← Book details Exiled Prince Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 27

Sashe 5

Exiled Prince Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

After some minutes ya fito daure da towel a kugunshi allamun wanka ya yi
Ya na fitowa ya nufi wata door ita ma dan nesa kadan da ta toilet
Ya na isa wannan karan ma ta bude kan ta

Bai yi five minutes ba ya fito sanye da wasu kayan barcin farare kal ma su mugun kyau kamar yanzu a ka ciro su da ga cikin leda , ya saki wannan lalawsan Darck black smooth hair din na shi ya zubo mishi har saman shoulder , sai tashin fitinannan kamshi ya ke
( kaiiiii , kudi duniya ne gaskia 🤣 amma na halak 🤣🤣🤣 )

Kai tsaye wannan royal bed ya nufa ya Haye ya konta ya lumshe idanun shi ya na karanto adu'ar barci
Ba jimawa barci ya yi gaba da shi

* MISALIN KARFE 2 NA DARE

Ya na tsaka da barcin shi a hankali ya fara jiyo kamar warin kuna
A dubu dari ya ware idanun shi , nan ya ga uban hayakin da ke tashi cikin bedroom din nan take ya fara tari ya na toshe hancin shi idanun shi su ka koma jazir

Kafin ya yi yunkurin tashi duk hayaki ya gawraye dakin ba ka iya ganin komai
Amma a hakan ya mike ya laluba jakar shi , ya rataya ta , sannan ya sauko da ga saman gadon ya na uban tari dan hayakin ya fara yi mishi yawa ya nufi dressing room ya shigo

Kamar wutar jira ta ke ko , ya na shiga kofar shigowa dakin ta ba da wata razananiyar kara kamar ta watsewar glass , ta fadi kassa , finger print din kuma ya watse nan take wuta ta gawraye bedroom din komai sai da ya kone a ciki
( bari dai mu ga da ga wajen kuma )

Duk mutanan masarautar su na tsaye gaban Building din , dan wajen hawa uku gare shi
Duk hawa ukun sun kama da wuta wajen ya koma jazir
Azim da wasu mutanan biyu su na rike da Malik sai kiran sunan AMIR ya ke ya na a bar shi ya ceci ran yaron shi kar ya mutu

MALIKAT AL'UMU ma haka zalika sai da MALIKAT INAS da MALIKAT DJAOUDATT da MALIKAT HOUDA su ka ririke ta
TESNIM da RIANNA kuma sai kuka su ke yi , su na kiran sunan AMIR
Su na a haka RIANNA ta saki wata razananiyar kara da ga haka ta dauke ta fadi a kassa sumamiya

Da karfi MALIKAT INAS ta kira sunan ta , ta saki MALIKAT AL'UMU ta nufi diyar ta , ta na kiran sunan ta

Ganin abun da ke faruwa ya sa Malik Zubewa kassa saman guyiwowin shi ya dafe kan shi da hannu guda ya na fadin " wai me ya ke shirin faruwa ne haka , Azim me ku ke jira har yanzu ba ku kashe wutar nan ba "

Bai gama rufe bakin shi ba duk glass din ginin su ka tarwatse su na bada wani razanannan sauti su ka fado musu kassa da sauri kowa ya juyo bayan shi wasu har guduwa su ke

Dan zaro idanu ta MALIKAT AL'UMU ta yi ta fadi sunan AMIR da karfi har Muryar ta na sarkewa , ta na gama fadar hakan ta dauke lokaci guda ta na neman zubewa da sauri MALIKAT DJAOUDATT da MALIKAT HOUDA su ka taro ta a tare

Da sauri Malik ya mike tsaye ya na fadin " ku kawo min ruwa tun da ku ba za ku iya kashe wutar nan ba , AMIR di na ya na ciki , NAWFEL ka na ji na , kar ka ji tsoro yanzu na zo na fitar da kai " ya kai karshen hawaye na zubo mishi ya nufi ginin da gudu ya na taka glass din da ya zube a wajen duk kafafun shi su ka fashe

Da gudu Azim da wasu dogarai su ka bi bayan shi su ka taro shi Azim na fadin " ku yi hakuri yanzu fireman sun iso , su na kan hanya , kar mu rasa ku duka "

Ina Malik ko jin su ba ya yi sai neman kwatar kan shi ya ke
Lokaci guda ya tsaya ya kai hannu ya dafe saitin zuciyar shi
Da sauri Azim ya shiga kiran sunan Malik ya na tambayar lafia

Kafin ya yi wani yunkuri Malik ya dauke kamar wutar nepa ya fadi kassa cikin wannan uban glass har sai da hannayan shi su ka farfashe su ka fara zubar da jini

Cikin fitar hayaci MALIKAT INAS ta shiga fadin " inallillahi wa ina illaihi raji'un , ya Allah me ya ke shirin faruwa ne haka , Ga MALIKAT AL'UMU , MALIK , RIANNA duk a konce , AMIR din mu kuma na cikin wannan uban wutar , wai me ku ke jira ba ku kira firemen da ambulance ba , jira ku ke sai kowa ya mutu ne "

Ta na gama rufe bakin ta Motoci goma na yan kwana kwana su ka shigo masarautar da mugun gudu su ka nufi building din nan su ka fara kashe wutar

Su Malik kuma A ka dauko wata motar a ka dauke su da ga wajen a ka nufi word room din da ke cikin masarautar dan ba su agajin gagawa

Duk wannan abun da ya faru a kan idon AMIR ya na kallon su dan tun lokacin da ya shiga dressing room ya fito building din ta hanyar sirri , ko shi Malik dan ya na cikin halin ha ula'i ne ya sa ya mance da hanyar , da zai iya shiga building din ba tare da wuta ta taba shi ba

Duk wannan uban kiran da su ke yi mishi ya na jin su , kuma ya kallon su
Lokacin da RIANNA ta fadi sai da ya kira sunan ta a hankali ya mika hannun shi nan take wasu hawaye su ka zubo mishi , cikin zuciyar ya na fara nadamar shawarar da ya yanke amma ba zai iya ja da baya ba

Haka ya ci gaba da kallon su , su na kuka ya na kuka hawaye bibiyu kamar karamin yaro
Har lokacin da ya ga Malik ya Zube kassa sannan ya yi sauri ya toshe bakin shi ya bar wajen da gudu ya fice masarautar ba tare da kowa ya gan shi ba

Sai ga shi a saman wata doguwar hanya babu kowa a saman hanyar , Titi ya na da kyau sosai an raba shi biyu da wasu ciyayi sa ga tsakiya da flowers multicolore kamar rainbow
Ga wasu manyan lamps zagaye da titin su na ba da haske sai ka ce da safe ne
Hanyar doguwar ce babu kwana ko guda. Sai shaguna sa su ke gefe da gefen titin

Haka ya kama hanyar nan da uban gudu , kamar zai tashi sama , ko takalmi babu a kafafun shi , duk taku daya in ya yi sai kassar ta ba da sauti dib dib gashin shi duk ya watsar mishi a jiki

Gudu ya ke kamar babu gobe , kamar wanda a ka biyo a na son kashe shi
Duk gudun nan da ya ke yi ya na rike da wannan jakar ta shi da hannu bibiyu

Ya dauki wajen good ten minutes ya na wannan uban gudun kafin ya fara hango wani plaza
Ya na isowa wajen plaza din nan wajen tsalaka titi ya rage gudun shi ya tsaya ya na meda nunfashi har da rike guyiwowin shi

Sai da ya dai'daita nunfashin shi sannan ya dago
Ya na shirin barin wajen da gudu ya ga wata dankareriar mota baka kirin ta sha gaban shi ta tare mishi hanya

Dum ya ji gaban shi ya fadi , ya kassa motsawa sai bin motar ya ke da ido zuciyar shi na duka uku uku

Ya na a haka ya ga an bude Side din driver an sauko da kafa guda cikin wasu sneakers farare kal kafin a ida sauko da gudar wani kyakyawan saurayi sanye cikin Suit farare kal shekarun shi sun zo daya da na AMIR

Karewa AMIR kallo ya yi da kyau kafin ya ce " AL-AMIR NAWFEL ? what are you doing here in this time , mu je na meda ka masarauta "

Wasu yawu AMIR ya hadiye kafin ya ce mishi " kai ina za ka je ? "

Dan karamin murmushi ya yi kafin ya ce " I'm sorry my Prince , kassar ne zan bari yanzu haka airport zan je "

Ajiyar zuciya AMIR ya sauke kafin ya nufi motar nan ya na fadin " ni ma garin zan bari mu je " ya kai karshen ya na bude kofar Side din me zaman banza ya shiga ya zauna

Da sauri saurayin nan ya shiga Wajen Driver ba tare da ya tada motar ba ya ce " ka yi hakuri ran ka shi dade , amma ba za ka iya bi na ba "

Wani mugun kallo AMIR ya wurga mishi sai da saurayin nan ya sha jinin jikin shi
" let's go , ba tambayar ka na ke ba umarni ne " AMIR ya fada cike da izza

Wasu yawu Saurayin nan ya hadiye kafin ya tada motar shi ya kama hanyar airport da gudu

Sai da su ka yi tafiya mai dan nisa kafin AMIR ya juyo ya kali saurayin nan
Dum ya ji gaban shi ya fadi lokacin da idanun shi su ka yi mishi arba da wani zanen sword guda biyu Da wani Lion a tsakiyar su ya bude baki hakoran nan na shi sun fito , a wuyan saurayin nan

Cikin nitsuwa ya ce mishi " What is your name ? " ya tambaye shi

Dan karamin murmushi saurayin nan ya yi kafin ya ce " ran ka shi dade suna na DIYA BIN ABDOUL MUJEEB ........ "

Katse shi AMIR ya yi da fadin " Da ga Daular Ottoman ! "
Hannu Diya ya kai ya shafi zanen da ke wuyan shi kafin ya saki wani cool murmushi ya ce " Eh , da ga Daular Ottoman , ni ne yarima na uku ga SARKI AHMED BIN ABDOUL MUJEEB "
Chapter 5 · 0% Book details