← Book details Ɗan Daba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 33

Sashe 12

Ɗan Daba Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Majami'a gun bautar addinin hindu ne sukan je duk ranar Alhamis dan kaiwa Ubangijin su kukan su tare da roƙon shi duk abinda su ke so,tun da suka tafi Siya ta zama baƙauya sai kalle-kalle ta ke yadda ta ga mata da ƴan mata sun sha ado cikin sahari gwanin kyau haka su ma mazan sun yi shigar al'ada.
Ta na daga gefen William wanda ya rufe ido ya na addu'a,wata mota ce mai cike da basawa tayi parking.Da saukar su yaron Abass yace "kai Oga ka ga wata zazzafa?alamu kuma kamar kalar fatar ku ce"Abass ya dubi Siya wacce ke raba ido murmurshi Abass yayi ya nufi motar shi ya na mai cewa yaran shi "ku tawo min da ita"kamar jira su ke kuwa haka wani ya tafi ya sungumo Siya tana zillewa tare son ƙwatar kanta,babu baki balle kuma tayi ihu William ya ji ta.
Mota suka cillata suka baɗe gun da ƙura suka yiwa mota key tare da sharara gudu.

William na gama sallamewa ya buÉ—e ido sai dai aka ce É—auke ta inda ka gani babu Siya babu labarin ta,dube-dube ya fara yi ko zai ganta amman shiru sunanta ya fara kira da sauri can wani tsoho yayi mashi alama da hannu ya je "yaro in dai yarinya nan ta kusa da kai kake nema ka fidda rai domin kuwa É—an gidan Danee ne ya sa aka É—auke mashi ita a gaban idona suka sakata mota,banda ikon da zan cec..."William bai tsaya jin abinda tsohon zai ce ba ya nufi motar shi direct gida ya nufa.
Tun kafin ya shiga ya ke jin kukan Michel babu ƙaƙautawa,da sauri Maman ta fito cikin kuka ta na cewa "William tun ɗazu Michel ke kuka ya na tsaka da cin abinci ban san miye ba"William na shiga ɗaki ya tarwatsar da faux du fleure cikin ƙaragi yace "Maman wannan da kike gani ba kare ne ba Abban Siya ne haka ma Miki ita ce mahaifiyarta,son zuciya irin na mutane yasa ɗan uwan shi mayar da shi kare kawai saboda neman dauɗar duniya,sai dai abinda ni ban sani ba tayaya ita ɗin ta zama karya tunda ba ta cikin shirin Danee?"Maman wacce tayi mutuwa tsaye ta ɓoye bayan William tace "to ina ita Siyai"William ya juyo ya zuba mata jajayen idon shi uwanda suka yi ja saboda ɓacin rai yace "Ɗan Oga Danee ya ɗauke ta, wannan shine babban kuskuren da nayi ta yaya aka yi ni har ban san da zaman Ɗan shi ba?miyasa Daddy bai sanar da ni Oga Danee na da wani Ɗa babba ba?"Maman tace "zai yiyuwa ba ɗan matar shi ba ne saboda Danee sai da ya jima bai yi aure ba".
Michel da ya bar kuka tun shigowar William yayi ƙuri ya na sauraron su, William kuma tsayawa yayi ya na tunanin ta yaya ne har za su koma ainahin ƴan Adam.
Miki ya É—auka ya sake yi mata scaning nan kuwa ya ida tabbatarwa ita É—in mutum ce saboda jaririn da ke kwance cikin cikinta ya na juyawa.

Wata uwar tsawa ya daka mata tare da ɗauke ta da mari ya na mai turata kan bed,sunsunar wuyanta yayi yace "hummm ƙamshi,ashe Afrikawa ma ana samu zazzafa tun da ni ke ban taɓa mu'amala da ɓakar fata ba sai hindu da nasaru yau kam ke kin yi nasara"yayi magana ya na kissing wuyanta,Siya kuwa jujuya ma shi kai take tana son yin magana sai dai babu hali.
Dariya Abass yayi yace "haba ashe kurma ce ?zan ci kare ne babu babbaka kamar kin sani ko na tsani kuka a rayuwata,balle magiya dan Allah kar ka yi ban so hhh haka ƴan mata kan ce in ina hutawa da su"ya faɗa ya na mai yin sama da rigarta.Wayar shi ce tayi ƙara yayi tsuki ya ɗaga "toh Daddy"kawai ya faɗa ya na mai sauka daga kan gadon ya na harar Siya tare da suɗe baki.

*Miyasa za ku yi neman ƊAN DABA alhalin last page ba ku yi comment ba?nima shiyasa na huta in da daɗi ai kun ji*🤷🏻‍♀️
*ÆŠAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

Page 19-20

A hankali ya matso da fuskar shi kusa da tata ya mai hura mata iska wanda hakan yasa ta lumshe ido, "an taɓa gaya maki ke kyakywa ce kuwa?"saurin buɗe ido tayi tana mai cigaba da kallon shi tamkar ba shi yayi maganar ba.
"Tu es très belle Leemat kyawu irin mai tsaftar nan,ke ɗin kyakywa ce ki na wani ɓoyayyen sirri wanda sauran mata ba su da shiyasa har kika yi nasara sace jaririyar zuciya wacce ba ta san komi ba sai kaɗaici"ya ida maganar a raunane wanda hakan ke nuni da ya na cikin kewa.
Gyara zama tayi suna facing juna tare ɗora gwiwoyinta kan nashi sannan ta riƙo hannun shi ta jimƙe gam gabanin ta ɗan rinƙa matsa su tace "gayamin minene damuwar ka Oga?sai ni ke jin furucin ka cikin maraici stp dis moi ce qui n'est va pas?"kamar wani ƙaramin yaro haka ya kwanta jikinta yace "Ma Maman me manque,ina jin kewar iyayena sosai sai dai ban iya tuna fuskokin su balle gun da suke kawai dai abinda na sani ina jina cikin kewa maras misiltuwa"yayi maganar hawaye na kwararo kan fuskar wanda zai iya cewa tun da yayi wayo bai taɓa zubar da su ba.
Damshin da Leemat taji na zuba a bayanta ya tabbatar mata da zubar hawayen shi,ta ɗago shi tana kallon shi kawai sai ta ɗora bakinta kan idanun shi tana tsotse hawayen ta ɗauki lokaci ta na haka kafin cikin muryar kuka tace "ƙaddara mu iri ɗaya ce da ni da kai banbancin su kaɗan ne moi au moins na san dangin mahaifana kuma suma ba sa son mu kuma shi kan shi Abba ɗin b..."azabar da taji ta dirar mata lokaci ɗaya ce ta hanata ƙarasawa "Washhh!"ta furta tare da dafe mara a ruɗe ya fara tambayarta lafiya amman ta kasa maganar sai faman duƙewa da ta ke tana dafe ciki.Hasken ɗakin ya kunna nan ya ga ikon Allah Leemat kuka ta ke wiwi tare da nishi,da sauri ya fita waje ya ɗauko ƙanƙa cikin frigo ya sa shi cikin farar rigar shi nan ya fara danna mata shi a ciki banda lumshe ido babu abinda Leemat ke yi.
An ɗauki lokaci sannan barci ya ɗauke ta , Dawood na mamakin ciwon nata kamar na iska kawai sai ya tâche ɗin jini.Kai ya dafe ya na mai cewa "wai period ne ko mi?shine ƴar rainin hankalin ta kasa gaya min sai da ta ɓata min gado to kin wanke shi in kika tashi"ya faɗa tare da komawa falo ya kwanta dan shi a cewar shi ba zai iya kwana da mai ƙazanta ba.
Chapter 12 · 0% Book details