← Book details Exiled Prince Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 27

Sashe 24

Exiled Prince Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta na fitowa kai tsaye ta nufi daddumar ta , ta fara gabatar da sallar ta
ko da ta Kamala ba ta tashi ba , sai da ta tsaya karatun kur'ani har lokacin sallar isha ya zagayo ta tashi ta gabatar da ita

bayan ta Kamala ta tashi ta fito dakin
ko da shigo corridor ta tardo RIANNA zaune saman carpet ta kontar da kan ta saman Cinyar MALIKAT INAS da ke zaune saman Sofa ta jingina bayan ta a jikin sofar ta daga kai ta kurewa waje guda ido
ga busashun hawaye nan konce saman face din su baki daya

karasowa wajen Inaya ta yi ta na fadin " Aunty RIANNA me ya faru da ke haka ? " ta fada dai'dai lokacin da ta ke zama gaban ta saman carpet ita ma

a hankali RIANNA ta dago kan ta , ta riko hannun Inaya ta ce " Baby tashi ki je wajen mijin ki , zai bukaci kulawar ki a wannan lokacin , ki tsaya ki kula da shi yadda ya dace , na san yanzu ya na cikin damuwa , ganin ki zai sa ya rage radadin da ya ke ji kin ji ko ? "

gyada mata kai Inaya ta yi ta na fadin " shikenan Aunty RIANNA , amma ba ki fada min abun da ke damun ki ba , ga hawaye nan konce saman fuskar ki , Ammie ku ma ga hawaye nan saman Fuskar ku " ta fada ta na dawo da kallon ta kan MALIKAT INAS

sai a lokacin MALIKAT INAS ta dawo cikin hayacin ta , a hankali ta juyo ta kali Inaya cikin disashashiyar Muryar ta , ta ce " ba komai baby , tashi ki je wajen Mijin ki , ya fi bukatar ki fiye da mu "

da to Inaya ta amsa musu sannan ta tashi ta nufi kofar fita parlourn zuciyar duk ba dadi ganin yanayin da su RIANNA ke ciki

a haka ta fito part din ta nufi Building din Amir , duk da so guda ta taba tafiya , amma ta san hanya ta kuma san yadda za ta yi ta shiga

abun mamaki kuma ta na zuwa guards din da ke tsarin wajen ko tare ta ba su yi ba
a haka ta shiga building din , kai tsaye ta shiga lift ta nufi floor na uku zuciyar ta na duka uku uku

bakin ta dauke da sallama ta shigo parlourn
nan ta tardo Rouksar , Aysher da Hafsat duk tsaye cikin parlour , Azim ya tare musu hanyar shiga corridor

A hankali Inaya ta karaso wajen ta tsaya ta na bin su da kallo ta na so ta tambayi abun da ke faruwa amma sam ba su ba ta fuska ba
asali ma kowa ce sai kallon wulakanci ke yi wa Inaya

kallon Azim ta yi ta ce " Uncle , yaya Zayd ya na nan ? "
dan karamin murmushi Azim ya yi kafin ya gyada mata kai ya ba ta hanya Sannan ya fada mata a wane bedroom za ta same shi
a hankali ta daga kafa ta wuce ta na tafiya kamar wadda a ka zarewa lakar jiki

Aysher na ganin Inaya ta wuce ta sa hannayan ta dukka biyu ta ture Azim gefe ta na fadin " fin mu ta yi da za ka ba ta hanya ta wuce , ba abun da zai hana ni ganin Amir " ta fada ta na wucewa
da sauri Rouksar da Hafsat su ka bi bayan ta har su ka kamo Inaya su ka wuce ta , su ka nufi Bedroom din Amir

babu ko Sallama su ka fado mishi a tare

Amir kuwa ya na konce bakin gadon shi , ya sauko da kafafun shi kassa
da sauri Rouksar ta karaso tsakiyar dakin ta marairaice murya ta ce " Akhie ! "

slowly ya bude idanun shi ya mike zaune ya dan lumshe idanun shi kadan kamar mai maye , ga gashin nan na shi ya zubo mishi har saman kirji , dukkan su sai da su ka hadiye yawu ba karamin kyau ya yi musu ba

har Rouksar ta bude baki za ta yi magana ya daga mata hannu allamun ta yi shiru
ba musu ko ta yi shiru ta tsaya ta na kallon shi , ta na kara yabawa kyawo irin na Amir , ni ta ke kamar ta hadiye shi

a hankali ya yi kassa da hannun shi dai'dai lokacin da Inaya ta shigo cikin dakin ta na sallama da wannan siririyar murya ta ta

ya na jin muryar ta ya ji wani mugun sanyi lokaci guda , har sai da ya dan lumshe idanun shi ya sake bude su a hankali kafin ya juya ya kale ta , ta na ganin ya kale ta , ta sakin mishi wani cool murmushi cike da shauƙi

ya na juyawa ko Azim shi ma ya shigo cikin dakin da sauri , ya na yin karo da idanun ya sha jinin jikin shi

tun kafin ya yi magana Amir ya riga shi cewa " Me na fada maka ? " ya fada cikin wata murya cen kassan makoshi kamar an busa sarewa dan dadi ,
har sai da Rouksar ta dan lumshe idanun ta a hankali cikin zuciyar ta ta na fadin " Masha Allah , ya Allah na roke ka , ka sa ya zama nawa " ta kai karshen ta na bude idanun ta

jikin Azim har kerma ya fara yi , ya na fadin " ina neman Afuwa ran ka shi dade wlh sun matsa ne sai s...."

cikin nitsuwa Amir ya katse shi da cewa " ku fita ku ban waje ba na son ganin kowa " ya kai karshen ya na sunkuyar da kan shi

Inaya na jin abun da ya fada ta dan sunkuyar da kai ta juya za ta fice
kamar da ga sama ta jiyo Muryar shi ya na fadin " Cutie ban da ke " ya fada da hausa dan ya san ita kadai ke jin hausa

wani cool murmushi ta saki kafin ta juyo ta tako a hankali ta karaso geffen Rouksar ta tsaya ta na kallon shi

ta na tsayawa Azim ya ce ma su Hafsat su fita , ba musu su ka juya su ka fice kowace ta na cika ta na batsewa
riko hannun Inaya Rouksar ta yi , ta na fadin " wuce mu tafi ke kuma ya ce ba ya son ganin kowa "

ba ta kai ga rufe bakin ta ba ta jiyo Muryar shi ya na fadin " sake hannun ta ki fice min da ga nan "

dan zaro idanu Rouksar ta yi ta na sakin baki har da cewa " Amir kai fa ka ce ba ka son ganin k....."

a dubu dari ya dago kai ya daka mata wata gigitaciyar tsawa ya na fadin " I say get out , Azim duk wanda ya sake shigowa ko da parlour ne sai na ɗaure ka da kai na "
nan take idanun shi su ka koma jazir , duk jiyojin jikin shi sai da su ka fito baro baro

ba shiri Rouksar ta saki hannun Inaya ta juya da gudu ta bar Bedroom din Azim na biye da bayan ta da gudu dan shi kan shi ya ji tsoron irin wannan tsawar da Amir

Rouksar kuma ta na baro wajen kai tsaye lift ta nufa ta shiga
kofar lift din na rufewa ta bace bat a cikin lift din

Amir kuwa ya na ganin sun bar wajen , ya kai hannu wajen bedside drawer ya dauki wata remote ya danna wasu button sannan ya ajiye ta
ya na ajiye ta , kofar dakin ta koma da kan ta ta rufe kan ta , ta saka security

sai da ya kofar ta rufe sannan ya juyo ya kali Inaya da ta yi sumar tsaye tun lokacin da ya yi tsawar nan

daga mata gera guda ya yi allamun minene ?
a hankali ta gyada mishi kai allamun ba komai ba tare da ta ce komai ba

ya na ganin hakan ya dan sunkuyar da kan shi ya dafe shi da hannu guda ya lumshe idanun shi

dan lumshe idanun ta ita ma ta yi a hankali ta sauke ajiyar zuciya sannan ta bude su
a hankali ta fara takawa , ta karaso bakin gadon ta cire flat shoes din ta ta haye gadon
ta koma bayan shi ta yi kneel down , sannan ta kai hannayan ta a hankali bayan wuyan shi ta fara yi mishi Taussa dan a tunanin gajiya ce kawai ya ke fama da ita

kamar ko ta san ya na da bukatar hakan , a hankali ya fara dago da kan shi ya gyara zaman shi , ta na ci gaba da yi mishi taussar har wata ajiyar zuciya ya sauke

ta na jin ya sauke ajiyar zuciya ta saki wani dan karamin murmushi mai sauti sannan ta zagayo da hannayan ta , ta rungume shi ta baya ta kontar da kan ta saman shoulder din shi cikin shagwaba ta na fadin " baby na yi kewar ka sosai fa , shi ne ka dawo ko nema ta ba ka yi ba , ba ka yi kewa ta ba kenan "

a hankali ya sa hannayan shi ya cire nata ya juyo ya kale ta ya ce " na yi miki kama da baby ? "

turo dan bakin nan nata ta yi ta sunkuyar da kai ta riko gudan hannun Abayar ta , cike da shagwaba ta ce " ni fa ba wancen babyn ba na ke nufi , dama Aunty RIANNA ce ta ce na daina kiran ka da yaya Zayd , wai na dinga kiran ka da Baby ko sweetheart , shi ne kawai na yi " ta kai karshen ta na gyara zaman ta saman gadon ta kauda kai gefe
Chapter 24 · 0% Book details