← Book details Doctor Eesha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 56

Sashe 25

Doctor Eesha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fawaz ya yi ajiya zuciya yace" Buddy maiyasa kake haka? Duk ka canza, Wai agayama so hauka ne, come back senses, gobe ne fa daurin aureka, suhaima duk girma kanta, jiya tazo ta samai mu da kuka Wai baka kulata, u ignore her calls, ka koma rayuwa kadaici da kunci akan yariya da bakasa mutum ce ko aljana ba.... Ya rage murya yace" Buddy please kadawo kamar da, if this Essha mutum ce ko da jima ko ba dade, zata dawo gareka, ka kwantar da hankali ka"

Haydar ya dafa Aliyu yace" Buddy, fawaz yay gaskiya, kaga duk amare suna kano, da tun safe mun wuce, dun yau akwai event a dare Kuma yakamata ka hallarci guri, gobe 10:00am ne fa za a daura, Ammi aciki damuwa take, maiyasa baza ka farata mata ba? Da Allah Don't say No, kashirya mun wuce, Kai mu ka zo dauka, munshirya flight 7:00pm za mu tashi, please Buddy"

Hafiz yasa baki yace" wlh buddy, duk tsanar da na ma suhaima jiya, San da na tausaya mata, ta na sonka, consider yourself in her shoe, kabar magana Essha Dina, ga luggage naka Ammi ta hadama, kaga ana daura aure gobe sai mu dawo, dubi a office yanda kasa workers a gaba, haba, ka Manta da battun ta, Im ma aljana ce ta Dade da manta shafika"

Aliyu baicce uffan ba, ya juya ya fice yayi hanya garden, da saurisu suka bi bayashi, yana isa ya tarda artist din har ya gama shirya items na zane ready to work, artist na ganishi ya Mike ya gaisheshi cike da girmamawa, ya amsa, ya Sami guri ya zauna Yana ajiya numfashi, ya na dafa kirji, sanda ya natsu na Yan mintuna Sana ya Mike ya kalli artist din yace" are you ready? Artist din ya amsa da yes sir, su fawaz na tsaye suna kallo ikon Allah, Aliyu yana lumshe Ido Essha ya gani, har wani murmushi ya sake, Ido a lumshe ya fara ma artist describing kamani Essha, her face, hair, lips, komai sanda ya zayyana ma artist, harda crying face nata tana haweye, har ya Kai Aya, ya Kara rutse Ido Yana ajiya zuciya, kafi ya bude idon a hankali, Yana gama budewa idoshi ya sauka aka hoto Zane Essha, artist din na gefe Yana mishi murmushi, gaskiya artist din ya kware, don tamkar Essha ne aka daura, harda hawaye dake siyaya a gefe idota.

Aliyu ya tako a hankali Yana hawaye Yana murmushi ya karaso gaba zane, yasa hannu Yana zagaye hoto yace" yaushe zangaki naji sanyi, uhm please ki dawo gareni..... Yata zuba ma Zane Nan kalamai... Haydar ne ya katseshi, gani kyau yariya dake ciki Zane is beyond their imagination, Aliyu da sauri yabar gurin, sai gashi yadawo hannushi rike da cheque da car key sabuwa dal Mai tambari Lamborghini a ciki, ya Mika ma artist cheque din yace" konawa ne ka rubuta nabaka" ya sake Mika mishi key din Lamborghini sabuwa dal.

artist jiki na Bari murya na rawa na murna da mamaki yace" yallabai ayi haka? Aliyu ya karbi cheque din ya rubuta billions of naira da baisan adadi su ba, ya Mika mishi, artist sai murna kamar zai zube a kasa don godiya har da kukashi, yau ne happiest day na rayuwashi, yabar gun da murna ko Kaya aiki bai kwasheba.

Suleiman yace" Buddy wace ce Wana dakayi kyauta billions of naira sbd ita? Badai aljana na bace ko? Dun Wana kyauta ya wuce na mutum"

Aliyu yayi murmushi yake yace" Buddy Essha ce, zan iya bada dukiyana gabadaya ihar zan gata"

Hafiz da haydar su gama rudewa, Hafiz aranshi yace" in wana na hoto ne Essha ,toh tabbas ko wani iri hauka so mutum zai mata toh Ina bayashi"

Fawaz yace" Buddy Essha ka kenan? Ya gyada Kai, fawaz zaiyi mgn Aliyu ya daga mishi hannu ya dakata yace" tun baya haduwata da Essha, Bata ba natsuwa na baku labari haduwa mu ba, toh yau zan gayamuku, Essha da ku ke ta Kira aljana toh ba aljana bace, mutum ce kamar kowa, and she's my wife....

Suleiman yace" dakata Buddy kana nufi ba aljana bace? Ur wife? Yaushe kuka hadu har aka daura muku aure bamusaniba? Duk ya jero tambaya a lkc daya..

Aliyu bai amsa ba, ya nufi guri board da akayi Zane yacire Yana shafawa sanan yace" let's have a sit, yau zanbaku lbr haduwa ta da Essha"

Baya su zauna duk suka zuba mishi ido, Aliyu ya fara Basu labari haduwashi da kungiya da hali dayashiga, the moment he fall in love with her, har aureshi da ita da aka hada , bai boye musu komai har yakai Aya. Their were shock, mamaki da rudewa ya hanasu furta ko da kalma daya, guri yayi tsit , Kara kuka dawisu Nan kawai ke tashi, sun fi minti na a haka, Suleiman ya kada Kai Yana sallati yace" lallai buddy kaga jarabawa, kana nufi kenan u had sexual intercourse with her?

Aliyu ya gyada Kai ya na haweye, haydar haweye sanda ya yi, ya sauke ya Mike ya dafa Aliyu ya furza da iska baki yace" Buddy na matukar tausaya ma, maiyasa baka sanar da mu tun farko ba? Aliyu bai bashi amsa ba ya zuba tagumi.

" Kace kaje har TATARA ba malami? Fawaz ya jefa minshi tambaya .... "Eh" Aliyu ya amsa..

Hafiz yace" ya tsorata ne Killa Kar yan kungiya su bi bayashi, when last ka koma daji ?

Aliyu ya amsa da " tun last week, na tarda daji gabadaya a mayar dashi titi, Kuma nasa aiki daddy ne, don agayamai Ina zuwa daji"

"Aina za'aganta yanzu? Haydar ya tambaya..

"With the help of this za'a ganta inshallah" Hafiz yabashi amsa Yana nuna Zane Essha, ya dafa Aliyu da ya zuba tagumi yace" sai yanzu mu ka gane hali da kake ciki, we misunderstand you, kayafemana, we will stand by you mu taimakamaka har ka ganta inshallah, da Allah ka yafemana, we fail as friends" Aliyu ya janye hannushi ya Mike ya rugumeshi, saura ma suka rugumesu, fawaz har da kuka, Aliyu ya tabbing nashi yace"baku mu laifi ba, Rashi fahimtar juna ne shiyasa, ama ba komai, komai ya wuce" suka saki juna , fawaz yace" Buddy we promised you tare zamu nemonta Kuma zaka ganta, inshallah, duk suka Amince,suka shirya yanda za'a baza hoto Essha har Allah yasa aganta, baya su gama shirya plan nasu, su ka Mike..

"Buddy lokaci sallah yayi, 7:00pm yakusa,ya kalli time.. muna idar da sallah zamuwuce Kuma har da Kai" haydar yafada..

Aliyu ya Bata fuska yace" am not in the mood kawai kuje, da Allah in ku ga Ammi ko Mami kuce musu munatare, ni bazan jeba"

Fawaz yace" eyee ango Essha karya kakeso muyi toh baka'isaba "

Yayi dariya yace" Allah am not in the mood for any partying tonight, I want to be alone"

" Hmmm kasa suhaima bara taji dadi ba ko" haydar ya fada

Aliyu ya daga kafada hali ko inkula ya fice a garden din rike da zane,suka binshi a baya,sai teasing nashi kawai suke Yana dariya...

ESSHA
*************************
Essha ce zaune gaba mummy ta, sanye take da vex da skinny jeans trouser ta yane kanta da white veil, ta canza ta murmure kamar ba itaba, yanzu hankali ta a kwance, ko baki gate daddy ta ya Hana ta fita, gashi ta Kara ci sosai, Essha da da ko Rabin plate batayi yanzu sai ta cinye two plates a take, yanzu ma abinci take ci , hannu baka hannu kwarya, Kar ku zata wani abinci arziki a'a, zalla wake ne tayi mix da gari kwaki da zobo drinks a gefeta , tana ci har tana lumshe ido..

Mummy sai bin ta kawai takeyi da Ido ta na Nazari ta, " ayya ba ciki Essha ke dauke dashi ba, tun last two months nake zargi haka ta fada aranta.( Last two months mummy har ta aiki pt strip, ta karbi fitsari Essha dun ta duba, da hankali ta bai kwanta ba tana son ta tabatar da zargi ta, baya ta aje Ptstrip a gefe toilet, kafi ya bada result, ta shiga kitchen ta duba girki, mufeedat ta shigo da scissors tana gani Ptstrip da yayakashi gunsir gunsir, gani hk ne yasa mummy ta fitar harka abun, tunda jikita bai wani nuna sign ba) mummy tayi ajiya zuciya , tana kallo Essha yada tacika gaba da baya , tace Allah yasa ba abun Dana ke zargi bane.. Essha na hada Kai idota ya hadu da na mummy ta tura baki tace" Kai mummy tun dazun fa kike ta bi na da kallo" ta fada a shagwabe

Mummy tace" hmmm Essha ba komai" Amir da Walid suka shigo..

" Mummy Wai yayshe daddy zai dawo ne? Amir ya tambayi mummy.

Walid yace" mummy sati daya kenan fa"

Mummy tace" yau zai dawo inshallah, ya na ma hanya"

Mufeedat tasa tsalle" ye daddy yau zai dawo"

Khairat tace" tafi can Mai bar na tsiya, mummy ta ja ta gefeta tace" zo zauna Kar su taba min ke"

Walid ya bi mufeedat da harara yace" Bari daddy ya dawo zaku biyani igiya PS4 na da ki ka tsinke"

Essha kam abinci ta takeci hankali kwance Bata kulasu ba, Amir ya leka plate ya ga Mai take ci, ya ga gari ne da wake, ya tabe baki ya janye plate din agabata yace" Allah sis kicika ci abinci kazata, Wana ai sai nayi amai"

Ta Mike ta kwace plate din tace" Ina ruwaka"

Yace" oho dai fake doctor kawai" ta amsa da "eh din naji"

Walid sai dariya yake musu, khairat tace" sis Kuma yayi dadi ? Ta tambayeta tana yamutsa fuska

"Eh Mana ci ki ji" ta Deba ta Kai mata baki, tana samata da sauri tayi kitchen ta furza kamar zatayi amai..

Amir yace" Allah ya shi Kara Mai kwadayi"

"Sis Essha inji bestie Wai na gaisheki" Walid ya fada.

Essha na take ta bar ci abinci ta juya gun Walid tace" Allah Mai tace Kuma baya Wana ?

" Nothing " ya Bata amsa..

Essha ta tsaya shiru ta kalli mummy murya tausayi tace" Da Allah mummy na je, please mummy ? Ta fada kamar zata yi kuka..
Chapter 25 · 0% Book details