← Book details Ɗan Daba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 33

Sashe 5

Ɗan Daba Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Mata ne da Æ´an mata birjit wasu na shara wasu na baiwa flowers ruwa yayinda wasu ke girki,sakin baki Leemat tayi ta na kallon ikon Allah ashe duk inda ta aje Dawood ya wuce nan.
"Boss ya ne ko ita ma shilar ka har da ita za'a rabawa aikin"cewar Arne,juyawa yayi ya na kallonta yadda tayi wani tsaye kamar sakarai ya so ba shi dariya ya san dai bai wuce ta na mamakin yadda ta ga da jama'a gidan ne ta ke.
Bai tankawa Arne ba ya wuce gun ta ya na tafiyar nan ta ƙasaita mai cike da izza,"keee!"ya faɗa can ƙasan maƙoshi a zabure ta juyo ta kalle shi "mi keke kallo a can ɗin?"ya faɗa ya na harɗe hannuwan shi a ƙirji "ba komi "ta ba shi amsa yace "ba komi kuma kike ta kallonta ko ta burge ki ne?"yayi maganar ya na haɗe fuska.Kai ta girgiza tace "tausayi dai ta bani"yace "na mi fah?"tace "tsohon ciki ne da ita kuma an sata yin shara"ya matso daf da ita yace "eh sai aka yi ya?"tace "na gani kamar hakan na bata wahala wajen duƙawa ne"ta faɗa kamar za tayi kuka.
"Mayeee ?" Dawood ya faɗa da ɗan ƙarfi da gudu Maye ya tawo yace "Oga ga ni"ya na mai kallon Leemata,manunin shi ya ɓurma mashi ga ido da sauri Maye ya dafe idon da Dawood ya tsone yace "ayi haƙuri Oga sharrin zuciya ne,am mi zan yi" "ka amshe tsintsiyar hannun wacan guzumar ka baiwa wannan sannan duk wani aiki da za ta yi ka wannan ce za tayi ta na jin tausayinta ne shiyasa ta karɓi duty ɗin"Dawood ya faɗa ya na mai yin gaba ya shige ɗakin shi.
Cike da jin haushi Maye yace "biyo bayana"Leemat ba tace komi ba ta bi bayan shi ya amshe tsintsiyar hannun Ladidi ya baiwa Leemat nan ta fara share gun ta na ja masu Allah ya isa.
Ta na gamawa Maye ya jata zuwa bayan gida inda ake wanki,tulin kayan su ya gwada mata yace ya bata minti talatin ta wanke su.
Leemat na kuka ta na wanki har ta kusa gamawa sai ga wasu ƴan samari uwanda dama a ƙa'ida aikin su ne,bar masu tayi ta ɗarwaye hannunta ta zagaya ta koma can.
"Ke É—auki tsintsiya ki sake wanke banÉ—akin can na ga ba su fita ba sosai"Maye ya faÉ—a cike da mugunta, Leemat na turo baki ta nufi bayin.
Dawood wanda fitowar shi kenan cikin shiga ta alfarma yace "ita kuma wacan ina za ta je"yayi maganar ya na waro ido ganin ta nufi toilet É—in da ta ke ta kowa da kowa.
Tunanin sunan da da ta gaya mashi jiya yayi sai dai sam ya matan can ya ce "Leemaaaa"cak ta tsaya tare da juyowa duk da ya na daga nesa bai hanata ƙare mashi kallo ba,sanye ya ke cikin riga da wando baƙaƙe ya shace dogon gemun shi tsaf sumar kan shi kuwa sai walwali ta ke.
Da hannu yayi mata alama ta zo,ta yadda tsintsiyar ta tafo tana zuwa gun shi ta fara bubuga ƙafafu ta na shagwaɓa ai kuwa nan kallo ya koma sama wai ɗan cako ya ɗau Giwa.
Yanayin shagwaɓar da yadda ta ke yin magana cikin gunguni ta yadda ba'a ma jin abinda ta ke cewa shi ya shagalartar da shi yayinda mutane suka tsaya suna kallon ikon Allah tare da tausayin irin nau'in azabar da zai sa a gana mata amman abun mamaki sai gani suka yi ya ja hannunta zuwa ɗakin shi.......

#COMMENTS
#SHARE Dan Allah

Jikar Rabo ce 😎
*ÆŠAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

*Na dai gaya maku in babu comment no posting*🤷🏻‍♀️

Page 9-10
Chapter 5 · 0% Book details