← Book details Doctor Eesha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 56

Sashe 49

Doctor Eesha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amir ya ja hannu Sadik ya daurashi a cinyarshi yace" Boy where is your grandpa?

Sadik ya amsa da" he is with my Dad"

Dukasu suka dago suna kallo Sadik da mamaki a fuskokisu. Daddy karami ya nantata" Daddy shi fa toh ai'na suka hadu!

Bai gama rufe baki ba suka Soma ji horn da jiniyar mototoci natashi a kofar gida.

Basu tsaya wani tunani ba duk suka mike suka fito. Essha ko motsawa batayiba Dan tasa su Daddy tane. Kara makewa tayi karshe gado ta na zance zuci.

Walid ya bude gate din, motoci suka sa Kai ciki gidan.

Su Daddy karami Mamaki ma ya hanasu magana sai bi motoci suke da ido har motoci suka gama parking.

Securities nandai suka sake fitowa suka bude motoci. Daddy da Tycoon suka fito lokaci guda. Saura ma duk suka firfito.

Aliyu ne karshe fitowa Hajiya ciki firgici ta matso gabashi ta Soma ta tabashi Nanda idonta ya cika da kwalla bakita na rawa ta kalli Daddy Tace"Ahmadu wa nake gani gabana, Kamar dai Aliyu nake gani Miji Essha da Yan kungiya su ka aura mata ko dai idona gizo yake min kuwa?

Hajiya takai hannu Tana shafa fuskarshi kwalla na zuba. Aliyu ya riko hannu ta Yana murmushi yace" kaka idonki ba gizo yake minki ba ni ne"

Hajiya ta fashe da kuka tace"dama kana raye?

Daddy yazo yaja ta yace"hajiya zo mushiga ciki magana bana nabane"

Suna Shiga su Mummy suka musu tarba na mutuci . Aliyu yasoma baza Ido Yana neman Essha, baiga gatanba sai wansu yanmata biyu yagani masu Kama da ita . Wato khairat da Mufeedat kenan. Sai yaji jikishi yayi sanyi yakasan dago Kai. Yanaji Daddy na basu Mummy labari haduwar su har shirya magana auresu da dagawa ana jira Essha, ya kwashe Tass yanda akayi ya shaida musu.

Daddy karami yace"kaji wani ikon Allah ko. Kai gaskiya Nima naji dadi haka. Ke mufeedat je ki kirawota"

Ammi tace" aa ku barta ta huta. Kar ku sake daga Mata hankali"

Hajiya tace" aa kunji wani daura ma karya gindi, tundama Saboda Wana magana ne yasa ta shigo gida da kuka kamar ace Mata na mutu"

Ji magana hajiya yasa duk suka fashe da dariya.

Hajiya Tasha mur ta kalli Aliyu tace" yaro Sha kurumika Kamar ka mayar da mataka ka gama bi'izinilahi"

Aliyu haryashi sanyi a ranshi ciki sansayar murya yace" nagode hajiya Allah ya Kara girma"

Tace" Bari godemin Dana ni kadai nasan wahala da Yan kungiya suka baka ga jinya so ai Dole ta koma gidaka"

Tycoon yaji Dadi haka nan aka Shiga hira kamar a Saba da juna.

Ciki daki Essha kuwa. Ita dasu Bestie ne da su Siyama su Santa a gaba tun Bata magana hartazo ta sake dasu. Yanmata su shiga ranta. Bestie kam sai kallota takeyi tanason tamata magana akan Aliyu ama tana tsora kartasake tsokolo wani tsuliya dodo taja bakita tayi shiru tana ta Mata dariya kasa kasa.

Essha ta kalleta ta tura baki tace" munafuka shine harda min dariya ko? Ta halbeta da pillow.

Bestie ta cabke ta fashe da dariya tace" da Allah siyama kunji nace wani abun? Kawai dai kice min ki tsargu ne"

Siyama tayi dariya tace" karfa ki Bata Mata Rai dun zaiya Kai karaki guri Ya Aliyu" ta fada ciki wasa.

Bestie ta rike kirji tace" ni wa da Allah ku rufa min asiri maza su binne ni ba mataba"

Duk suka fashe da dariya ama Banda Essha. Tayi shiru tana kallo gefe daya. Rahma ta tapping nata a hankali tace" Anty yadai ana hira ke kiyi shiru?

Essha tayi murmushi kawai tace" bakomai dr"

Sukacigaba da hira sai wurare 6 na yamma family din Tycoon suka shirya zasu koma. Tycoon Yama Daddy sha Tara na arziki da farko Daddy ki karba yayi sanda Tycoon yariga hadashi Allah da Annabi Sana ya karba Yana godiya.

Suka rakasu har baki motar, Aliyu ba haka yasoba shi da za a barshi ma kwana zaiyi. Sai kumbere kumbere fuska yake tayi su Haydar na mishi. Yana kallo su Rahma sun fito suna rike da hannu Sadik tare zasu wuce, Still ba Essha cikisu ya ja karami tsaki yaji sanyi kadan yau zai kwana da danshi na cikishi. Sai binshi kawai yake da idon, suzo za sushiga motar ya saki Hannu Rahma zai koma ciki tace" hey boy where are you going?

Sadik Yana tafiya ya na" sorry aunt, one minute, i want to say goodbye to my mum"

Siyama tayi murmushi tace" yawa Dan albarka toh sai ka dawo munjiraka"

Aliyu ya zagaya ciki sauri ya bi baya Sadik bawanda ya lura dashi. Yaga Sadik yashiga wani Daki dake gefe hannu haggu na parlor shima yashiga da sauri. Yana shiga yaji wani kamshi ya mamayeshi ya lumshe idon a hankali. Ya ji a rike Mai hannu. Ya bude idon a firgice yaga Ashe ma Sadik ne.

Sadik yayi murmushi yace ciki harshe turaci yace" la Papa kaji tsoro"

Aliyu shima yayi murmushi a hankali yace" where's your mum?

Sadik yace" nashigo ba gantaba Killa tana toilet, papa mu zauna munjirata ko?

Aliyu ya daga mishi Kai yana murmushi.

Sadik ya kalleshi shiru can yace" did wanna say goodbye to her too?

Aliyu yace" shsssh reduce your voice"

Sadik yasake rage murya kamar Mai rada yasake nantamishi tambaya.

Aliyu Yana dariya ya amsa da yap.

Ba'afi second goma sukaji Kara bude kofar toilet din.

Sadik ya Mike yace" papa gata zata fito"

Aliyu ya zuba ma kofar toilet din na mujiya, na yafara cin karo da farare dumaduma cinyoyita, sanda ya hade wata shegiya iyau kutt ya wuce. Ya dago Kai ciki sauri yaga daure take da towel fari sol, Dakar towel din ya rufe Mata mazaunata, sai fama share wet hair nata take da karami towel dake hannuta da alama dai wanka tayi, batasan da waesu mutani a daki ba. Ta sauke karami towel din kenan zata shara fuska taci karo da shi a tsaye Yana binta da wani iri kallo Kamar maye, zata saka Kara Sadik ya matso ya rike Mata Hannu Kamar Yana whispering yace" sssshhss Mummy don't scream we just wanna say goodbye to you"

Essha tasoma kame kame ciki ranta tace"tabdijam tare ma suke"

Sadik ya katse ta yace" Mummy zamuwuce bye" ya kalli Daddy shi yace" papa baka ce Mata good bye ba"

Aliyu Yana murmushi bai dauke idosa daga kallota ba ya matso daf da ita Kamar sai ta bata kaiwa yasa hannu ya sukuci Sadik, Essha hartaji tsoro .

Sadik na kafada Daddy shi yasa dariya yace" ye mummy kema kinji tsoro"

Essha ta baka mishi harara ta Kara takurewa a kofa toilet tana Kare kirjita, Aliyu kuwa Kara matsowa yakeyi har ya naiyaji sauti bugu zuciya ta. Yayi murmushi gefe baki yana kashe Mata Ido daya har zai juya sai yasake matsowa yace" Boy close ur eyes"

Sadik ya kulle idoshi gam.yace" okay papa"

Aliyu ya zuba Mata lumsasu Ido sa. Batasan gani kwaya idonshi ciki sauri ta runtse nata gam gam ciki haka kawai taji ya sumbaci kumatuta da gashi kanta.

Tanason ta tureshi tana tsoro tawul dinta Kar ya fadi. Haka ta zuba ma saurauta Allah idon.

Yace" good boy open your eyes"

Sadik ya bude a hankali.

Aliyu yace" Babyyy Bye mu salameki"

Sadik yay sauri yabata peck a goshi yace" Bye mum"

Essha Ido kawai taiya binshi dashi Bata amsaba. Aliyu yayi murmushi zasu fita Sadik ya dakatar dashi.

Aliyu ya tambeyeshi yadai?

Yanuna Mummy shi yace" Bata mishi peck ba" ya fada a shagwabe

Aliyu yayi murmushi mugunta ya karaso gabata Sadik ya juya Mata gefe fuska shi, baya da taiya ta mishi peck, Aliyu daidai saiti kunneta ya Mata rada da Bye bye Dream about me" ya Dora mata light kiss a gefe kunne ya juya suka fice Yana murmushi he feels Happy now.

Essha baki kawai tasake tana binsu da kallo. Takasa motsawa.

Aliyu kam suna fita yaga duk an zuba musu ido dagashi har Danshi mamaki suke basu.

Bawanda yace musu kala, haydar ne ya matso kusadashi Yana dariya kasa kasa yace" Buddy maikaje yi ciki?

Aliyu yace" bansaniba, wuce muje"

Duk suka shiga motar suka fice, Sadik na daga masu hajiya hannu.

Washegari..

More comment 🙏 More typing 🥰
Love you guys 🥰

👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
*DOCTOR ESSHA*
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️

*WRITING BY*
*J Hajara*

🌍 *MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION* 📚 🖊️

*M. W. A*

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoya ta.🤙🏻
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________

7️⃣ 9️⃣&8️⃣0️⃣

Washegari....

Essha kirra Sallah Asuba na farko ta farka, ta zuba tagumi tana tuna mafarki da tayi jiya, Through out dare jiya mafarki Aliyu ta rigayi, ta sauka a hankali ta isa gaba mirror, ta kure ma mirror kallo tana bin kanta da kallo, she can believe herself yesterday night mafarki Shi tarigayi playing love together, ta fuzar da iska baki" ya Allah Kar kasa na fada son Wana bawa nan naka, ya Allah Ina roka kar kasa mafarki na na jiya yazama gaskiya, I hate him I hate him"

Taji wani zuciya na tambayata" why did you Hate him? Ta tsaye shiru kawai ta kasa ba ma kanta amsa, jiki a sanyaye ta fada toilet ta Dora alwala ta fito ta shimfidar daddumar ta gabbatar da Sallah nafilah raka'a biyu, ta na idarwa aka tada Sallah Subhi ta Mike ta bin Sahu ciki natsuwa take Sallahta harta idar ta zauna zama Azkar da neman Zabi ubangiji ta Dade tana rokon har gari ya Soma haske Essha Bata tashi daga kan daddurma ba tana ciki casbaha ta somaji wayata na ringing sanda ta shafa Addu'a sanan ta Mike ta lalubo waya daga kasa pillow, new number ne kafi ta daga Kira har ya tsinke, zata aje wani Kira na sake shigawa ta daga kafi ta yi magana aringata "Aminci Allah ya tabbata agareki ummul Sadik?

Essha ko ba'a fada mataba tagane Mai murya ta yatsine fuska kamr Yana kallota zata dialing guri katse kira. Aliyu ya katse ta ciki sauri yace"Baby please don't cut my call" Kamar kuwa yasa abunda tayi niyya yi kenan.

Can kasa makwoshita tace"maye"
Chapter 49 · 0% Book details