← Book details Doctor Eesha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 56

Sashe 20

Doctor Eesha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mummy tsoro nakeji inaji fargaba mummy, su aurar da ni, they have ruined my life" ta Kara sauti kukata, daddy ya matso kusa da su ya shafa kanta, a firgice ta juya tana gani shine ta rugumeshi " Daddy zuciya, daddy kasana, zan mutu daddy, ka raba aura na wlh banso, shikena an aura dani daddy na bazai kaini makarataba balle na cika burina har yakai ga kirana DOCTOR ESSHA, nasan daga Rana ita yau zan daina sa .... Ta dakata, jiki ta har rawa yake saboda tsumayi kuka" daddy why me? Why? Why?

Daddy haweye fuskata yashiga gogewa shima dauriya kawai yayi, Yana rike haweye bai barsu su sauka ba ya daure yayi murmushi Yana girgiza Kai yace" ya'isa haka Essha daddy, ki daina ai'bata aureki Kar ki mantafa aure sunnah ne na Ma'aiki (S.A.W), aure rahma ne Kuma alkharine, magana karatu inshallah ba abun da zai hanaki bearing suna DOCTOR ESSHA" yaja mata kumatu yayi murmushi " ba abunda zai saimeki inshallah, ni da mummy ki dasu hajiya muna tare da ke"
Daki ya dauki shiru, bakaji komai sai shesheka kuka Essha da hajiya, Essha na kuka zafi da ke damunta, hajiya Kuma tausayi hali da Essha ke ciki shiyasa ta kuka, Essha sai zabura take ita daya, haryanzu da alama tsoro a atare da ita, daddy nata aiki lallashi, can ya Mike yace" Essha zanje sallah ankira zuhur"

" Ni ma zanyi sallah daddy" ta fada Tana share hawaye , tun jiya banyi sallah ba"

" Toh mummy ki da antyki zasu tamaika miki" ya fice da sauri baison ya rasa jam'i.
Nurse din ta kalli mummy tace" hajiya bara na taimaka mata dun ba'ason tayi kwakara motsi saboda dinki dake jikita"

Essha ta makale kafada ta tura baki tace" uhm uhm mummy nane zata taimakamin"

Nurse tayi murmushi ta shafa kanta tace" okay beauty badamuwa Bari na baku waje" ta fice..

Mummy ta Mike ta dauki flask din da hajiya suka kawo da safe, tafasheshe ruwa ne dam , tashiga toilet ta juye a baho wanka, da taimako anty zainab ta kaita toilet, ta zuba gishiri kadan ta Kara surka ruwa, sanda suka Kai ruwa Rana Essha ta Amince ta shiga ruwa zafi, ihuta yagama cika asibiti, kuka tasaki da Karfi tana Kira hajiya da daddy ta su zo su taimaketa, Wai balle Essha iyaye raki.. sanda mummy ta tabbatar ta gasu sosai sanan ta cire ta tasata tayi wanka janaba ta Dora alwala tafito, tan Dan ji dama dama, Dakar take takawa mummy na rike da ita, har su ka Kai baki gado, haweye kawai take sharewa ta hura baki, ita kadai tasan yanda takeji a zuciya ta, sai tsine Aliyu takeyi, yasha Allah yaisa ba adadi.

Mummy ta shimfidar mata daddurma tabata riga da skirt na atamfa tasa da hijab , a zaune duk ta Rama sallolita tana hawaye..

ABUJA
************************
Gari na wayewa ummi tasa su a gaba sai fada take musu" tun jiya nagaya muku cewa su shafi Aliyu ama kuka ki yarda da batuna, gashi har su na nema sumishi illa, Allah sarki bawa , Yana ban tausayi , ke Kuma aljana Essha, Allah yama jikana kataga karfe dake" Mami ta amsa da ameen sanan tace" ummi maiye mafita?

Ummi ta rike haiba tace" mafita kenan ana sallamorshi atara malamai Yan ruqiya kawai suriga mishi tofi har tasakeshi"

Tycoon ya Mike yace" ummi ni zan wuce asibiti"

Tace" bamugama magana ba"

Yace" duk abunda kika ga yadace shi za a yi, sai na dawo"

Mami ta Mike tace" jirani na dauko mayafi na muje"

Yace" sai ki fitoh"

Suna isa asibiti Tycoon ko yaji ra a bude minshi kofa ya bude kofar da kanshi, guards na gani hk da sauri suka bi bayashi ya dakatar dasu.. I C U ya wuce Mami na biye dashi, suka Tara a canza ma Aliyu room an cireshi a I C U. Mami tayi ajiya zuciya tace" Alhamdullila son yasamu sauki tunda acireshi a ICU" tana magana saiga haydar yamusu iso zuwa harzuwa daki da Aliyu yake , Allah sarki, Hafiz suna na a zaune su zuba uba tagumi harsu dan fada kamar a jikisu ciwo yake, Tycoon ya binsu daya baya suka yi musabaha cike da girmamawa suka gaida mummy ta amsa .

Tace" Allah ya muku albarka" suka amsa da ameen Mami

Tycoon ya nufi gado Aliyu ya ke kwance kamar gawa, baya ko motsi, fuska na tayi fayau, lips nashi duk su bushe, ya shafa ganshi kan Aliyu yayi ajiya zuciya sanan yace" boy Allah yabaka lafiya suka amsa da ameen, ya nemi guri ya zauna a gefeshi ya kalli fawaz yace" Doctor yajiki nashi?

Fawaz ya su sa Kai yace" da sauki dad.gani sauki ne shiyasa aka canza mishi room.

" Ya farka dai ko ? Mami ta tambaya

Yace" eh mami ya farka around two na dare, sai sambatu yakeyi Yana Kira suna dai Essha, shine kawai mikamishi allura bacci, inshallah na bada jimawa ba zai farka"

" Inalilahi waina ilaihi raju'un, Essha Essha haba haba, wanan Essha mutum ce ko aljan da zata adabi rayuwa dana" Mami ta fada ta rike Kai ta fashe da kuka..

Suleiman dake gefe ta ya Mike ya dafata yace" Mami ba kuka zakiyiba, addu'a zakimishi, Allah yabashi lafiya, yanzu Yana farkawa yaji kina Kira suna Essha Dina Kara rikecewa zaiyi"

Mami ta hada hannu ta na addu'a Tana haweye tace" Allah ga Dana na, ka. Fitar da shi daga ciki wanan hali dayake ciki, Allah na rokeka" suka amsa da ameen, suna amasawa sukaji an bake kofa anshigo bako sallama, suna daga Kai sukaga suhaima ne, dogo riga ne a jikita na atamfa ta cugale dauri dankwali bako mayafi s jikita, car key ne da waya a hannu ta kirar iPhone 11 pro max, Suleiman na gani itace ya baka mata harara, ya Mike ya fice, saura ma suka bi bayashi, don bakarami haushi ta sukeji ba, toh su San hali, ita kam ko ajikita kallo sama da kasa ta binsu dashi taja tsaki.

Suleiman suna yaja tsaki yanemi guri ya zauna yace" wlh I hate this girl, gsky an cuce Buddy, yariya batasan daraja mutani ba, Mai karanci addini" ya Kara ja wani dogo tsaki..

Hafiz yace" Nima ko kallo ta basanyi Mai Kama da sisiya, wlh ko a office ko kallo Bata isheniba, Allah ancuceshi , dubeta ma Kama kara, Allah yasa ma aljanana Essha Dina , aljana ce dagaske, Allah zan iya biyata tayimin maganita yariya ba tarbiya kawai (lolz kuji Hafiz fa).

Haydar yace" Kuna ma da lokaci ta kenan bara kuga hoto da ta daura a page nata na Instagram guri misali karfe 3 na dare fa" ya ciro wayar shi daga aljihu Yana nunamusu hoto suhaima, suhaima ne zaune a club, su hudu itace kawai mace a ciki su, tasa dogo riga ne a cikita ya matse ta sosai ko rabi cinyar ta baiyi ba, fixing da tayi na attach duk ya barbaje tukunyar shisha ne a gabansu, tana tsakiyar maza, hayaki take fesowa cike da korewa a fuska yan samarin.

Fawaz ya ja tsaki yace" tir da hali iri nata, ni narasa dalili da yasa for the first place daddy ya Amince da aure na, wlh da abani irita guda goma goda aban Yar karkara wancan batasa komai ba" duk suka fashe mishi da dariya..

Hafiz yace" ahaf Kar kudamu nasan buddy zaiyi maganita, zanta gane kureta, Allah sarki buddy yaro kirki Allah yabaka lafiya" suka amsa da ameen..

Ciki daki kuwa, suhaima Chewgum take fasawa fas fas kas kas batama San da su Tycoon a daki ba, hankali ta na waya tana chatting, yantsu zaro zaro yasha pink artificial nails, Mami sai binta take da kallo mamaki, Bata cemata uffan ba, ita akullum tir takeyi da Wana Hadi aure batasan maiyasha kan maigida nata ba da ya nace sai ya aura ma Aliyu Wana gataleliyar, kwanaki baya har batawa sukayi akan magana aura Ammi ne tabata hakuri tace su zubamishi idon Allah yasa haka shine mafi alkhari..

Mami ta tabe baki ta bita da kallo.. Tycoon yace" a'a daughter welcome ga guri ki zauna"

Suhaima har ta Dan firgita da taji magana ta daga Kai suka hada Ido da tycoon ta saki murmushi tace" good morning Dad " a tsaye ko ta Dan ragwafa.

Yace" morning daughter ga Mami ki " ta juya ga kallota ga inda yanuna mata, Mami sai binta take da harara kamar idon zai fadi.. na take taji shakku Mami ta sukunyar da Kai tace" good morning ma"

Mami ta amsa fuska a hade ta kauda Kai..

Suhaima Sumi Sumi taja jiki zuwa gefe Aliyu tace" dad ya Mai jiki?

Ya amsa da sauki Yana shafa kafa Aliyu, yana shafa kafa kuwa, kamar ace ma Aliyu ya farka, ai da sauri Mami da Tycoon suka Mike , Tycoon ya rike hannu shi Yana murzawa yace" Aliyu bude Idonka kaji "

Aliyu dayayi kamar zai bude sai yakara lumshe dasu, har yazo yabudesu gabadaya..

"Aliyu, Aliyu " yaji daddy shi na Kira, bai iya amsawa ba, ya yinqura zai tashi Tycoon yayi sauri taimaka mishi ya zauna yace" son sannu yajiki? Bai amsaba ya binshi da kallo yasoma motsa baki yanasa yayi magana ama yakasa. Mami ta rike mishi hannu tace" boy badai jiki bane ko?

Kamar ansashi magana dole yasoma magana a rarabe yace" da...ddy m..ami, kun..gan..ta, kug...amin Essha na"

Tycoon yace" subhanallahi, Aliyu ba kabar magana Essha Dina ba?

Ya dafa saiti zuciya shi yana cewa" daddy zuciya na zata buga da Allah ka taimakeni kanemo mi Essha, daddy imbahakaba wlh zaku iya rasani" da sauri Mami ta rugumeshi tana shafa bayashi Alama rarashi tace" boy kadaina fada haka, kaji ko, take it easy, ba abunda zai saimeka, this Essha you are talking about , we don't even know whether ita mutum ce ko aljan, I probably guess ita jinnu ce, don inba jinnu ba, babu mahaluki da zai'iya rayuwa a ciki wanan daji, ka Manta da ita kaji ko"
Chapter 20 · 0% Book details