Sashe 16
Exiled Prince Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cike da rudu RIANNA ta ce mata " Inaya , lafiya na ga Amir ya fita da sauri haka ba dai wani abu ki ka yi mishi ba "
a hankali Inaya ta girgiza mata kai ta na fadin " Aunty RIANNA ni ma ban sani ba , kawai na ga ya tashi ya fice "
" shikenan zan tambaye shi " RIANNA ta fada ta na shirin juyawa
da sauri Inaya ta ce mata " Aunty "
cak ta tsaya ta juyo ta na tambayar ta minene
girgiza mata kai Inaya ta yi kafin ta mike zaune , ta shiga cikin contact , ta nuna wa RIANNA screen din ta na fadin " Aunty mi haka ta ke nufi , ni ban gane larabci sosai "
a hankali RIANNA ta kai hannu ta karbi wayar
nan take ta saki wani kyawatencen murmushi ta na kallon sunnan da a ka yi register din number Amir dan ta gane numbar shi ce
" Inaya wa ya saka miki numbar Amir ? " RIANNA ta fada ta na mika wa Inaya wayar ta
hannu Inaya ta kai ta karba ta na fadin " yaya Zayd ya Saka min ita "
" shi kuma ya saka sunnan ? "
gyada mata kai Inaya ta yi kafin ta ce " eh shi ya sa na ce ki fada min me hakan ke nufi , ni ban gane abun da ya saka ba "
girgiza mata kai RIANNA ta yi ta na fadin " yi hakuri ni ma ban sani ba , amma ki bari shi da ya saka , ya fada miki da kan shi "
da to kawai Inaya ta amsa mata kafin ta koma ta konta ta ci gaba da game din ta
a hankali RIANNA ta juya ta fice dakin ta na murmushi cikin zuciyar ta ta na fadin " Gaskia Amir ka cika dan rainin hankali " ta kai karshen dai'dai ta shigo cikin parlour
MALIKAT INAS na ganin murmushin da ke saman face din RIANNA ta san ba banza ba , amma sai ta shanye dan ba ta son ta shigo cikin harkar yaran nan
▪AMIR
ya na baro part din MALIKAT INAS bai tsaya ko ina ba sai building din su
ya na shigowa parlourn su na uku ya tardo Malik zaune da wasu mutanan guda hudu , babu ko sallama ya shigo wajen ya nufi corridor
da sauri Malik ya ce " Amir dawo ina son magana da kai "
cak ya tsaya da tafiyar shi , har ya kai bakin corridor din , sannan ya juyo a hankali ya karaso cikin parlourn ya nufi sofa one seater ya zauna ya na kallon Malik
ya na zama Malik ya mika mishi wasu takardun da ke gaban shi saman table
da sauri Azim ya taso ya karaso wajen ya karbi takardun ya nufi Amir ya mika mishi cikin girmamawa
a hankali Amir ya kai hannu ya karba ya na fadin " na minene wannan ? "
kallon mutanan Hudu Malik ya yi ya ce " Wadanan dai ka san su ba sai na fada maka ba " ya fada ya na nuna Sarkin bayi , da Sarkin dogarai
sannan ya nuna wanda ke kusan sarkin Bayi ya ce " wannan kuma shi ne Miram bin Salman , mai kula da Bankin Daular "
sannan ya nuna na karshen ya ce " wannan kuma ,General Abdallah Mohamed , Shugaban masu tsaro , General of Army kuma , duk su na cikin mutanan Fadar Malik , kamar ko wace shekara kafin a fara azumi a na fitar da Ten Milliard , da ga Bankin Daular , dan a rabawa Al'uma , to wadanan Takardun ne ! ka san ban da gobe za mu tafi makkah , shi ya sa su ka zo dan mu tatauna a kai , zan so na ji ra'ayin ka yadda za a raba kudin "
shiru Amir ya yi ya na kallon takardun ya na karantawa
sai da ya karanta takardun tsab sannan ya ajiye takardun a kassa sannan ya jingina bayan shi a jikin sofar ya kali Malik ya ce " wa ke kula da raba kudin kowace shekara ? "
" Sarkin bayi " Malik ya fada a takaice
a hankali AMIR ya juyo ya kali Sarkin bayi ba tare da ya ce komai ba
sai da ya dauki wajen good five minutes ya na kallon sarkin bayi babu ko kiftawa kafin ya ce " a ba wa MALIKAT INAS kudin wannan shekarar "
" what ? " Sarkin bayi da Miram su ka fada a tare
sannan Sarkin bayi ya ɗaura da cewa " tare da dukkan girmamawa Amir , Kowace shekara mu mu ke kula da wannan ta ya za a tashi rana guda a bawa wani , wanin ma....... "
cikin nitsuwa Amir ya katse ta hanyar daga mishi hannu sannan ya kali Malik ya ce " ra'ayi na ka ce na fada kuma shi zan fada , ina son a duba cikin prisoner Din masarautar nan , wanda ya kusa kai karshen zaman shi , ko da ya haura wata biyar a sake shi , su koma gida jen su , zancen kudi kuma na san dalilin da ya sa na ce a bawa MALIKAT INAS , ita za ta fi sannin yadda za a yi da kudin , na san kowace shekara , da ga bayi sai dogaran masarautar nan ke samun kudin , shi ya sa na ce A kai wa MALIKAT INAS , ba ku sani ba amma yawwan cin mata sun fi wasu kaifin tunani da sanin abun da ya dace , Idan shawara ta ba ta yi muku ba , ku yi yadda ku ke so " ya na gama fadar haka ya tashi ya nufi corridor ya shige bedroom din shi
ya na barin wajen Mohammed ya kali Malik ya ce " Ran ka shi dade ni dai ban yarda da wannan shawarar ba "
ya na gama rufe baki Miram ya ɗaura da cewa " haka ne ya shugaba na , kowa ce shekara mu ka ke bawa ragamar kula da raba kudin nan ta ya rana guda a ce an sauya , kuma a ce mace za ta raba kudin "
kallon Hussein Malik ya yi kafin ya ce " Hussein , General , me za ku ce a kai ? "
" ran ka shi dade ina ga abun da Amir ya Fada dai'dai ne , ko wace shekara tsarin Raba kudin nan duk ɗaya , canjin da Amir ya kawo hakan ba karamin ɗaukaka shi zai yi , specially da ya ce a saki sauran prisoner , ko ba haka ba General " Hussein ya fada ya na kallon General
gyada kan shi General ya yi kafin ya ce " Haka ne yadda ka fada , magana ta rage gare ka ran ka shi dade "
a tare duk su ka kai kallon su kan Malik su na jiran su ji abun da zai ce
dan jinkirtawa Malik ya yi kafin ya ce " a yi yadda Amir ya fada , za ku iya tafiya "
cikin girmamawa su ka mike dukkan su , su na yi wa Malik sai da safe sannan su ka nufi hanyar fita building din baki daya
▪ MIRAM
Tsaye ya ke shi da Mohammed a cikin garden din cike da bacin rai Miram ya ce ma Mohammed " Mohamed , yanzu ya za mu yi , Wacen sakaran Amir ya bata mana shirin mu "
" Miram kontar da hankalin ka " Mohammed ya fada cikin nitsuwa
" ta ya za ka ce na kontar da hankalin na , ni dama na San kallon nan da ya yi min ba na banza ba ne , mun jima mu na jiran wannan damar yanzu ya bata komai "
wata shegiyar dariya Mohammed ya yi ya fara takawa ya yi gaba ya na fadin " kar ka damu , wannan ne na farko kuma na karshe , dan babu wanda zai dawo da ga Makka a cikin su , kai dai ka tsayar da maganar auren ka da RIANNA kafin Malik ya bar kassar nan "
haka dai su ka ci gaba da tafiyar su su na hirar su ta makirci
▪AMIR
Ya na jin su Miram sun fita , ya dawo cikin parlourn
Malik ya na zaune inda ya ke ko motsi bai yi ba
a hankali Amir ya karaso cikin parlourn ya nufi sofar da ya tashi ya koma ya zauna ya na fadin " Ina son mu yi wata Magana "
a hankali Malik ya juyo ya kale shi ya ce " wace magana ? "
" wanene ya nemi auren RIANNA lokacin da ba na nan "
" Miram ne ! amma ta ce ba ta son shi , yanzu dai Akwai Sarki Abdoul Mujeeb ya nema wa yaron shi babba , Aymane auren ta , kuma mahaifiyar ku ta ce ta yarda ka san Abdoul Mujeeb yayan ta ne "
cikin nitsuwa Amir ya katse shi da cewa " na san da wannan dukka , ina son na ga Yaron , MALIKAT INAS da ita RIANNA sun yarda ? "
" yanzu dai ba ya cikin saudiya , ya tafi wani aiki a kassar Turkey , bayan Azumi ya dawo , RIANNA ta ce sai ta gan shi kafin ta yanke shawara , ka san yar uwar ta ka da mugun son maza ma su kyau shi ya sa ta ki yarda da Miram wai ya yi mata tsufa " ya kai karshen ya na yar karamar dariya
" kennan babban yayan Diya ne ? " ya fada cikin zuciyar shi
ya yi nisa cikin duniyar shi ya jiyo Muryar Malik ya na fadin " ya kamata ka je ka yi wa matar ban kwana yadda ya dace "
slowly ya juyo da kan shi ya kali Malik ya daga mishi gera guda ya na fadin " What do you mean ? "
yar karamar dariya Malik ya yi kafin ya ce " ka na nufin ba za ka yi mata ban kwana ba , kar ka manta cikin daren gobe za mu tafi "