← Book details Exiled Prince Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 27

Sashe 2

Exiled Prince Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su na barin wajen ya dago kai ya fara bin wajen da kallo , amma bai ga komai ba
A hankali ya ci gaba da takawar shi har ya nufi wani dan building mai mugun kyau , ga wasu jibga jibgan dakaru zagaye da wajen

Ya na isa wajen duk dakarun su ka zube saman guyiwowin su su na gaishe da shi
Bai bi ta kan gaisuwar su ba ya shiga wajen kai tsaye ya na sallama kassa kassa babu wanda ya ji ta sai shi da ya yi abun shi

Ya na shigowa wajen idanun shi su ka sauka kan wata mace sanye da wando palazzo Fari kal da riga ita ma fara ta na da madauri da ga tsakiya , ta saki wani lalawsan gashin kan ta baki kirin har tsakiyar bayan ta
Ta juyawa kofar shigowa baya , ta na kallo ta cikin wata katuwar Window ta glass

A hankali ya ci gaba da takawa , ya sa hannu ya cire alkyabar shi ya ajiye saman wata table ya daura arrow din a sama

Kamar ta san da shigowar shi , ba tare da ta juyo ba ta ce " calm down , ni ba da niyar fada na kira ka ba " ta fada da larabci

Ya na shirin daukar takobi ta fadi hakan
Ya na jin abun da ta fada ya juya ya fara takawa ya karaso geffen ta ya tsaya ya nade hanayan shi a kirji ya na kallon cikin Window din shi ma

Sai da su ka dauki lokaci a hakan kafin ta juyo slowly ta kale shi
Kyakyawar budurwa ce mai jini a jika , ta so ta dan yi kama da NAWFEL , amma kuma kama ta jini , sannan launin idanun ta hazel ne kamar na shi bayan haka ba abun da ya yi kama tsakanin su , a shekaru za ta kai 27 haka ina kyautata zaton wannan ita ce RIANNA BIN JAABAR

Cikin sanyi murya ta ce " Amir , wai me ya ke damun ka ? "

Girgiza mata kai ya yi ba tare da ya kale ta ba allamun ba komai
Hannu ta kai ta shako wuyan shi ta kai mishi bugu a ciki , ta na fadin " Wa za ka yiwa miskilanci , kar ka manta na girme ka fa "

" Please Ukhtie let me " ya fada cikin siririyar murya
Sakin shi ta yi kafin ta sa hannu ta tura shi kadan har ya yi baya zai fadi
Cikin zafin nama ya taro kan shi ya mike tsaye ya na kallon ta

Nade hanayan ta ta yi a kirji ta na kallon shi ta ce " za ka fada min ko sai na karaya ma ka hannu " ta kai karshen ta na daga mishi gera guda

Ajiyar zuciya ya sauke , kafin ya ce " wlh ki na son takura min dayawa ni na fada miki ba abun da ke damu na "
Ya kai karshen ya juya , ya fara takawa ya na neman ya bar wajen

Da sauri ta sa kafa ta tade shi , ya fadi dib ga kassa
A hankali ya dago ya mike zaune ya na kallon ta ya shagwabe fuska kamar karamin yaro ya ce " wai me na yi miki da za ki dake ni haka in da kin ji min ciwo wlh sai na fadawa Abbi "

Yar karamar dariya Ta yi kafin ta zaune kassa ita ma ta na kallon shi ta ce " ban son shirme AMIR wa za ka yi wa shagwaba , ko kunya ta ba ka ji , ni yanzu fada min , mi ke damun little brother di na " ta kai karshen cikin zolaya

Kauda kai gefe ya yi ya na dan turo karamin bakin nan nashi ya ce " ni kyale ni ba abun da ke damu na "
Dariya sosai ta yi , ta na kallon shi ta ma rasa abun da za ta ce mishi
[16/09 à 09:57] M.N.M:

❤⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❤

(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

⚘🕊 MALLAKIN MEERAH 🕊⚘

【 CUTIE PIE 】

Marubuciyar littafin :【 TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 】

YOU CAN FOLLOW MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

BOOK .............. 2 🌹👑

【 THE ROYALTY LOVE ✌👑🌹】

________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊________________

P A G E 2 ❤ 🔥

Dawo kallon shi ya yi kan ta ya na matse gera ya ce " ki bar min wannan dariyar ta ki ta keta "

Tsagaita dariyar ta ta yi kafin ta ce " okay , okay , Akhie fada min me ya ke damun ka "

Sai da ya dan jinkirta kafin ya ce " Ukhtie , Abbi ya ce gobe zan fara bin shi fada , dan in ga yadda ke kula da masarauta "

" okay , minene matsalar to , ko ba ka son zuwa " ta tambayeshi

" ni fa na fada mishi ba ni son zama MALIK bayan shi amma ya ki sauraro na " ya fada cikin sanyi

Daura hannun ta ta yi saman kafadar shi ta ce " in tambaye ka , in ba ka hau mulkin Saudiya ba , me za ka yi , kai kadai ne fa yarima cikin ahalin mu "
Dan turo baki ya yi cikin shagwaba ya ce mata " ni na fada mishi company Sarrafa petroleum na ke son budewa , kar ki manta ko a school business na ke karantawa , amma ya na neman ya daura min abun da ya fi karfi na , ni gaskiya ba zan iya mulkar mutane ba "

Yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " gaskia kam ba za ka iya ba , da wannan shagwabar za ka zama Malik , ko Tesnim ba za ta gwada ma ka shagwaba ba "

Hararrar wassa ya wurga mata ya na shirin magana ta mike tsaye ta mika mishi hannu ta na fadin " let's go see Abbi mu yi mishi magana a tare "

Da sauri ya mika matta hannu ya mike tsaye ya na murmushi
Ya na mikewa ya ji kamar karar faduwar karfe a wajen kofar shigowa wajen
A tare su ka kai duban su a wajen kafin Amir ya fara takawa a hankali ya nufi wajen da ya jiyo karar
Cikin nitsuwa Ta tsayar da shi da cewa " ina kuma za ka je ka bar alkyabar ka " ta fada ta na fara takawa ta nufi table din ta dauki alkyabar sannan ta nufo shi ta ce mu tafi ko
Ba musu ya bi bayan ta su ka bar wajen a tare ta na rike da Alkyabar shi

Su na barin daya da ga cikin dakarun da ke tsaron wajen ya juya ya bar wajen da sauri sauri
Sai da ya karaso kassan wata katuwar bishiya cen bayan masarautar inda babu kowa ko me wucewa babu sannan ya tsaya ya Zube saman guyiwowin shi ya na sunkuyar da kai ya ce " gaisuwa na ke ya shugaba na "

Wani mutun ne zaune kassan bishiyar ya na sanye da wasu kaya bakake Dukan su , Idanun shi kadai a ke iya gani saboda ya rufe fuskar shi da wani bakin harami baki shi ma
Cikin wata murya cike da isa ya ce " ya a ke ciki ne ? "
Ba tare da ya dago kan shi ba ya ce " ya shugaba na , na jiyo Amir na fadin zai fara shiga Fada tare da Malik "

Da sauri mutuman ne ya katse shi da cewa " sai in ya na raye zai shiga Fadar "
" Haka ne shugaba na "
" gobe ina son in ji labarin mutuwar Amir , idan kuma ta wuce gobe kai za ka mutu a madadin shi Meli "

Murya na kerma Meli ya ce mishi " in sha Allah ba za a samu matsala ba shugaba na , duk wani shirye shirye da za a yi mun yi shi , lokaci kawai mu ke jira "

Jinjina kan shi mutuman ya yi kafin ya ce " ina jiran albishir mai dadi Meli , ni kuma zan cika maka alkawarin ka "

" Godiya na ke ya shugaba na , Allah ya ja zamanin ka , Allah ya kare gaba da bayan ka ya shugaba na "

Daga mishi hannu mutumin nan ya yi kafin ya ce " ya isa haka tashi koma bakin aikin ka "
" godiya na ke ya shugaba na " Meli ya fada kafin ya mike kai a sunkuye ya bar wajen
Ya na barin wajen mutumin nan ya bushe da wata shegiyar dariya ya na fadin " sai dai ka yi hakuri dan uwa na amma dole Mulkin saudiya ya dawo cikin tafin hannu na , ko da kuwa Malik din da kan shi zan kashe " ya kai karshen ya na sake bushewa da dariya kafin ya bace bat a wajen

* MISALIN KARFE 8 NA DARE

Wani katuwar dining room dauke da wata kyawatatar dining table Fara kal dauke da wasu chair goma sha biyu suma farare kal gwanin burgewa
Table din shake ta ke da abincin kala kala da Fruits wannan abincin sai ya ciyar da gida je goma su ci su koshi har su samu na breakfast
Nan na hango mutanan gidan zaune saman chair su shidda ne mata hudu da namiji biyu
AMIR NAWFEL da wani dattijon wanda na san Shi ne MALIK din dan kamanin shi daya sak da AMIR NAWFEL har Hazel eyes din su
MALIK ya na zaune saman chair din da ke tsakiya , geffen shi na dama RIANNA ce zaune tare da MALIKAT INAS sak kamanin ta da RIANNA

Geffen hagun shi kuma AMIR NAWFEL ne zaune tare da TESNIM , sai MALIKAT AL'UMU ta so ta dan yi kama da AMIR NAWFEL amma ba sosai ba

A hankali MALIK ya dago kai ya kali AMIR NAWFEL da ya sunkuyar da kai ya na cin abincin shi , amma da ga gani ka san ba dan ya na son abincin ba ya ke cin shi
Chapter 2 · 0% Book details