← Book details Doctor Eesha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 56

Sashe 2

Doctor Eesha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Essha daki sumy ta haura, daki yayi kyau, teddy ne manya manya guda biyu sucika sama bed, tayi sallama bataji ba, da allamu waya takeyi. Don sai murmushi takeyi. Essha tace" ke Wai da Allah dawa kike waya ne? Sauri fa nake zan wuce. Ta" amsa da Rabin Raina mana, Wai bashir? Eh man. Toh da Allah ki katse Kira Nan don nasa bagamawa yanzu ba, abun zanduba a wayaki, ga amir na jira na a kasa.bestie tace" Naji naji Essha. Sweetheart zankiraka anjima kasan inbana kashe yanzu ba Essha hanamu sakewa zatayi.daga cikin wayan ya amsa da okay bye ki gaisheta,

Tace"zantaji bye.ta katse kira.essha Tace"
Bestie wayaki zakiban jamb Dina zan duba sauri nakeyi.

Ok gashi , sumy ta Mika mata. Tana dubawa, Sumy tace "dazu muka Gama waya da mutumiki, Wai da Allah zakije kaduna da gaske?

eh Esshata amsa da Kai,

sumy ta marairace fuska tace "eya bestie zanyi missing naki gashi zaki wuce bani. Karkidamu bawani dadewa zamuyi ba Monday zamu dawo, Kuma kiga shiyasa na shigo na sallameki gabadaya, Allah sarki ni Khalid ne yaban tausayi, Wai yanaji wani iri a jikishi kamar kar kiyi tafiya na. Wlh Nima hk bestie tun lokaci da dadnina ya fadamin nakeji faduwar gaba. Toh Allah yasa yazama alkhari ameen. Can sukaji Kara shigowar message a wayar sumy. Suna budewa suka sa ihu sanda su mum suka firgita, ya nazeer da gudu ya hauro . Yana tambayasu Mai ye samaiku, ba mgn sai murna. Sumy ne ta Mika mishi wayata, Yana dubawa yaga jamb results din Essha tasamu 252🤗. Yace" wow little sis congrats,
Thanks Yaya ai dole kiyi ihu, Essha buriki yakusa cika. Mum da dad suka hauro . Maiye faru? Ya nazeer ya gayamusu. Wow congratulations daughter ; Thanks ta amsa . Ta juya tace mum sai da safeku da murnata, sumy tace" bazaki jira na raka kiba? a'a na hutar dake . Tana sauka tasamu amir tace" tashi muje yace yadai sis da wuri haka? Eh ta fada. Suna tafiya a hanya Tana bashi labari Jamb nata har suka karaso ciki gate nasu, sai murna yakeyi kamar shine yasamu. Suna karasowa ta tsaya Tana ma gateman mgn aka ya kulle gida bamai fita. Ya amsa da toh. Amir ya wuce ciki ko sallama baiyiba yace" mum,dad sis Essha tasamu 252. Mum tace Allahu akbar, alhamdullila. That's my daughter ai tayi gado na ne, daddy yace" ah ' ah abun gori ne, ai sai duka suka fashe da dariya, dad yace" Ina Essha din? Amir yace Tana zuwa daddy kafi yagama rufe baki sukaji sallamarta, su amsa kosa na mata congrats. Walid yace" sis Essha dole na poping Miki champagne a jiki kiyi kokari . Tace" walahi Kar ka kuskura, Allah daddy kayi mishi magana.

A'a walahi daddy sai na mata ai Ina tayata celebration ne Koh? khairatTace" eh man, Nima zantayaka. Duka su biyu suka nufi dinning area, khairat ta bude fridge ta fitar da champagne guda ta rike daya tabama Walid daya. Duk suka nufota,suka balle murfi, suka fara mata wanka dashi, daddy ne ya dakatar dasu, yace"ya isa kar kusamin likitana tayi mura. Essha wani University kikasa? Tace' Dad A.B.U(Ahmadu bello University z). Daddy yace"Oh natuna, yanzu dai kowa yaje ya kwanta kuga har autana yau tariga ku bacci. Amir da Walid suka amsa da ok dad, good night, yawwa good boy's Allah yatashemu? Ameen. Mum tace" Essha zo ki dauki mufeedat ki kaita daki,toh mum. Khairat tama mum,dad peck a kumatu , tace" mum dad goodnight? Daddy yace kiyi addu' a fa kamin ki kwanta dun nasaki. Daddy I will inshallah bazamantaba. Good yace. Suma suka nufi nasu daki. Essha na kwantar da mufeedat itama ta wuce zuwa nata daki. Wanka ta karayi sanan ta canza kaya, ta dauki wayata, ta bude WhatsApp ta daura results nata a status, friends nata mata congrats, Tana musu reply. Sai around eleven tayi addu'a bacci ta kwanta. Aciki bacci Bata samu nutsuwa ba sai mugaye mafarke mafarke take tayi,nandana ta farka da wani Kara sanda mum da dad suka farka, da gudu suka karaso dakita, da sauri su karaso wurita. Dad yace" lafiya Essha? Maiye samaki? Bata iya amsawa ba, sai ajiya zuciya da zufa ta ketayi. Mum ta dauko ruwa Mai sanyi ta bata, ta yayye mata gashi kanta da ta barbazo a fuskata tace" sannu Essha, maiye samaiki, zatayi magana daddy yatare ta da cewa yi shiru Essha ba ' afada mugaye mafarki. Ta gyada Kai Alama gamsuwa. Mum tace" yi addu' a ki canza gefe kwanciya kijiko? Eh ta amsa murya na rawa. Mum da dad suka fita a daki jiki a sanyaye . A zuciya ta tace ya Allah ka kawomin dauki basan maike shiri faruwa Dani ba.
Washe gari a makare ta farka around 7:00am tayi sauri sauka da addu'a tashi a barcci a bakita, tayi sauri shiga toilet ta Dora alwala tafito da shimfidar danduma ta gabbata da sallah asuba ta Dade zaune Tana addu'a, Tana shafawa, ta Mike ta dauki wayata Tana dubawa taga missed calls din Khalid ne Dana besty, suka cika waya, batayi harama kirasuba, dun tasan besty ta shiga lecture , Khalid Kuma intakirashi ,. Za su iya jimawa suna waya gara taje ta gaida su dad, inta dawo ta kirashi,. Ta jawo teddy slippers nata dake karshi gado ta saka, ta fito jiki a sanyaye, ta Tara dasu amir a parlor suna karatu, duk suka hada baki sukace" good morning sis ? Ta amsa da fara'a da morning my joygivers, how was ur night? Suka amsa da alhamdullila, Ina mum da dad? Dad yaje dauko hajiya,

dakashi? Amir ya amsa da eh Wai batask driving bala driver Wai yacika gangaci, toh Allah yakawo su lafiya, ameen. Ina mum da Kareema(Yar aikisu) ta tambaya? Suna kitchen suna hada ma hajiya koko da kosai. Walid yace" wlh hajiyan nan tacika iyayi,mum tafito daga kitchen ta amsa iyye Walid mamana kake cewa tacika iyayi? A' a mum afuwa da khairat nakeyi, oh nine sa'a ka koh? A'a goggo khairat (😅) mayarda wuka. Taja kwafa. Ina kwana mum, lafiya. Mum tace" zonan Essha ta taho a hankali. Zauna mgn zamuyi, maike damuki? Na lura tun lkc da daddy ki yamiki mgn tafiya ki ka rage walwala, kobakison tafiya ne? Aa mum. Toh kisanki ranki kinjiko baby, Yan uwanki na kaduna Basu da matsala Kuma ai ba wani dadewa zakuyi ba, yau Friday, Sunday ko Monday zakudawo inshallah ,ki sanki ranki kinji ko, eh ta daga kai. Yawwa humaira n, bani wanan smile naki nan, ta washe hakora sai shining sukeyi, yawwa dats my doctor ( inkanaso ga ni fariciki Essha toh ka Kira ta da doctor). Toh ki Taya Kareema hada Kaya breakfast, kinga daddy ki sun kusa da gari lafia, sai kinje ki hada kayaki ko? Owk mum, ta wuce kitchen ta Tara da Kareema na jerewa a ciki tray, tace" kawo natayaki, Ina kwana aunty Essha? Llfy , yasu ummaki? Lfy. Yawwa hada flasks sai kizo ni zanfitar da wanan. Kareema tace" nagode anty, suna Gama jerewa tace "mum baza naje nashirya, okay sai ki fito.

More comment more typing

Comment
and
share🙏🙏🙏😘

Doctor Essha
👩‍⚕️
Written-by j hajara

7️⃣&8️⃣

WACECE ESSHA

Asali sunata *AISHA AHMAD* haifafiyar gari uke ne, dake jahar Nasarawa . Mahaifita cikaikenyin suna shi AHMAD YUSUF NOMA, Dan asali gari uke. Aiki ne ya dawo dashi gari Lafian bare bare da zama.

Matar daya hajiya Fatima, Yana da kanne biyu, Alhaji Adam(daddy karami) da Aunty Jamila suna kirata da(big mum)Tana aure a kaduna,
Mahaifisu ya jima da rasuwa, yanzu maihafiyarshi ne kadai a raye, sunata Hajiya maimuna , ama suna kirata da hajiya uke, Tana zama a uke , anyi anyi ta dawo lafia da zama taki.

Daddy yata mukammai kala kala tun daga kan councilor,har zuwa Dan majilasa, yanzu hk Yana aiki ne a government house dake lafia.

Mummy Kuma business woman ce Tana safara zanuwa, Tana da babba shagota a shendam road.
Allah ya albarkaci su da yara biyar, Aisha( Essha), Yusuf(amir), ummulkhairat, Abdullahi( Walid) sai autarsu mufeedat.
Alhaji Adam Wanda akafi sanni da daddy karami, matarshi daya, Mai kirki ( anakirata da auntyn yara) yara shi bakwai, Abdulhamid, salis, aina' u, khamis, hafsat , hanan sai Hassana daya ta koma.

Sai big mum( aunty Jamila) yara ta itama hudu, usman, Yusuf anakirashi da Abba, hunaisat, Sameer tunda daga kanshi Bata Kara haihuwa ba, ayi magani har agaji. Mijata babba Dan kasuwa ne, big mum ta rige su dad aure don Tana da shekara sha bakwai babasu ya aure da ita. Yanzu haka hunaisat za'a aurar.baya tayi candy nata, tace ita aure kawai take so.

Essha tayi primary and secondary school nata a Hall mark international academy dake ciki gari Lafia, Ta sauke alqur'ani maigirma da saura littafai na addini, ta zana WAEC nata da jamb last year, batasa mu jamb ba, shiyasa tasake maimatawa har Allah ya Bata sa'a tasamu a Wana shekara, Amir na jss3, khairat da Walid suna Jss 1, mufeedat na nursery 2.

Essha hadadiyar yariyace wance bazata wuce shekara shabakwai ba, Tana nan fara ba can ba, baza a sata a siririya ba bakuma za sata a Mai jiki ba, fuskana Mai Dan tsayi, hanci har baki, idon na ya manya manya ba Sosaiba, farare kal kal, lumsheshu, kullum kamar maiji bacci, bakita Dan karami, pink lips gareta, a jiki kuwa ba a magana, dun tana daga ciki jere yanmata da akekira masu coca cola shape, dukiya fulani nan a cike yake dam🙈, haka hips kamar zansu fado.

Kawanta daya tak ko Kuma ice aminiya, *summaiya*, tare suka tashi, tun suna yara har girmansu, sumy ya ce ga Doctor Abbas jibrin, daddyta babban likatane, sai mahaifiyarta hajiya ikilima.

Su biyu Allah yaba iyayasu, nazeer, sai ita summaiya, sumy tun last year da suka zana jarabawa tasamu FULAFIA ( federal University lafia) Tana karata mass com.
Chapter 2 · 0% Book details