← Book details Doctor Eesha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 56

Sashe 30

Doctor Eesha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta nemi guri ta zauna tana share kwalla, tana daga Kai, tayi ido biyu da wata kyakyawa budurwa, da mamaki ta bude baki tana kallota don yariya Kama take da Alia Bhatt, babacisu kawai tafi Alia Bhatt girma jikine, ta fito daure da towel tana busar da gashi kanta da hand drying, tana gani Essha ta saki murmushi tazo ta rugume ta, ta Mike taba Essha hannu suyi musabaha, Essha kam takasa mgn sai binta take da kallo mamaki,

ta shaking hannu Essha tace" Namaste! Essha Ahmad right? Welcome to India, am your new friend, course mate, my name is Pooja Chandra am from pune, nice to meet you too"

Essha ta saki murmushi tace" nice to meet you too"

Pooja tafara zuba da turaci Tace" ni Yar Hindi ce, ke Kuma musulma ko? ai zamuriga zama tare ba matsala ko? Ki na da kyau sosai, Mr Ra'uf ya bani labariki, ki na da aure, Nima nakusa aure,Nanda wata biyu, mijina da zan aura a Dubai yake aiki, sunashi saif Khan shima musulmi ne, ai zakizo ko? Kiga kena ki zama babba kawana, tundama a kauye mu ba Wanda yakeso yayi kawa Dani saboda nayi kiba da yawa, kina so na a haka ko? Ta fada ta marairace ma Essha fuska...

Essha batasan lokaci dariya ya kubce mata ta Soma kyakatawa, gsky Pooja ta shiga ranta, sanda ta natsu tabar dariya sanan ta gyada mata Kai Tana murmushi tace" ta Amince"

Pooja ta rugume ta, tana murna ta mikar da ita ta Soma zangaya da ita gida tana ta zuba tana Bata labari school, har waje ta kaita ta nuna nata gida su landlord nasu, Essha duk ta gaji, Pooja ta Bata hakuri, ta nuna nata dakita, Essha na shiga baya Pooja ta wuce ta fada gado ta fashe da kuka, ita kanta ta rasa dalili kuka, sanda tayi Mai isarta tukun ta Mike ta share hawaye ta fada bathroom tayi wanka, Tana Gama ta daura alwala ta fito tayi sallah, Tana idarwa ta fara jera kayata a ciki wardrobe, Pooja ta shigo ta taimaka mata suka jera foodstuffs a kitchen tana gamawa ta fito da dambu kaza da mummy ta hada mata taci sosai ta bin da ruwa ta kwanta da kewa gida...

Monday

Tare suke tafiya school da pooja, su tashi Tare, tana fahimta karatun sosai... Tun safe in suka fitai lecture sai 7 wani lokaci har 9 suna kaiwa, su dawo duk a gajiya..a kullum sai tayi waya dasu daddy ta, harda su hajiya suna kirata su gaisa..

Baya three months

Essha ciki ta ya girma har ya Soma fitowa, tana samu kulawa sosai guri Pooja da mummy, Dan ko wani karshe wata mummy take zuwa dubata, su Saba sosai da Pooja, da Pooja Bata da matsala, inkagasu kamar amine juna da sukayi shekaru a tare,a bangare karatun kuwa, karatun take sosai ba Kama hannu yaro, ta mayar da hankali ta sosai ba wasa, har ayi biki Pooja two months dasuka wuce, suyi shagali biki sosai, baya biki miji ya dauketa sukaje honeymoon a Dubai, Essha tayi kewata sosai, sati daya Pooja ta yi ta dawo saboda school, ta koma gida mijita , tayi da Essha ta dawo, Essha taki amincewa, haka ta hakura itama ta park ta sake dawowa gidanasu suka cigaba da zama...

Duk abunda Essha ke bukatar Pooja ne kayi mata,ta hanata to komai sai dai taci ta sh tayi karatun, gashi tana samu kulawa sosai guri mummy da Daddy ta.
tun Pooja baiya girki naija ba har ta kwaya ta kwairai sanadiyar Essha, baza ta iya cewa ma Pooja komaiba dun ta mata abubuwa da ko yanuwata barasa su mata ba, shiyasa a kullum take kara shiga ranta..

Ciki na 6months sukaje scanning, scanning ya nuna namiji zata Haifa, Pooja tagaya ma mummy, su ka fara sayayar Kaya haihuwa, kafi wani lokaci suga ma sayayar komai...

Baya wata tara da Yan kwanaki, Da safe, Essha na zaune , tana tsifa, takkadu ne birjik a gabata, mummy na gefe ta, tana bare ma ta gayda , Pooja na ka gado tana barci, Essha sai mutsu mutsu takeyi ta kasa sukuni, mummy ta kalleta tace" yadai ?

Ta yatsine fuska tace" bakomai mummy"

Mummy ta Mika ma ta gayda ta amsa zata Kai baki taji kamar wani Abu ya tsarga mata mara, ta dakata da sauri, a hankali ciwo ta takeji ya fara tsanata, Essha ta kasa Koda motsi sai cije lebe take, can azaba ya ya tsanata tafara murkusawa, Nan ta fashe da wani kuka Mai Kara, mummy da hankali ta baya kanta tanaji kukata da daga Kai da sauri ta Mike Tace" Essha lafiya?

Tana kuka Tace" Wayoo mummy zan mutu marana"

Mummy tace" subhanallahi" na ta fara Kira suna Pooja.. Pooja na barci ji yanda mummy ke kira sunata tasan ba lafiya ta farka a zabure ta diro daga gado gani Essha a durkushe yasa ta karasawa gareta da sauri, daga ita har mummy dukasu a rude suke, Dan Essha ta Soma fita daga hayacita, azaba takeji sosai, gashi kanta duk ya mutse , duk ta jike gabadaya.

Pooja da sauri ta shiga bedroom nata ta zari car key da mijita ya Bata gift a lkc bikisu, ta koma daki da gudu, tana zuwa da turanci tayi magana tace" mummy dagata mukaita asibiti"
Mummy ta dagata a rike suka fito da'ita, Pooja tayi sauri ta bude back sit ta aka Kwantar da Essha, mummy ta zauna a baya ta Dora kan Essha a ciyarta tana shafa Kai Tana tofa mata duk addu'a da yazo bakita.. Pooja ta figi motar sai asibiti ...

A haraba hospital tayi parking ta sauri ta fito tashiga ta Kira doctor, sai gasu su fito da nurses da gado tura marasa lafiya su ka daura Essha akai, babu Bata lokaci suka shigar da ita labour room.

Pooja da mummy na tsaye gaba labour room suna ta safa da marwa, Pooja sabage rudewa ko takalmi bashi a kafarta, anfi awa hudu ana abun daya, Essha duk ta galaibata , tanaji kamar rayuwa ta ne yazo karshe, mummy duk su shiga tashi Hankali , addu'a kawai take Allah ya sauke ta lafiya....

Karfe hudu na bugawa cib Essha ta sauka, mummy ta dawo daga sallah ita da Pooja su zauna jugum kamar ayi mutuwa,suka jiyo kuka baby daga ciki labour room , mummy ta Mike da hamdala , Pooja tasa ihu ta rugume mummy, can sai ga Doctor da ya amshi haihuwa ya fito da fara'a dauke da baby boy a hannushi da sauri suka nufeshi...shima Yana ganisu Kara saki murmushi yace" congrats ma, is a baby boy"

Mummy ta amshi baby daga hannu doctor Hadi da washe baki tace"Alhamdullilah! Alhamdullila! Allah muna gode maka binsa Wana kyauta " ta rugume boy din a hankali so da kauna yaro na ratsa ta..
Pooja na gefe sai washe baki take, Saba fariciki har ta kasa magana.

Nurses suka fito da ga labour room suna tura gado da Essha ke kwance zuwa rest room, da sauri su suka bin baya nurses din zuwa daki, suka Tara Essha na bacci , nurse ta samata drip , Pooja ta tsaya a gefeta tana gyara mata gashi Kai dasuka barbaje.

Baya komai ya lafa, mummy ta tuna Bata sanar ma daddy ba, da sauri ta duba taga ma ta Manta da waya a gida saban rudewa..

Pooja Tace" mummy zanje na dauko" ta fita da saurita bada jimawa ba sai gata ta dawo, Wana Kara tasa slippers ta Mika ma mummy waya, ta na karba ta dialing number daddy, ringing na farko ya daga da sallamarsa ta amsa..

Tace " albirshika ?

Yace" goro, goro ma fari tas tas"

Tayi murmushi Tace". Toh diyaka ta haihu"

Daddy nazaune a office dama,yanaji ace Essha ta haihu da murna ya Mike har Yana haweye yace" MashaAllah Alhamdullilah, Mai aka samu?

Tayi dariya tace" sabon ango nayi"

Yayi murmushi yace"alhamdullila Allah ya Raya ya Bata lafiya, Ashe dai ankusa shayani gefe " yayi magana cike da barkwaci

Tace" sosai ma kuwa, Sana tace" yaushe zakuzo "

Ya amsa da gobe inshallah, kila muzo dasu hajiya"

Tace" toh Allah yakaimu..ta katse Kira..

Bangare daddy kuwa, su hajiya yakira ya sanar musu , suyi fariciki sosai , daddy karami harda kukasa..

Washe gari sai misali uku na Rana su daddy suka iso, lokaci har àn sallamarsu Essha dun jikita na da kyau,harda hajiya da daddy karami,su zo da Kaya baby dayawa kamar za'a bude karami boutique.. cike da girmamawa mummy ta tarbesu, Daddy ya wuce ida Essha ke zaune gabata ruwa zafi ne ke turiri, cewa tayi tanaji kishi ruwa shine mummy ta,ta hadata da wanan sai fama tura baki take, ta masu hajiya sannu da zuwa..

Daddy ya shafa mata Kai Yana murmushi yace" sannu Essha Allah baki lfy, ya Miki albarka ya Raya abunda aka Haifa"

Ta amsa da ameen da ameen nagode"

Ya juya ga Pooja da tasa tuwa da Miya kuka da mummy ta girka tanace sai ta koyi ci, hajiya na mata dariya..

Daddy yasoma mata mgn ciki harshe turanci yace" Pooja mungode da kulawaki, Allah yamiki albarka ya sauke ki lafia(Kai Ashe ma tana da ciki ba lura ba 😛😅sai yanzu) "ta amsa da amen...

Daddy karami yace" sannu daughter Allah yamiki albarka" a shagwabe ta amsa ta fara complaining ruwa zafi da mummy ta Bata...

Daddy k yayi dariya yace" yi hakuri daughter ,Kisha kiji a haka zai da Kara samu lafiya"

Hajiya tace" wanan ma kadan ne yariya, uke zan wuce dake dagana, imiki wanka jego, in cudiyaki da ganye dawa da ruwa tafasheshe habawa yariya Zaki samu lafiya" duk suka fashe da dariya Banda Essha..

A shagwabe tace" daddy ni dai banza bin hajiya uke ba, exams namu yakusa fa" ta fada kamar zatayi kuka..................

More comment more typing ❤️❤️❤️❤️

Jk to u guys 🥰🥰😍😍
Love you guys 🥰🥰

_👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
DOCTOR ESSHA
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️

WRITING BY
J Hajara

🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION 📚 🖊️

M.W.A

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta.🤙🏻

https://www.facebook.com/107980080946102? referrer=whatsa
____________________________

5️⃣2️⃣&5️⃣3️⃣
Chapter 30 · 0% Book details