ya gyara zaman shi ya na fadin " Next time "

dan murmushi Malik ya yi ya na gyada kan shi kafin ya ce " okay na san ba za ka manta da wadanan nan ba , Sarkin Dogarai Hussein Bin Hashim da kuma Sarkin Bayi Mohammed Magid "

gyada kan shi a hankali AMIR ya yi kafin ya ce " Yes ban manta da su ba , ba wannan ne ba ya taba tsula min bulalar bayin shi ba " ya fada ya na nuna Sarkin bayi da ido

a tare duk su ka yi dariya sannan Sarkin bayi ya ce " To ina neman Afuwar Yarima , akasi ne a ka samu a ranar "

dan tabe baki AMIR ya yi ya na kauda kan shi gefe
sai da su ka tsagaita dariyar su sannan Malik ya ce " Kar ka manta matsayin uncle din ka su ke "

cikin nitsuwa AMIR ya katse shi da cewa " Abbi ba sai ka fada ba na sani , wannan shi ya ke auren MALIKAT MANISHA yarinyar MALIKAT HOUDA , Wannan kuma Yarinyar MALIKAT YOUSSRA " ya fada ya na nuna Sarkin bayi da ga karshe

Jinjina kan shi Hussein ya yi kafin ya ce " Ashe dai ba ka manta da mu ba "
" no " ya fada a takaice kafin ya mike ya nufi lift ya shiga ya nufi hawa na uku , ya na hawa ya wuce kai tsaye bedroom din shi

A cen kassa kuma inda ya baro Malik , sai da su ka Kamala tatauna war su a kan matsalolin da su ka shafi masarautar sannan ko wane ya tashi ya kama aikin gaban shi

▪NESRINE
Chapter 11 · 0% Book details