← Book details Doctor Eesha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 56

Sashe 7

Doctor Eesha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tycoon ya kalleshi ya murmusa yace" thanks son" yaciga da cewa" tundama nakira Kane na tuna ma maganar aure ka, Kuma na shaida ma cewa next week zaka fara zuwa office, ka ga kenan sai ni na huta da zirgazirga, Kai ka cigaba, I surely know my boy can do it, kaga kenan zaka zama junior tycoon, ya murmusa, yacigaba , toh nabaka hutu one week kenan, Hafiz tun last week ya fara zuwa office zai nunama komai so don't worry"

Aliyu bai amsa kanshi a kasa Yana ta ma kafa daddy tausa.

Tycoon yace" son baka jinane?

Yace" dad naji ama please maganar aure da Allah a dafashi please ? Ya marairace fuska,

Tycoon yace" ama Aliyu maiyasa kakeso a daga?

Yace" haka kawai dad"

Tycoon yace" toh kayi hakuri son gaskiya bazaniya sa a daga biki ka ba, just have patients komai zaiyi dadai inshallah kajiko?

Yace" toh dad nagode sai da safe"

Tycoon ya amsa da Allah yabamu alkhari sa"

Ya Mike jiki a sanyaye zuwa dakishi, jalabiya kawai yacire ya kwanta.

KADUNA

Su Essha sai wurare 3:30pm su ka Isa kaduna duk sugaji, anguwar dosa straight baba driver ya wuce dasu, a kofar gate dinsu big mom, baba driver yayi horn gate man yabude musu, ciki gida makil da Yan biki , tun daga yanuwa miji big mom da nata, da abokaina arziki.

Baba driver ya Parker motar duk suka fitoh, hanan ta hangi Essha da gudu taje ta rugumeta, tace" Oyoyo sis Essha"

Essha tace" ohh baby hanan yaushe kukazo?

Hanan tace" shekaran jiya, Ina khairat da su Yaya amir? Ta tambaya

Essha tace" suna gida suce a gaisheku " taja mata hanci.

Tace" toh maiyasa basu zo ba?

Essha tace" baby hanan makarata ne ya sayardasu"

Su daddy karami suka wuce masalaci dake kofar gida domin suyi sallah la'asar.

Essha Kuma na kwashe Kaya dake boat, hanan na Taya ta. Taji a rufe mata Ido ta rasa wayane .

Tace" baby hanan da Allah waye rufemin idon " batasaniba hanan tun lokaci da tafitar da trolley nasu ita da hajiya suka wuce ciki.

Ta Kara tambaya ta marairace murya tace" da Allah waye? Akaki magana, tayi tayi ta bude ta gagara a rike Ido tam, sai can taji a koyi murya ta da Allah waye?

Tayi murmushi tace " Aina'u bude min idona, ai tundama nasa kece" ta cire hannuta da sauri tana dariya tace" Oyoyo sis"

Essha tace" bazan amsa ba, baya ki tsoratar Dani"

Aina'u tace" yi hakuri zomuje ciki, kiga hajiya ta Dade da wucewa Wai bazata tsaya kallo shirmemu ba, Wai kafafuwata suyi tsami" dukasu suka fashe da dariya.

Gefe guda ta hangi su Yaya Usman, Yaya Abba , Yaya salis , sai hira suke akar Kashi bishiya mangoro dake ciki gida.

Aina'u tace" ni bazan Kai Kaya ciki, kije ku gaisa ko?

Tace" toh sis ngd" ta nufisu, dayake Bata guri suke kallo ba shiyasa Basu gantaba, ta cigaba ta nufisu ciki tafiya ta Mai dauke hankali Mai kallo, tana zuwa daf dasu

Tace" hi yan samari" duka sukayi sauri juyawa don suga mallaki murya, kawai sai sukaga Essha, kawai dukasu suka sake mata murmushi, Usman ne kawai ya hada fuska.

Salis yace" sis sauka yaushe mutani lafiya ne(ya koyi hausa lafia😆)

Ta harareshi sanan ta amsa da" yanzu na tare dasu hajiya da daddy karami muke"

"Eya sannu da zuwa Yar kauye " cewar Yaya Abba

Tace" ni ka daina cemin Yar kauye"

Sameer yace" ke Yar

kauye ne mana, da wani hausar ku tsamama Wai ku Kuna hausa😆( mutani lafia kumun afuwa😅🙏)

Tace" Allah Sameer ka kiyayeni" ta juya ga kallota zuwa bangare Usman ya wani hada fuska kamar baitaba murmushi ba, hkl shi na waya.

Tace "babba yaya Ina gaisuwa" bai amsa ba ya Mike kamar zai wuce ta, ya dawo ya tsaya daidai inda take ya kama mata kunne.

Tace" wassh ni Mai na maka?

Yace" laifi ki da yawa, na daya bakison san da zumuta, Kuma sau nawa zagaya maki, ki daina sa iri Wana gyale ki ki ji, Kuma daddy Yana kalloki"

Tace" ni ka kyalleni" Tana tura baki.

Salis ya Mike ya kwace ta daga hannushi,

Yace" bros kyaleta yi hakuri, ka ga tayi tafiya Mai nisa ko, ta gaji"

Usman yace" ai Allah yasoki"

Tace" eh din" ta mishi gwalo , da gudu ta wuce ciki. Tana shiga ta Sami big mom zaune a parlor tana waya, da gudu ta fado jikita,

Big mom tace" eh zankiraki anjima, ta kalli Essha tace" Wai Wai daughter so kike ki karya ni, wow daughter na ta Kara kyau da girma, ki gaki kuwa"

Tace" Kai big mom" ta rufe fuska. Yan parlor sai dariya suke musu.

Tace" big mom Ina hunaisat?

Big mom ta amsa da tana dakita"

" Ok mom" da gudu ta wuce daki hunaisat, big mom tace" daughter kiyi a hankali fa?

Ta amsa da " toh big mom"

Ta shiga,ta Tara da humai zaune a tsakiya gado, ta Sha lalle a kafa da hannu sai walkiya kawai take na amare, sai waensu yanmata su uku, agefe ta, suna kallo Abu a waya, a zuciya ta tace Killa ma hotuna biki suke kallo.

Tayi sallama suka amsa, hunaisat ta daga Kai taga Mai sallama taga Essha ne, tayi Kara, ai da gudu ta rugumeta, sai murna takeyi.

Essha tace" Kai amarya na Zaki karya ni"

Hunaisat tayi murmushi tace" sis kigaki kuwa, ki hadu fa"

Tace" ni wa , ai duk haduwa da nayi ai ban Kai ki ba amarya"

Hunaisat tace" sis Allah wlh dagaske nake"

Tace" toh nagode amarsu"

Hunaisat ta juya ga friends dinta tace" Maryam, asma' u, dija Meet my special cute sis, itace Essha Dana ke baku labarita"

Maryam tace" ai Naga Alama , sannu da zuwa"

Essha Tamika musu hannu sukayi musabaha,da fara'a a fuskata tace" nagode"

Dija tace" Kai walahi ki hadu da inada Yaya namiji Dana mishi hanya"

Essha tayi murmushi tace" Kai bar fasamin Kai"

Asmau race" Allah da gaske ne"

Tace" nagode tom sosai, sis bara nayi sallah ko"

Ok " ta wuce toilet tayi alwala, ta fito ta gabatar da sallah la'asar, Tana idarwa suka Soma hira.

Tace " sis Naga hotuna bridal shower din?

Hunaisat tace" a'a ni bazan nuna miki ba"

Tace" haba mana amarya Anas"

Hunaisat tace" har kisan naji sanyi gashi ki ganni"

Tana kallo hotuna tace" gaskiya sis ku fito, I really miss" taga hotuna har Dana KAMU tace" sis Wai yaushe akayi wanan?

Hunaisat tace" yau man"

Tace" eya sis maiyasa bakusa 4:00pm a tashi seven ba?

Hunaisat tace" a'a ba ruwana, Yaya Usman ne ya Sara komai"

Essha ta hada fuska kamar zatayi kuka tace" shi Kuma Yaya Usman Nashi kenan ra'ayi tsiya kamar shine ango, ace nazo biki sis, events ko daya bani aciki"

Maryam tace" Essha karkidamu ai ba'ariga a daura ba, Kuma ai gobe akwai walima sai reception bayan daura aure"

Tace" Kai har naji sanyi"

Yan daki sai tsokanar hunaisat suketayi Wai tacika surutu da rawar kai kamar ba amarya ba"

Essha tace " Kar kudamu gobe ne Ido zai Raina fata " duk suka fashe da dariya

Hunaisat tace " eh din ku kyalleni"

Hafsat ta shigo tace" sis Essha big mom nakiraki, Wai kizo kici abinci"

Tace" toh hafsy muje"

Ta Mike tabi bayata, ta samu big mom tana shirya abinci akan dining, Yan taro sai safa da marwa sukeyi.

Essha ta lagwabar da Kai tace" big mom ni gsky baza iya ci abinci anan ba zan Kai daki"

Big mom tace" toh badamuwa , zo ki Kai ma hajiya da daddy ku nasu"

Ta kwashe nasu hajiya takaimusu, taxo ta dauki nata sai daki, tana zuwa ta jima wayata na ta ringing ta dauja, taga bestie ne.

Tace" hello"

" Hi har ku sauka"cewar bestie"

Essha tace" eh dear tun misali 3:30"

Bestie tace" tom ya hanya?

Tace " hanya lafiya lau, ya lecture din?

Bestie tace" ai kibari kawai Essha lecturer dina yaso yasamana zafi, daga zuwa aji fa, Wai tests, ai student nata complain shi ne ya hakura Wai gobe Saturday mun dawo 4:00pm"

Essha tace" toh bestie iya complain Allah yabaki sa'a"

Bestie tace" ameen bestie mie, ni gsky nayi missing naki, ki dawo Sunday kijiko"

Essha tace" Nima hk, Kar kidamu, Sunday zamu dawo inshallah, ga amarya ku gaisa" ta Mika ma hunaisat waya suka gaisa sanan ta mata bye ta kashe waya. Ta Kira mum da dad dinta suka gaisa, sanan ta Kira Khalid su Dade suna waya kamar baza su rabu ba, shima ta ba hunaisat waya suka gaisa, suna Gama gaisawa ta kashe, ta Soma ci abinci, sanda aka fara Kira sallah mahgrib sanan ta handa plates takai kitchen.

Su maryam suka musu sallama zasu wuce sai gobe da safe zasu dawo , har baki gate suka rakasu, sanan suka juyo ciki , sai kiraye kiraye sallah kakeji, suna dawo suka Dora alwala , sukayi sallah magarib, suna idarwa suka fara tilawa alqur'ani maigirma har akayi Isha, suna idar da sallah Isha.

Essha ta shiga ta watsa ruwa, ta fito daure da da towel Dakar ya wuce cinyar ta.

Hunaisat tace" sis kigaki kuwa, kigama haduwa tuburkallah dama ni ne"

Tace" Kai hunaisat basan shairri "

Hunaisat tace" Allah ba sharri bane , dubeki fa kamar Nicky Minaj " tayi dariya

Essha taja pillow dake baki gado ta harbe ta dashi tace" ke yariyana Allah yashiryamin ke"

Hunaisat ta cabke pillow tana dariya tace" ameen"

Tana rufe baki sukaji sallamar , big mom, anty zainab da Aina'u, dukasu rike da Kaya a hannusu, big mom kula ne a hannuta, guda biyu , ita Kuma anty zainab robar ne kamar na talla, cike yake dam da turare wuta, daya Kuma da lalle na Hadi na wanka amare, Aina'u Kuma gora ne maidaidaici a hannuta sai leda fari baiya gani abunda keci.

Big mom ta a aje kulla a gaban hunaisat, ta amshi roba da ke hannu anty zainab shima ta aje a gabanta , har da Kaya hannu Aina'u duk ta hada ta aje.

Big mom tace" hunaisat? Ta amsa da na'am momy"
Chapter 7 · 0% Book details