← Book details Ɗan Daba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 33

Sashe 11

Ɗan Daba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A zuci Dawood yace "wannan yarinyar ta raina ni,nufinta a rabe za mu kwana ko miye?"ya faÉ—a ya ba mai É—an waigawa ganin ta takure waje É—aya tare da bashi baya.
Mirginawa yayi bai tsaya ba sai da yaji ya kai mata karo "Washhh!"ta furta tare da juyowa suna facing juna,ta turo baki tace "ni yunwa ni ke ji"yace "maishe ni abinci ki canye"tace "tab a da na amayar da kai dan daga ganin ka za kayi bauri"Dawood ya waro ido yace "ko zaƙi ba?"dariya tayi ta na mai tashi zaune tace "a ina ka taɓa ganin Boss da zaƙi tunda kake balle ma nawa Boss ɗin mai baƙin rai da saurin zuci..."kasa ƙarasawa tayi ganin ya tashi zaune shi ma ya na kallonta,ƙuri suka yi ma juna suna hangen ƙwayar idon su ta hasken ɗakin da ya rage.

***MOUMBAY

Hannu Siya ta sa tana share mashi hawaye kafin ta buɗe hoto na gaba,wani gabjejejen mutum ne baƙi ƙirin maras tsayi fuskar shi cike da ƙasumba kallo guda za kayi mashi ka gane babu gurbin imani a tattare da shi.
Cikin jin tsoro ta yamutsa fuska ta nuna mashi hoton,"Oga Danee kenan uban daban Moumbay da sauran ƙasashen Afrika,shi ɗin ya kasance babban tantire wanda yayi ƙaurin suna a duniyar DABA duk wani tantire da kika ji ana magana a kafafan yaɗa labarai to Danee ne shugaban shugaban su.Danee ya kasance *ƊAN DABA* kuma matsafi,duk duniya mutum ɗaya tak ya san ainahin fuskar shi wato mahaifina sai mu yanzu da mu ka ga hoton shi"shiru William yayi ya na kallon Siya wacce tsoro ya kama,da hannu tayi mashi tambaya ya na ina yanzu?yace "shi ɗin ɗan asalin Jos ne wacce ke ƙasar Nigeria,karatu ne ya kawo shi Moumbay inda nan suka haɗu da Daddyna haɗuwar da ta zama ta nadama"....

*Wannan page ɗin ce ta ƙarshe ga group ɗin da ba su comment wannan na nuni da baku karantawa ne*🤷🏻‍♀️

Jikar Rabo ce 😎
*ÆŠAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

Page 17-18

Siya ta dube shi duba irin na alamar tambaya, William yace "eh su na tsaka da karatu Oga Danee ya shigar da Daddy ƙungiyar asiri kasancewar shi ma Daddyn irin mutanen nan ne masu son kuɗin tsiya ya amince suka rinƙa cin duniyar su da tsinke suna facaka da kuɗi,har sai suka shekara wajen goma a lokacin ne ƙungiya ta nemi kowa ya kawo sacrifice ɗin shi kuma makusanci a ke so to nan fah Daddy yace bai san wannan ba.
Cikin zullimi Daddy ya tura Dawood makarantar koyon siddabaru yayinda ni kuma ya tsafe ni ta yadda ba za'a su iya gane ni jinin shi ne ba dan dama Dawood kawai Danee ya sani bai san da zamana ba,ganin Daddy ya ƙi yarda yasa suka kama shi suka kai shi gidan azaba a doli sai ya fitar da wanda za'a sha jinin shi."banda fiddo ido babu abinda Siya ta ke,sai tayi shafi hoton Oga Danee tayi mashi alama da hannu to shi wa ya bada matsayin sacrifice ɗin? murmurshin takaici William yayi yace "Ƴar yayan shi wacce ya fi masifar so ya sadauƙar,da dabara da rumfin baki ya tafi Nigeria ya ɗauko ta a lokacin ba ta fi shekara uku ba a duniya.Tun ranar da aka kawo ta shugaban ƙungiyar gaba ɗaya ya hango wata baiwa ga yarinyar shiyasa yace ba za'a sha jininta ba sai ta cika shekara ashirin da biyar a duniya kafin sannan kuma sun tsafeta ta yadda za ta bada kuɗi sosai sannan da sharaɗin sai Oga Danee ya kwanta da ita tamkar matar shi ta aure wannan shi zai bashi ikon mulkar duniyar matsafa ga ba ɗaya na duniya"William na kawowa nan ya rufe album ɗin amman Siya ta riƙe shi gam ta na mai girgiza mashi kai.
Agogon É—akin ya nuna mata alamun dare yayi sosai,ta turo baki ta na mai jin haushi babu yadda ta iya ta samu gefen bed ta kwanta.
Jawota William yayi ya ɗora saman ƙirji babu jimawa barci ya ɗauke su.

Washegari habshin Michel ne ya tada William daga barci,Siya ya hango zaune kan sallaya ta na tasbihi.Ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya shafa mai,sannan ya duƙa yayi mata kiss a kumatu yace "good morning ma lumière"haka kawai yau taji ta na ƙaunar William murmurshi ta sakar mashi ta na mai nuna mashi tapis alamun ya hau yayi Sallah,girgiza mata kai yayi yace "ni ban yi sallah addinin mu ba iri ɗaya ba ne,am mu ma zuwa gobe za mu yi ta mu sallar a majami'a ai za ki raka ni ko?"kai ta ɗaga mashi yayi murmurshi tare da fita falo.
Direct kitchen ya wuce inda Maman ke haɗa breakfast, huging nata yayi "bonjour Maman"ba tare da ta juyo ba tace "bonjour !tu t'es bien réveillé jspr ?"yace "fine" "et Siya?"ta faɗa ta na duba bayan shi "ta na barci"ya bata amsa ya na mai ɗaukar mug wanda ta haɗa mashi Lipton.
Falo ya koma ya na sha, Michel na gefen shi yayinda Miki ke kwance can nesa da su ta na fama da cikin jikinta da ya fito sosai.
Ƙuri yayi mata zuciyar shi na bugawa da ƙarfi sam bai lura da cikin Miki ba sai yanzu,a ɗan rikice yace "Maman Miki ciki ne da ita?"daga can cikin kitchen ta bashi amsa da "eh nima ban daɗe da sani ba sai bayan tafiyar ka,am ya kamata ka duba lafiyar su ita da babyn".

A dadafe Siya ta koma kan bed ta lafe nan wani barcin ya sake ɗauke ta,sai wuraren ƙarfe takwas na safe William ya tasheta ta hanyar saka ta cikin baignoire.
Har lumshe ido ta ke jin yadda ruwan É—umin ke ratsa ta,sai da ya gasa ta sosai sannan ya naÉ—o kayar shi a towel ya fito da ita.
Tea ya bata ta sha sannan ya fara zuba mata wani kalar abinci irin na can ƙasar su,kai ta girza mashi alamun ba ta so amman sam bai saurare ta ba sai da ya ɗura mata shi sannan ya shirya ta cikin riga da wando suka nufi gun Mama da ke can zaune falo ta na kallon tv.
A hankali Siya ke taka step ɗin ta na ɗan buɗe ƙafa dan har yanzu zafi ta ke ji,da murmurshi Maman ta kalleta ta na amsa gaisuwar da Siya tayi mata da Yaren kurame.Sosa ƙeya William yayi ganin kallon tuhumar da Maman ke yi mashi wanda bai da nasaba da buɗewar idon Siya,kai kawai Maman ta girgiza ta na tunanin sauri irin na William wato har yayi sex da ita bai bari ko ta huta.

Ƙuri Siya ta yi ta zubawa tv ido,karon farko da ta fara ganin tv da abinda ake cikin ta.Kallo guda za ka yi mata ka gane ta na cikin farin ciki, William ya jawota jikin shi ya ɗauki télécommande ya na gwada mata yadda ake canza chaîne amsa tayi ta canza zuwa Tom ans Jerry ta cigaba da kallo yayinda William ya ɗauki Miki ya nufi da ita wani ɗaki dan yi mata scaning.

Da marice Siya ta shiga kitchen ta ɗora girki rice ta dafa tare da yi mata ƴar sauce marar kwaramniya, William na daga gefe ya na kallonta tare da yi mata dariya ganin ba ta iya ko girkin ba sai ta dubi waya ta ke saka ingrédients.
Shi ya tayata kwashewa suka kai falo suka ci en famille,Miki da Michel cikin plate aka zuba masu suma sannan aka ba su ruwa.

Shower ta kunna ta na kallon yadda ruwa ke tsatsafowa daga ciki,hannuwanta ta tara ruwan na ta zuba ciki sai ta zubar da ta gaji da wasa sannan tayi wanka.
Gaban madubi ta tsaya tana ƙarewa ƙirar jikinta kallo ta na mai wasa da jiƙaƙen gashin kanta,wani hayaƙi tare da haske ƙuri tayi da ido tare da zaro wasu abubuwa ne suka shiga dawo mata uwanda suka shuɗe shekaru dayawa kanta ya shiga juya mata babu shiri ta nufi bed ta kwanta.
Towel ɗin jikinta ta cire ta shiga fizge-fizge ta na son yin magana amman babu baki sai motsa shi ta ke,an ɗauki mintoci kafin abu ya lafa.William da ya shigo da ƴar waƙa a bakin shi ya kasa cigaba sai saurin ƙarasawa yayi kan bed ɗin,bai wani ɓata lokaci ba ya caɓi uwanda suka yi mashi lale marhaban ya fara sucking tare da massaging nasu.
Wannan kawai ya fitar da shi hankalin shi, ƙoƙarin shigarta yayi ta farka saboda zafin da ta ɗan ji tamkar wata ƴar maye haka ta ɗan buɗe ido ta na kallon shi bakin shi ya kai cikin nata ya na mai yin having sex da ita kuma.
Cak numfashin William ya tsaya na wucen gadi saboda bayanan cikin zuciyar Siya da suke shiga kwanyar shi tamkar ana transfert haka ya ke jin abubuwan dalla-dalla can kuma suka daina shigowa ashe barci ya É—auke ta gaba É—aya.
A wahalce cike kuma da tsoro William ya zare jikin shi daga nata,gefe ya mirgina ya na tunanin cakwakiyar da ke tattare da wannan sha'ani.
Shiru yayi ya na tunanin zuci "oh shiyasa Daddy yace kar a taɓa bari Miki ta samu ciki kenan?to miye dalilin da ya sa na ƙi ganin komi da nayi scaning cikinta?doli kuma akwai wani ɓoyayyen abu bayan wannan"ya ida maganar ya na kallon Siya da ke sharar barcinta karon farko da yaji ta bashi haushi ya dungure mata kai yace "ƴar baƙin ciki maimakon ta bari har bayanan su gama shigowa kwanyata shine tayi barci mtws"ya ja tsuki tare da shigewa toilet yayi wanka.

Washegari tun da safe William ya tashi saboda zuwa majami'a,Siya da ta gama sallah sai kallon shi ta ke yadda ya shirya tsaf yayi kyau cikin kayan India gwanin kyau.
Nuni yayi mata da toilet ta shiga tayi wanka,babu muso ta shiga tayi ta shirya cikin riga da buje tare da yane kanta da wani kallabi.
Chapter 11 · 0% Book details