Sashe 7
Ɗan Daba Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Oga Danee ya gyara zama ya na kallon William da ke yi mashi kallon tuhuma,"William na zaɓe ka ne ka zamo makamina saboda cikar wani ɓoyayyen burina da na daɗe ina son gani, tabbas ba'a ɓoyewa abokin cin mushe wuƙa dan haka zan gaya maka kaɗan daga cikin labarin da fatan za ka riƙe min sirrina?"yayi maganar ya na mai zaunawa a kujerar da ke facing da wadda William ke zaune,"ina sauraren ka Oga Danee kar ka damu ni ɗin mai bin umarnin ka a ko da yaushe"cikin jin daɗin amsar shi Danee yace "wannan mutumen da ka gani ba ɗan Adam ba ne aljani ne"waro ido William yayi da sauri yace "aljani?ta yaya ka san haka?to ina ma ka ga mu da shi"yayi maganar a ruɗe.
Oga Danee yace "calm down kar ka wani ji tsoro ba zai cutar da kai ba,shi ɗin ya kasance aljanin da ni ke bautama ya na taimako na a duk lamurrana ya bani abubuwa masu tasirin gaske wanda kallo idon mutum kawai zan yi na gane abinda ke ran shi,to aljanin Gamsak ya faɗan burina ba zai taɓa cika ba sai na samu wanda ya fi ni ƙarfin iko wanda sam ba zan iya ganin abinda ke zuciyar shi.Na daɗe ina nema har ƙasashe da dama na tafi ban samu ba sai yanzu kwatsam na gano ashe kai ne shiyasa ban yi ƙasa da gwiwa ba mu ka tafi"William yace "ni kuma?to ni mi zan iya yi?"Oga Danee ya miƙe tsaye ya na gyara maɓallan rigar shi yace "in lokaci yayi za ka sani,am abinda da dai ni ke so da kai ka riƙe sirri"William na shirin magana sai ga abokan aikin su sun dawo jiki jina-jina.A firgice Oga Danee ke kallon su kafin yace "ya haka?ina kuɗin su ke da sauran mutanen?" "An kama su har sai da mu ka ɗauko kuɗin ashe an yi masu mugun tsaro ta yadda mu na taɓawa jiniya za tayi ƙara"a hasale William yace "aikin banza tirrr duk yawan ku aka rasa wanda zai iya ƙwace kuɗin?Oga Danee shiyasa na so in tafi mtws"ya ida maganar ya na jan tsuki tare da ɗauko gorar ruwa ya sha.
Oga Danee ya nufe shi ya na lalaɓa shi dan kaf cikin yaran shi ya fi son William saboda ƙwazon shi da iya aiki,hannu William ya ɗaga tare da ficewa ya bar gidan gaba ɗaya.Oga Danee ya rufe su da masifa "da kuka ga an kama ƴan uwan ku miyasa ba ku ceto su ba yanzu ga shi za ku ɓallo min ruwa,babban baƙin ciki kuma William ya tafi cikin fushi bari na aika mashi text".
Tsakar gado ya hangota ta game kai da gwiwa ta na kuka,ta na jin motsin buɗe ƙofa ta taso a guje ta na shirin faɗawa jikin shi ta tsaya cak sakamakon sabuwar fuskar da ta gani.Ja da baya ta fara yi har tayi nasarar shigewa toilet cike da mamaki ya fara kiran sunanta amman ta ƙi buɗewa,ya gota ya hango abinda ta ke ma gudu a zuci yace "wato fuskata ta biyu ta ke yiwa gudu"ya faɗa ya na mai kwale fatar a sannu har ya cire ya fito William ɗin shi sak.Wayar shi ya duba ya ga saƙon Oga Danee akan ya je ya sheƙe mutanen su da aka kama kafin a kaisu kotu,lekowa Siya tayi sai ta ga William zaune bakin bed.Fitowa tayi kamar mai koyon tafiya a shagwaɓe ta faɗa jikin shi "minene baby?"da hannu tayi mashi tambaya "who are you ?"tashi yayi ya ɗauko wani albums wanda ake da hotuna.
Ya buɗe hoton wani African man ya bayyana gefen shi kuma wata baturiya ce, William yace "wannan shine babana sunan shi Ahmad wannan kuma Maman ce , Baba ya kasance asalin ɗan Mali ne yayinda Maman kuma ƴar France ce.Sun yi auren soyayya inda suke a France zaune tunda na mahaifina ya ke aiki, kasancewar Maman a gidan marayu ta taso shiyasa ba'a wani samu matsala wajen auren su ba"hoton Siya ta shafa ta na murmurshi ta na son tambayar ta shi ina Baba ya ke amman ta kasa.Wani hoton ya sake buɗowa inda shi kuma ɗan matashin saurayina da ba zai wuce 20years mai kama sak da Baba sai dai shi baƙin shi mai sarkaye da fari hakan ya sa fatar shi bada wani kala na musamman,ganin William ya kasa cewa komi sai ma hoton da ya ke shafa ya sa ta ɗan zungure shi.Ya sakar mata murmurshi yace "wannan kuma Dawood kenan,Yayana ne ya na can India wajen karatun SIDDABARU (Muntasir Shehu)tun ina ɗan shekara shidda ya tafi bai sake dawowa ba wannan hoton ma malamin su ya bani shi lokacin da na tafi kai mashi ziyara"ya ida maganar hawaye na zubo mashi a ido.......
*ÆŠAN DABA*
```love
and
romantic story
``` _MRS SADAUKI_ 💫
*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰
â˜€ï¸ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀ï¸
____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM
Page 11-12