← Book details Doctor Eesha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 56

Sashe 24

Doctor Eesha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta.🤙🏻
https://www.facebook.com/107980946102? referrer=whatsa
_________________________

4️⃣1️⃣&4️⃣2️⃣

Khalid yace" love mainamiki? Wani laifi na aikata Miki da kikeso ki hukutani haka? Baby love please talk to me, please forgive me Ina azabtuwa"

Essha naji muryashi ta rutse Idon ta na fitar da hawaye masu zafi, ita kadai tasan yadn takeji a zuciya ta, ta kalli bestie murya a hankali tace" ki ce mishi ya manta dani
Bestie ni....... Ta kasa karasawa kamar an rufe mata baki ta fashe da kuka tace" kawai ki ce mishi ya fita daga rayuwa na, ya daina sona"

Khalid daji haka ya sarke da wani mugu tari, Basu Kara ji komai ba, sai hayaniya mutani, duk hankali su ya tashi, bestie na kuka tace" ki gani ko, kigani Zaki kashe yaro mutani a banza, ki manta alkawari daku ka ma juna ne, Essha Bata ba zato zakiyi haka na, ni zanje na sameshi" ta fice rai a bace.

Essha ta kife a gado tana kuka, bestie na fita mummy ta shigo, duk ta ji hirasu, ta dagata ta rugume Tana lalashita, sanda taga ta bar kuka tace" Essha ki cika Yar halak, ki na bi duk sharadi da daddy ki ya daura Miki, baki bi so zuciya ba,am proud of you, a kullum ki kasace Mai tawakali, in khalid mijiki ne, in Allah yaso Zaki aureshi, komai mai wucewa ne, watarana sai lbr, nasiha sosai ta mata Wanda ya rasata, yasa ta Kara saduda ta mayar ma Allah lamarita..

Bestie lkc dai Mai napep ya sauke ta a Bliss park, tun zurutu mutani tagani su taru a gefe daya, sai baza Ido take ko zata ga Khalid, banshi, wayashi take ta trying ama bai dauka ba, kawai ta yake taje inda aka taru ko Allah yasa tagashi, tana zuwa ta samu ta kusa ciki, Tana shiga khalid tagani kwance numfashi sama sama yake fita, tana ganishi tasa ihu tana a taimaka mata,ba Wanda ya kulata karashe ma watsewa akariga yi daya baya daya, tana kuka ta rasa yanda zatayi , ta fara neman wayashi, ama ba waya, batasaniba, tun lkc da suke waya ya sarke da tari, waya ya fadi,daga ciki masu zuwa kallo ne, wani ya dauke waya.

Khalid numfashi Dakar ya ke fita ga tari ga amai jini, da sauri ta dauki wayata ta Kira Bashir, ta gayamishi hali da Khalid ke ciki, da address din guri, bada jimawa ba sai gasu su karaso, suka Parker motar a gabasu, su uku suka zo, da Bashir sai wani saurayi Mai Kama da Khalid din, ama Khalid ya fishi girma, sai mahaifi Khalid.cike da matsifa baba Khalid ya fito Yana babbali matsifa ya nufo khalid yace" wlh ko zaka mutu, bara ka auri yariya na ba, yariya da aka gayamin tagama talla kanta a titi, shine kake neman kashe kashe ka ka akanta, toh wlh ba ka isaba, Kai ko Mai halaka da yariya bara na bar wani nawa ya aura ba, labari tas yazo kunne na, har hanata fita akayi, sbd abun kunya da ta aikata( ohh ni ya su🤦 mutani mutani, hmmm)..

Toh bakai bar Yar iska yariya na har abada nagayama kenan"

Bestie dake zungune ta kasa gasgata abunda kunnuwata suka jiyo mata, bestie ta ne ake mata Wana shairi , Wana abun da mamaki yake, abun daurai Kai ma Bashir(saurayita) tunda yazo guri yashareta Yana wani kauda fuska kamar bashi ba, bai ko kulataba, tun shekarajiya ta lura da chanzawashi, ga Kuma abunda baba khalid ke fada ya matukar girgiza ta, ta Soma tambaya kanta maiyasa yake aibanta bestie na haka? Yana kirata da Yar iska baya ba halita bane, toh maiyasa ma bestie ta canza? Tsikaro murya baba Khalid tayi Yana cewa" sa shi a motar , Kai Kuma Bashir na ji ance kana nema kawata ko? Toh ku rabu tun da wuri,kafi su shafa ma Kashi kaza"

Bashir ya dagaa hannu Alama baruwashi yace" ai daddy na dadane da cireta,sai dai ta nemi wani a gaba ba niba" ya baka ma sumaiya harara

Bestie ta sandare a guri daya ta kasa gasgata abunda takeji, Kuma take gani da idonta, tana hawaye tayi sauri goge idonta da Karfi ko za ta farka Killa mafarki takeyi , tana budewa dsame tagani , ta fashe da sabo kuka ta nufi guri motar ta rike Bashir tace" sweetheart ni ne fa, Wai maike faruwa ne? Kugayamin, wlh Essha na ba yar iska bace"

Bashir ya fisge rigashi da ta rike ya nuna ta da yatsa yace" kul Kar kisake kirana sweetheart, asiri ku ya tonu, a rayuwa na na tsani mace fasika, Kar ki sake nunawa ki sani , shima Khalid giyar so ne, ke dibarsa ba da daidawabs zai farfado, Allah ya hada kowa da rabonshi" ya shiga motar.
Sumy sandare wa tayi a guri ta saki baki da hanci ta na kallosu
Murya Khalid taji daker yake mgn taji yana cewa" sumaiya kiyi hakuri, ki ce ma Essha Kar ta Manta da alkawari da ke tsakanimu, baza taba daina sonta ba, sai Rana ......... Bata Gama ji maizai fada ba Bashir ya ja motar ya bade ta da kura, suka fice daga park din.

Sumaiya tasa hannu akai tasa ihu kamar zarariya, yau Bashir sweetheart nata , shine ya barta, aka maganar da batasa dashi ba, kowa sai kallota akeyi a park din, zuciya yi yake kamar zai fashe, don tashi hankali, ta zube a kasa tayi kuka Mai isarta, sanan ta Mike Tana layi, yanzu haushi Essha ta ke ji, Taki gayama ta damuwata, ta tsaya shiru, tace kila gaskiya ne abunda baba khalid ya fada, Auzibillahi da sauri ta kori shaidan tace" I trust my bestie, bahaka take ba, ama zanyi fushi da'ita, bara Kara kulataba, har zaitazo gidamu taban hakuri, Bashir Allah na gani zai sakamin" ta share hawaye tace" i love you Essha , bestie Mai tauri kai, da zurfi ciki" ta fada Tana dariya tana kuka, tana tafiya tana magaganu har ta fita daga park , kowa kallo mahaukaciya akemata saboda yada tayi badau badau da kasa a jiki, Dakar ta samu Mai Nepep ya Kai ta gida , tana sallamarshi ta juyo ta kalli gate din gidasu Essha ta murguda baki tace" bestie nayi fushi dake, Kuma ko ki kirani bazan amsabs, har sai kizo gidamu kiban hakuri, gashi Bashir ya gujeni, wayyo Allah na" ta fashe da kuka abun tausayi ta bude gate ta shige "

*************************

Baya wata uku da faruwa haka, Aliyu ya canza gabadaya, yarage fara'a bakamar da ba, kullum bashi da Aiki sai na neman Essha, ba Rana da bai zuwa daji na, yasha zamashi, har TATARA ya je gari mallam Dagana waliyishi, Yan gari suka shaida mishi Bata mallam Dagana guri wata uku kenan dagashi har iyalashi ciki dare suka bar gari, a Rana yi yayi Kamar zaiyi hauka, sbd mallam Dagana ne only hope nashi gashi shima bashi, saura kwana uku bikishi, daddyshi ya tsanata mishi sai ya resume a office, baiyi musu ba , aka daura shi as director of Tycoon companies, Yana zuwa office ama fuskana a hade, duk ya fada, baya bacci kullum kwana yake sallah Allah ya bayanamishi Essha, bai son ci abinci sai Ammi tasashi a gaba, zaici ama baize wuci three spoon ba zai tashi yace ya koshi, Ammi duk tashiga damuwa hali da yaro na ke ciki, tayi fada har ta gaji, ta zuba ma saurauta Allah Ido, sai shirye shirye biki akeyi,, ama ango ko a kolashi,bikisu su hudu zasu ango ce,Aliyu , Idrees, haydar da Hafiz. Sai shirye shirye sukeyi ama Aliyu ko kulasu ma bayayi nema Essha yasa agaba birni da kauye na kd , ba' ida baje nema ta ba, ama ba sa'a.

Ana gobe dauri aure, yadawo office a gajiya , fuskana ba walwala as usual, baya ya watsa ruwa , ya fito ya dauki waya ya Kira artist Mai zanen ya nasan ya zana mishi hoto Essha, zai Dora a media ko Allah yasa a yi dace, Kuma yanasa yariga kallota ko zaiji sanyi, bada jimawa ba dani liti yashigo yasanar mishi yayi bako,
Yace" ya jirani a garden Ina zuwa"

Dan liti ya amsa da" toh yallabai"

Dan liti Yama artist din iso zuwa wani beautiful and fresh garden na gida, koina na guri nature ne, hata kujeru farare dake gurin sanda aka bisu da fresh flowers, gurin a zangaya yake, kasa gurin carpet grass ne, lafiyayu danwisu masu kyau suke yawo a gurin.

Aliyu ya Mike ya dauki wayashi da headphone kala kayashi, 3q ne da armless t-shirt light green ajikishi,ya hada fuska tam yanaji haushi kowa a gida, yanda ya ga anata hidima.

A kullum in ya rinse idon Essha yake gani, burishi a duniya shine ace yau ya wayi gari gashi ga Essha, headphone ya daura waka Aransh ft helena_ Broken angel yake sauraro, kullum sai yaji waka, Yana sauka a matakala waka na ratsashi yanaji kamar tare da Essha yake, hannu shi daya a aljihu Yana bin verse din waka a hankali"🎶🎶 am so lonely broken angel, am so lonely listen to my heart, one and only broken angel come and save me before I fall apart🎶🎶" har ya sauka daga stairs Idona a rufe, jishi kawai take a lovers and lonely mood,zai fita kenan yaji a zare headphone din, firgit ya juya da sauri ya bude idon dayasa aiki Ammi ne........

Comment And share🥰🥰🙏🙏🙏 love you guys

👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
DOCTOR ESSHA
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️

WRITING BY
J Hajara

🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION 📚 🖊️

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta.🤙🏻
https://www.facebook.com/10798094102? referrer=whatsa

_________________________

4️⃣3️⃣&4️⃣4️⃣

Yana juyawa yaga su haydar ne, tun a stairs na farko ya na saukowa suka shigo, suyi sallama baijiba , ya kure volume, idonshi a rufe, dukasu su zagayeshi, Suleiman ne ma ya cire headphones din, suka zuba mishi Ido.
Chapter 24 · 0% Book details