← Book details Doctor Eesha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 56

Sashe 38

Doctor Eesha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kiraye kiraye sallah assalatu ne ya ta data, ta Mike da addu'a tashi a bacci dauke a bakita, ta bude kwaya idonta data rufe da rufe da mask na Ido ta ta sauko a hankali ta fice ta tada Amir da Sadik ta koma daki tashiga toilet tayo alwala ta fito ta shimfidar daddumar , tana shimfida wa aka fara sallah, tasa hijab har kasa tayi sallah ta a sukuni, baya ta idar ta zauna tayi ta Azkar sai kusan 5:45 ta Mike da sauri ta Manta ma flight din safe zasu bin, da saurita ta Kara hada kayayaki su day Amir baigama hadawa ba, tana kan hadawa Amir da Sadik suka shigo, Pooja na biye rike da tray ta shako kayan breakfast a ciki , Essha ta karba Tamata godiya ta Mika su Amir, Sadik yasa hannu zai tashi Arudh, Essha ta hanashi tace" barta tayi bacci ta"

5:53 harsugama shiryawa tsaf,Pooja ji take kamar tayi kuka, tasan ma nata kadane dun bataga su ba karamin lalashi zatayi ba.

Ta kwashesu a motar zuwa Airports suna isa 6:00am na cika, da zuwa su ba'afi mintina b aka fara Kira jirgi zai daga, Pooja ta rugume Essha dukasu kuka suke na rabuwa da juna, Sadik ma kuka yake zai bar Aunt Pooja, Amir ya dagashi ya rugume suka shiga jirgi, Essha na biye dasu tana daga ma pooja hannu tana hawaye, Allah sarki ayi sabo azo a rabu ba dadi.

Essha na shiga ta duba seat number ta, ta zauna su Sadik na gabata ta Mike ta shafa Mai Kai , gyagadi yakeyi dun Sadik baida wuya bacci, Amir yagyara Mai kwanciya ya Dora Mai sit belts, video game karamin dake hannushi, ya karba ya ije Mai a gefeshi, Essha ta zauna itama Tana gyara belt nata, gabata faduwa yakeyi, ta lumshe Ido kamar Mai bacci tana ji jirgi ya daga ta saki ajiya zuciya tana roko Allah ya saukesu lafiya.

*Few hours later*

Nigeria gida, da komai lalacewarta Muna Alfahari da ita.

Nnamdi Azikwe international Airport Abuja.

Ciki ikon Allah jirgi su Essha ya landing lafiya, Essha naji su land ta sauke ajiya zuciya tace" Alhamdullila" ta kalli su Amir da bacci suke Hankali kwance ta Mike ta tada Amir, sanna ta samo tapping Sadik a hankali tace" Sadik wake up , open ur eyes, you in Nigeria welcome home" ta fada Tana murmushi

Sadik daji haka da sauri ya bude ido ya juya ya kalli kofa yaga har anfara sauka ya mike, sit belt ya dawodashi, yasa hannu ya cire belts din ya Mike zai yi hanya fita, Amir ya rikoshi Yana dariya da turanci yace" easy boy, Allah Allah kake kaga kasarna ko? To gode ma Allah first"

Sadik yayi murmushi yace" Alhamdullila"

Essha gani kallo da waensu daga ciki passengers din ke bin Sadik dashi ne yasa ta tsargu da sauri ta dauki hanbag nata ta ciro face masks baki tasa ma Sadik Wanda kwaya idoshi da tunda hanci kawai ake iya gani

Amir yabata fuska yace" sis yaza ki rufe Mai fuska Kuma?

Tace" Amir sauko kawai muje nasan su mummy nanan suna jiramu Kar mu Bata musu lokaci"

Amir bai tanka ba ya rike hannu Sadik sukayi gaba, tana biye dasu, suna sauka, Essha tayi hanya guri kwashe musu Kaya da har ta hangi su mummyko, Sadik ya saki Hannu Amir, yana ihu murna Yana zangeya Airports din Yana" ye am in Nigeria, am so happy" Yana kan ihu da tsale ne yaji ya buge mutum, video game dake hannushi ya fadi, yadaga Kai yaga waya ya buge, yaga mutumi har ya tsuguna ya dauki video game din ya rike a hannu yadaga Kai Yana ma Sadik murmushi, La Isa ne kanni Aliyu ga uban escort Dina na fama a bayashi..

Sadik ya tsaya kalloshi shiru ..

Isa yayi murmushi yace" little boy ka buge ni ka kasa bani hakuri ko? To banza baka video game naka ba har sai ka ce min sorry"

Sadik baigane maiyake nufi ba shi fuskarshi ma kawai yake kallo Yana shafa nashi fuskar, abun mamaki yake bashi yaga Mai kama dashi(lol yaro dama baka ga Daddy ka ba kenan)

Isa yakara maimatawa yace" tell me sorry"

Sadik naji haka yayi murmushi yace" sorry uncle"

Isa yayi murmushi yace" boy gayamin sunaka, maiyasa ka rufe fuska bakaji zufa ne?

Sadik da bagane hausa yakeyi ba sai bin bakishi kawai yake da kallo, can yaji Uncle Amir na kwala Mai Kira ya juya da gudu tabar guri"

Isa Yana" tsaya ka karbi game na ka"

Sadik bai tsayaba bai ma fahimce abunda yake fada ba,juyawa kawai yayi yadaga Mai hannu..

Isa yayi murmushi Yana kallo video game din, ya Mika ma daya daga ciki security dake bayashi yace" bin bayashi Kai kaimishi"

Ya amsa da "okay sir"

Sadik kafi yaisa guri dasu mummyshi sukai sukayi kicibus da uncle Amir,

Amir yace" Boy bakaji ko?zaka daga ma mummy ka hankali Ina ka shigane?

Sadik yarike hannushi yace" let's go uncle" kamar bashi Amir ke ma fada ba.

Amir ya dafa goshi yace" ohhh gosh sai shirmana nake bai ma ji abunda na fada ba, ke kam Sis Zaki banu da Daddy, Boy ko zo na kashe ka da hausa baisaniba"

Sadik yajijiga mishi hannu yace" uncle what are you saying?

"Ohhni Amir, I said let's go" ya rike hannu suka Kama hanya, tunkafi su isa Amir ya hango su khairat Walid harsu hunaisat da Aina'u, motar biyu suka zo dashi.

Walid da mufeedat dagudu suka zo suka daga Sadik, Essha na tsaya a gefesu tana murmushi tace" what!! Tuntuni Ina tsaye babu Wanda yamin Oyoyo, wato boy naku kadai kuka gani ko"

Walid dake rugume da Sadik yayi murmushi yace" Eh ni shi nazo tarba my one and only son"

Essha tace" oho dai Nima ganawa mummy zanje na rugumeta" ta fada tanufi guri mummydake tsaye sai fama zuba murmushi take da gudu ta rugumeta tace" Oyoyo mummy na I really miss you"

Ta kalli gefeta tagasu hunaisat tace" lah Sis hardaku, a lallai kuyi kokari" ta zunguri Aina'u tace" Mrs Usman mijiki Mai ra'ayi tsiya na haryabaki kika fito da wanan tsoho ciki Kai lallai ni Yar gatace"

Aina'u tayi dariya tace" ai Yana ciki Yana ji ki" ta fada Tana nunanu ciki motar..

"Ohh ni Yaya Usman bai canza ba shine ko ya fito"

Hunaisat tace" kaima ai ba canzawa kikayi ba surutu da shagwaba nanan"

Essha tayi dariya ta Kama baki tace"nayi shiru, ina tsohuwa Mai ran karfe?

Usman yafito daga ciki motar Yana murmushi yace" tana na ta shirya Miki liyafa sai Wanda ki ka zaba , ni fa Boy Dina nazo tarba bake ba, ina yake?

Essha ta tura baki a shagwabe tace" kowa boy boy yanzu shikena a cikiku ba Wanda yazo tarba na guri boy naku ku ka zo, ni Ina Daddy na? Nasan shi zai kulani ai"

Duk suka sa dariya, mufeedat tace" Daddy yayi tafiya sai gobe zai dawo yace mubaki hakuri, Daddy karami kuwa baiji dadi jikisane shiyasa bai zo ba"

"Allah sarki" Essha ta fada zatayi sake magana mummy ta dakatar da ita " yarana hiraku ba Mai karewa bane, ku zo mukarasa gida ko cigaba, ina shi Wana raino jajaye kunnuwan yazo mutafi"

Khairat tace" Kai mummy miji naki ne raino jajaye kunnuwan toh anfasa aure da ke da anty zainab ko big mum za'ayi"

"Oho dai Nima bance inaso ba" mummy ta fada cike da barkwaci duk suka fashhe da dariya...

Duk suka shiga motar, ciki motar su mummy kowa na zumidi taba Sadik, kowa naso shine ace ya zauna kusa dashi, Amir ya raba fada ya Dora Sadik a cinyar shi, zasu tada motar kenan aka fara musu knocking, mummy ta zuge glass din kasa taga baki mutum maiji da Karfi yasha black coat da eyeglass baki mummy tace" yadai lafiya dai ko?

Yace" yihakuri Ma, yallabai ne yaban wanan naba wani yaro danaga yashiga motar na, nashi ne" ya Mika mata video game din, mummy ta amsa Tana juya a hannuta tace" Aya nane ba Bata hanya kayi ba?

"Yes nane, yaro na sanye da facemask baki Dana bi bayashi motar na yashiga"

Tace" oho " ta juya ga Sadik dake back sit tace" kai renon masu jajaye kunnuwan nakane, ka wani sa facemask na rigima da basan dalili sawaba"

Sadik da baji yaren ta yakeyi bA hannu kawai yasa ya karba, tace" iyye ina ma magana baka ba amsaba shine kawai zakasa hannu ka karba, kaji min yaro"

Sadik kanshi na kasa Yana kokari kunna video game din baimasan tanayi ba"

Ta juya ga security tace" mungode a ma wani yallabai kenan?

Happy Juma'at Kareem 💓 💓💓💓 💓💓💓

Comment and Share 🥰

Love you guys 😘😘

👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
DOCTOR ESSHA
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️

*WRITING BY*
*J Hajara*

🌍 *MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M.W.A*

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta.🤙🏻
_________________________

6️⃣4️⃣&6️⃣5️⃣

Security yace" oga nane" ya Bata amsa ya juya yayi wucerwasa..

"Oga nane? Mummy ta maimatar amsa da yabata..

"Shi oga nashi baida suna ne, a'ina Sadik yasashi daga zuwa shi" ta juya ga Sadik" Kai Raino jajaye kunnuwan ai'na kasashi daya baka wanan?

Sadik hankali kwance game nashi kawai yake bugawa, Amir najita yayi tsit, dayasa inyagayamata Sadik wani dramer za a kwashe, gwara yayi shiru insu je gida tasani..

Walid dake gefesu yace" Boy, Granny na magana dakai ka mata shiru" ya fada Yana shafa Mai Kai.

Sadik ji ankira Boy, granny yasa yadago Kai ya kalli mummy.

Mummy tace" ugo na nabaka, ko uwarka ina magana Bata share ni balle Kai tasisi dakai"

Sadik yanayi yanda take Magana ne yabashi dariya harda kyakatawa shi, duk suka zuba mishi Ido.
Khairat tace" Walid cire Mai abun fuskar na yasha iska"

Walid kamar jira yake yasa hannu ya cire Mai face mask din, daga mummy harsu duk suka bude baki suna kalloshi, yanda yake dariya gwani sha'awa..

Mufeedat ta Kai Hannu daidai dimple nashi tana murmushi tace" wow I have a cute boy, Kai wlh saina kaishi school dimu, na nunama Yan ajimu, yaro sister na Mai kyau ne"
Chapter 38 · 0% Book details