← Book details Exiled Prince Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 27

Sashe 19

Exiled Prince Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shi kuma Amir ya na Shiga Bedroom din shi ya wuce kai tsaye cikin toilet
jim kadan ya fito daure da towel a kugunshi ya wuce kai tsaye dressing room
nan ma bai wani dauki lokaci ba ya fito sanye da wata jallabiya fara kal mai dogayen sai baza kamshi yake

ya na fitowa ya nufi wajen da daddumar shi ke shinfide ya Haye ya tada sallar shi cikin nitsuwa
bayan ya Kamala ya zauna ya na karatun kur'ani har sai da lokacin sallar la'asar ya zagayo ya tashi ya gabatar da ita
bayan ya Kamala ya yi aduo'in shi , ya mike tsaye ya cire jallabiyar jikin shi ya tila ta saman bed din sannan ya nufi bed din ya Haye ya yi rub da ciki , ya lumshe idanun shi , tun da ya dawo cikin masarautar ya ke jin wata muguwar kasala ta rufe shi , ba shi da aikin yi sai barci
bari mu leko wani bangaran na cikin masarautar kafin ya tashi

* DAMBA

zaune ya ke kassan Bishiyar nan dai , kamar kullum yau ma ya na cikin wadanan bakaken kayan na shi , ya rufe fuskar shi da bakin rawani , idanun shi kadai a ke iya gani

Rouksar na tsaye a gaban shi ta na fadin " Shirin mu ya fara tafiya yadda ya dace "

dan gyada kan shi Damba ya yi kafin ya ce " Tukunna Shirin mu bai fara ba "
cikin rudu Rouksar ta ce mishi " Ban gane abun da ka ke nufi ba , a sani na shirin mu shi ne na janyo hankalin Amir gare ni "

cikin nitsuwa Damba ya daga mata hannu ya katse ta sannan ya ce " Shiri na daban na ki daban , amma nan gaba za ki sani , ke dai ki yi kokari ki shawo hankalin Amir gare ki , tabass zai bukaci macen da za ta kontar mishi da hankali bayan dawowar shi da ga Makkah "

" Ni fa sam ban gane abun da ka ke fada " Rouksar ta fada dan ya na neman ya juya mata shirin da ta yi dangane da Amir

wata shegiyar dariya Damba ya yi sannan ya ce " Za ki gani nan gaba kadan " ya na gama fadar haka ya bace bat a wajen

ya na barin wajen Rouksar ta saki wani dan karamin tsaki ta na fadin " za ka ga abun da na shirya maka ! " ta na gama fadar haka ta saki wani makirin murmushi sannan ta bace bat ita ma

▪AMIR

misalin karfe 8 na yamma su na zaune a cikin dining room din Part din Malik kamar kowa ne dare dan su dining
kowa ya nitsu ya na cin abincin shi
Amir kuwa ya sunkuyar da kai sai juya spoon din shi ya ke cikin Plate din , da allamun hankalin shi na nesa

su na a haka su ka jiyo Muryar Malik ya na fadin " MALIKAT INAS , in sha Allah zuwa gobe za a kai miki kudin da a ke fitar wa sadaka kowace shekara wannan shekarar ke za ki raba "

har hada baki MALIKAT INAS da MALIKAT AL'UMU su ke su na fadin " amma ran ka shi dade ba ....... "

cikin nitsuwa ya daga musu hannu ya katse su sannan ya nuna Amir ya ce " ku tambaye shi , shi ya bada shawarar "

a tare su ka jiyo su ka kali Amir da ke ta faman juya spoon din shi , da allamun ba ya ma tare da su
su na ganin hakan kowace ta ja bakin ta , ta yi shiru dan sun san ko sun yi maganar ba zai amsa musu ba
haka su ka ci gaba da cin abincin su har sai da su ka Kamala kowa ya tashi ya yi tafiyar shi , Amir kuma ya koma bedroom din shi , da allamun yau na miskilancin su ka mishi busa

▪AFTER SOME DAYS

Tun safiya Manya' manyan motoci su ke shigowa Filin Daular
da ga Sarakunan masarautun da ke karkashin Daular saudiya har da ahalin Malik da kan shi da mazaunan fadar da ahalin su , kowa zowa ya ke ya na yi wa Malik da Amir Allah kiyaye hanya , ma su yi tsakani da Allah na yi , ma su muguwar manufa a zuciya su ma na nasu
Malik kuwa farin ciki ba a magana hakan ba karamin dadi ya yi mishi ba , Musaman ya sanya a ka shirya musu wallima dan tarben baƙin shi

▪MISALIN KARFE 10 NA DARE

duk Sarakunan da su ka zo yi wa Su Malik ban kwana kowane ya koma gidan shi , ahalin Malik ne kawai su ka yi saura

a wannan lokacin babu kowa cikin parlourn Malik sai Hussein , da Mohammed tare da Ahalin su , Gimbiya Manisha yarinyar MALIKAT Houda matar Hussein

sai kuma Gimbiya Aysher Yarinyar MALIKAT Youssra matar Mohammed
kowace ta na tare da yarinyar ta guda , da sunnan sun zo yi wa Amir Allah kiyaye hanya
yan mata ne biyu ma su jini a jika renon madara da ice cream ga kuma jinin Sarauta , ba laifi duk sun hadu iya hadu ga kyawo Masha Allah
Muntaz shi ne sunan ta wajen Gimbiya Manisha , a shekaru za ta kai 24 Haka
sannan kuma ta wajen Gimbiya Aysher , Hafsat a shekaru za ta kai 21 years

tun da su ka shigo parlourn Malik babu wanda ta ce ma yar uwar ta ufan wai su ji'ji da kai
sai tsuke fuska su ke su na shan tsami , su kali nan , su kali nan su na duba Amir , amma ina ko hango Bedroom din shi ba su yi

Su na a haka su ka jiyo wani mugun qamshi mai dadi ya daki hancin su , a tare duk su ka kai kallon su wajen da su ka jiyo qamshin

sun dauki wajen good on minutes a haka kafin Su ga Amir ya fito da ga cikin Corridor kai a sunkuye ya na latsa wayar shi
ya na sanye cikin wasu Tracksuit Farare kal , rigar ta na da hula , an Rubuta NIKE da launin Black da ga gaban ta , kafafun shi kuma cikin wasu sneakers Farare kal su ma abun dai Masha Allah , ya saka hannu guda cikin aljihun rigar sai baza qamshi ya ke kamar wanda ya yi wankan turare

kai tsaye ya shigo parlourn babu ko sallama , abun da ba su ni ba ya yi sallama amma shi kadai ya ji abu ne , Idan ba ka kali lips din shi ba da kyau ba za ka ce ya yi sallama ba

Muntaz da Hafsat na ganin kowace ta washe baki ta na kara yaba irin wannan kyawon na Amir

su na a haka ya zo ya nufi Hanyar fita wajen ko sannu bai ce musu ba
da sauri Malik ya taro shi ya na fadin " Amir ba ka ga mutane ba a wajen ? "
slowly ya dago kan shi ya kali su Hussein da matan su sannan ya ce musu " Hi ! " da ga haka ya juya ya ci gaba da tafiyar shi

" Nawfel ba za ka tsaya ka gaishe da Auntyn ta ka ba ? " Gimbiya Aysher ta fada cike da kissa

hmm ni kuma na ce kin yi a banza dan ko kallon inda ta ke bai yi ba ya sa kai ya fice
da sauri Hafsat ta mike ta bi bayan shi
kamar ko ya san haka za a yi , ya na fitowa ya ce ma Azim kar ya bar kowa ya fito wajen da sunnan zai biyo shi

Hafsat na isowa Kofar fita parlourn Azim ya tare ta ya na fadin " yi hakuri ran ki shi dade , Shugaba ya ce kar a bar kowa ya biyo shi "

ba dan ta so ba ta koma cike da bacin rai ta zauna kusan mahaifiyar ta ta , ta hura kumatu da iska wai ita ta ji haushi

duk abun da ya faru Malik na gani amma bai yi kokarin tsayar da Amir ba , sai da ya fita sannan ya shiga bawa Gimbiya Aysher hakuri ya na cewa wani aiki ne zai je yanzu zai dawo su yi sallama
da ga haka su ka ci gaba da hirar su

Amir kuwa ya na fitowa kai tsaye part din MALIKAT INAS ya wuce
( hmmm 🤔🤔🤔 ko me ya je yi a cen )

bakin shi dauke da sallama ya shigo parlourn ta , ya nufi Hanyar corridor ko dago kai bai yi ba bare ya san da mutum ko babu

har ya ka tsakiyar parlourn ya jiyo Muryar MALIKAT INAS ta na fadin " Amir lafiya dai ko ? ka zo ka wuce ni haka ko sannu babu "

a hankali ya tsaya da ga tafiyar shi ba tare da ya dago kai ba ya ce " lafiya Ammie "

dan karamin murmushi MALIKAT INAS ta yi kafin ta ce " shikenan zo zauna ina son mu yi magana "

a hankali ya dago da kan shi ya kale ta na dan wani lokaci kafin ya juya a hankali ya nufi Sofa ya zauna ya na kallon ta , irin kallon nan na son karin bayani

sai da ta dan dauki lokaci kafin ta ce " Amir ni fa ban san yadda a ke raba kudin nan na sadaka ba , ya za ka tashi lokaci guda ka ba ni ya zan yi yanzu " ta fada ta na dan marairaice fuska

wani dogon nunfashi ya ja kafin ya ce " Kar ki damu Ammie na san za ki yi abun da ya dace , dalilin da ya sa na ce a ba ki kudin na lura wanda su ka yi sadakar ba sa yin ta tsakani da Allah , kuma ban yarda da zubin su ba gaskia "

" to ya ka ke so a yi yanzu dan ni fa ba wani abu da na sani "
Chapter 19 · 0% Book details