Sashe 32
Ɗan Daba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Zama Imam ya fara yace waliyai su matso a fara shirin ɗaurin aure, kowanensu shi ya wakilci Ɗan shi Dawood sai murmurshi ya ke baki ya ƙi rufuwa sai ya ke jin ina ma ace bai kasance *ƊAN DABA* ba?da yanzu abokanan shi sun zo sun taya shi murnar ranar farin cikin shi,wasu hawayen takaici ne suka zubo mashi kafin ya kai ga goge su ya ji muryar Arne da Maye suna cewa
"بَارَكَ اللَّه٠لَكَ، وَبَارَكَ عَلَيْكَ، وَجَمَعَ بَيْنَكÙمَا ÙÙÙŠ خَيْرÙ"
```ALLAH YA SANYA MAKA ALBARKA (CIKIN WANNAN AUREN)YA ALBARKACE KA,YA ALBARKANCI RAYUWAR KU DA FARIN CIKI MAI ÆŠOREWA```
Da sauri Dawood ya miƙe cike da murnar ganinsu cikin shiga ta kamala irin ta ƴaƴan musulmai,rungume su yayi gaba ɗaya su kuma su na sake yi mashi Barka da murmurshi kan fuskar shi ya amsa tare da cewa "yaushe kuka zo?"Adam(Arne😹) yace "tun jiya mu ka zo dan oga ya sanar da mu maganar auren ka kuma yace nan za mu cigaba da zama"Moctar(Maye😹)ya karɓe zancen da cewa "mu muka ce kar ya gaya maka mu na son yi maka surprise"kunnuwan su ya murɗe yace "shine dan shegantaka ba ku halarci ɗaurin aure na ba?"ƴar ƙara Arne ya saki yace "ai tun ɗazu mu ke nan har Fatiha mun shafa kawai dai ba ka lura da mu ba"sakin su yayi suna dariya suka zazzauna nan aka shiga zuba abinci.
Miƙewa Siya tayi saboda ba ta son ƙamshin girkin ta nufi inda Leemat ke ciki,a kwance ta tarar da ida ai kuwa ta shiga yin buɗa wacce ta sa Leemat sakin kuka😰 dariya Siya ta shiga yi mata kafin kuma daga bisani ta jawo hannun ta dan komawa part ɗin su saboda gyaran da Momy tace za a fara yi mata.
Babu kunya Dawood ya ƙurawa Leemat ido wacce ke kuka Siya ta jawota,har zai miƙe Daddy ya harare shi sunne kai yayi ya na mai jin haushi cikin ran dan ya so ya tafi ya rarrashi abar sa.
Waje suka fita a cikin jardin Dawood yace "ya kuka yi da mutanen da mu ka kama?"Maye yace "mun sake su sannan mu ka neme su gafara wannan mai cikin ma har da addu'a tayi maka ta kuma ce a gaishe ka"murmurshi kawai Dawood yayi ya na kallon flowers É—in da ke kaÉ—awa kafin su cigaba da hirar yaushe rabo.
Bayan sati guda tuni su Dawood sun koma danƙareren gidan su mai ɗakuna dayawa,babu yadda Momy da Abba ba su yi ba a kan sun koma Niger amman Daddy ya hana a cewar shi an zama ɗaya.
Æangaren siyasa kuwa tuni Oga Darma ya samu kujerar da ya ke so,cikin lumana haÉ—e da adalci ya ke tafiya da al'umma tuni yayi aure shi ma suna gouvernor house.
Waleed da Maman kuwa ana ta koyon karatu sosai kuma suke ganewa dan sun maida hankali.
Arne da Maye sune drebobin Oga Darma yayinda Daddy ma tuni ya riƙe wani muƙami wanda yawan buɗo su a tv ya saka Oga Danee baro ƙasar Moumbay ya koma Niger da zama kafin su hauda mashi tension😹.
Tamkar basarakiya haka Momy ke kula da Leemat duk zumuɗin son kasancewar su amman an ƙi basu damar tarewa sai an gama gyara,tun Dawood na zura ido har ya fara magana amman babu abinda ya canza sai ma tsanani dan Daddy yace sai an shekara ko an bashi ita har yanzu Leemat yarinya ce ƙasusuwanta ba su yi ƙwari ba😹 wannan ya sa Dawood yayi zuciya ya tafi Nigeria ƙarin karatun Islama a gun malamin shi na Maiduguri.
***
Banda ihu babu abinda Mami ke yi hawaye kuwa tamkar Teku ta fashe,lokaci zuwa lokaci ta ke satar ƙafar Oga Danee wacce ta ke sak irin ta kare.Tsananin damuwa da tashin hankalin da ta shiga ya haifar mata da zubar jini,a sukwane Abba ya ɗauke ta zuwa asibiti suna zuwa aka kwantar da ita a gado aka taleta ana ciro mata babyn da guntu-guntu sai ihu ta ke saboda azaba ana gamawa kuma aka yi mata wankin mahaifa.
Sai da ta kwan uku sannan aka sallamo ta,sai a lokacin ne Abba ya tambayeta ina Laila?ba ta ɓoye mashi komi ba ta baya labarin yadda aka yi.Cikin ƙunar rai ya ke kallonta sai dai babu ikon yin magana saboda duk masifar nan shi ya jawota.
A ɓangaren su Laila kuwa alhamdullah bayan gurmuzun kishi da suka tayi ita da Asabe yanzu sun dawo sun haɗe kawunansu, Muntari babu laifi ya na bakin ƙoƙari wajen yi masu adalci yanzu ya na da rufin asiri bakin gwargwado dan har sabon gida ya gina masu ko wace ciki da falo haka ma Inna an yi mata nata ɓangaren.
Shekarar farko Laila ta haifo Twins ɗin ta maza wanda rainon su ya koma hannun Asabe tunda dai ita Dr ya faɗa mata mahaifarta ta tushe saboda maganin hana haihuwa da ta ke sha ba bisa ƙa'ida ba ga kayan mata suma sun so yi mata illa dan ita babu ruwanta da bincike duk wanda ta samu sha ta ke wanda kuma yin haka ba ƙaramar illa ba ce ga rayuwa ɗiya mace.Tun tuni kuma Asabe ta ga illar shan kayan mata barkatai domin in bata sha su ba ta jin daɗin auratayya haka ma Muntari saboda ta riga ta yiwa jikinta sabo da su,ga yawan zubar ruwa dan wani sa'in in ta zauna har zanenta ya ke ɓacewa amman yanzu alhamdullah ta na kan traitement sannan kayan mata ita ke haɗa kayan lambunta ta sha.
Yau tun da wuri suka shirya ita da twins ɗin ta Asabe na gefe ita ma cikin shirinta,yayinda Inna ke waje ta na mitar har yanzu sun ƙi su fito.
Asabe ta É—auki Hassan ita kuma Laila Hussaini suka fito tuni Inna ta fita,gidan suka rufe suma suka shiga motar Muntari yayi mata key.
Tun da suka karyo layin ta hangi ƙofar gidan su cike da kujeru ga mutane ƙwarara,jiki a saɓule duk suka fito ta na gaba suna biye da ita a baya.
Sallama suka yi Abbas da ke zaune a falo ya amsa ya na kallon,"ku wuce ke mana"cewar Mami ta na mai miƙawa Abba kuɗin da ya tambaya.
Sororo Mami tayi ganin Laila riƙe da jariri,bayan duk sun zauna Inna ta basu labarin komi tun daga zuwan Laila har izuwa haihuwar Twins.
Cikin kuka Mami ta shiga godiya tare da nema yafiya,Laila dai ba tace komi ba sai sharar hawaye da ta ke.Muntari kuwa suna ɗan taɓa hira shi da Abbas,Mami ta karɓi yaran ta aza su a cinya ta na ɗan yi masu wasa.
Abba wanda ya ji daÉ—in zuwan Lailar yace "ga ÆŠan uwan ki nan Abbas yau aka É—aura auren shi gobe su ke wuce Moumbay,am Abbas ka kaita ta gano amayar"gaishe shi Laila tayi cike da girmamawa shi ma ya amsa cikin sakin fuska saboda Deeya ta koya mashi hankali da sanin ya kamata.
Sai da suka ci abinci sannan suka wuce gidan su Deeya,sosai Laila ta yaba da Deeya ɗin ita ma sai shige mata ta ke irin an ga dangin zariyar wando😹.
Bayan sun dawo ne Laila ke tambayar ina Jasmine,ai kam ta sha kuka da aka sanar da ita ta rasu.
Sai ƙarfe biyar na marice suka koma inda suka bar Laila ta yiwa su Mami sati biyu,cike da begen Twins Asabe ta bi jarababen mijin su.
***MOUMBAY
A hankali ya ke saukowa daga matakalar jirgin hannun shi riƙe da ƴar ƙaramar tabzaha,gashin kan shi sai walƙiya ya ke.
Murmushi yayi ganin Waleed tsaye bakin mota ya na jiran shi,tako É—aya zuwa biyu yaji an ce "Dawoood?"da mugun mamaki jin muryar mace ta kira shi ya waiga,nan idon shi ya sauka kan Deeya wacce ta sha lalle tayi tsaf cikin doguwar rigar kallo guda za ka yi mata ka gane amarya ce.
Tunanin inda ya san ta ya ke amman sam ya kasa tunawa,ta na shirin zuwan gun shi Abbas ya wani fincikota ta faÉ—a jikin shi.
Taɓe baki yayi ya nufin gun Waleed wanda tun tuni ya buɗe mash mota,shiga yayi bayan ya amsa sannu da zuwan da ya ke yi mashi.Ya na zaune cikin mota ya na tunanin yadda zai kasance da Leemat daren nan yayinda Waleed ke saka tsarabar da ya tawo da ita bayan mota.
A hanya sai surutu William É—in ke yi mashi amman sam hankalin shi bai ma gun shi,sai yaji ya yi magana Farhat (ÆŠiyar da Siya ta haifa) ce ma ya tsoma bakin shi.
Duk mutanen gidan oyoyo suka shiga yi mashi ko wanensu murmurshi kan fuskar shi, little Dawood ya É—auka ya tilla sama ya na yi mashi wasa kafin ya amshi Farhat da ke hannun Siya sai kuma ya fara dube-dube amman bai ganta ba,sunne kai yayi ganin duk mutane na kallon shi tare da yi mashi dariya.
Æangaren shi ya nufa nan wani ni'imtacen Æ™amshi ya daki hancin shi,komi na É—akin rose ne tun daga meubles har rideaux da salon.Murmushi yayi dan ya san couleur préférée É—in Leemat ce wanka yayi ya shirya cikin Æ™ananan kaya ya fita zuwa masjid da ake kiraye-kirayen sallah magrib a can ya zauna har ya yi isha'i.