← Book details Ɗan Daba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 33

Sashe 30

Ɗan Daba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sallah isha'i Muntari ya shigo É—auke da kwanon abinci wanda duk dare Laila ke fiddawa Inna,bayan ya aje ne babu kunya ya yi mata sallama ya wuce É—akin Asabe ba tare da ya yiwa Inna maganar dawowarta ba.
Ƙamshin turaren huta ke ta tashi da murmurshi kamar gonar auduga ya shiga ɗakin,sai da Asabe ta ja aji sannan ta amsa sallamar.
Ruwa masu sanyi ta bashi tare da yi mashi sannu da zuwa ya amsa ya na murmurshi,abinci ta gabatar mashi wanda ya sha maganin da Ayya ta kawo mata cike da zaƙuwa ya fara cin naman kajin ya na gamawa da burodi har ya ƙoshi.
Ruwan wanka ta kai mashi yayi,ko ya shigo da mamaki ya ke kallon Asabe wacce ta shirya tsaf cikin kayan barci wanda tunda suka yi aure bai taɓa ganin haka ba.
Da ɗan saurin shi ya zo zai rungumeta ta ja da baya tace "Muntari miye haka ai ka jira har ƙafa ta tsana na san halin ka kai ba kada sirki"kafin yace wani abu yaji maganar Inna a bakin ƙofa "Zo ka rufe gida ni zan tafi gun waccan baiwar Allah na tayata kwana"da "to" ya amsa Inna na jin haka ta fice ta nufi gidan Laila.
A zaune ta tarar da ita ta saka abinci a gaba ta kasa ci,jin sallamar Inna ne yasa tayi saurin goge hawayen da suka zubo mata.Murmushi ta ƙirƙiro tace "Inna ce ina wuni?""lafiya lau Lailatu ya gida " "alhamdullah"ta amsa a takaice kafin ta tsiyayawa Inna ruwan sanyi nan suka fara taɓa hira wacce rabinta duk nasiha ce Inna ke yi mata.

Tamkar Muntari ya taka rawa dan murna jin Inna ta bar gidan za ta kwana gun Laila,da sauri ya rufo gida ya dawo.
Wata wawura ya yiwa Asabe ya na sauke numfashi kafin ya ɗauke ta ya dire a kan gadonta da ya sha sabuwa drap,ƙamshin da jikin Asabe ke yi shi ya ƙara dagula mashi lissafi ya fara romance ɗin ta Asabe yau duniya ta dawo mata sabuwa jinta ta ke tamkar wata amarya a zuci ta ke cewa "dama haka ake ji in an sha maganin mata,hum ashe na cuci kaina da ban farga ba ni ke zamanni na hakanan"soyayya lubayya yau kam Muntari ya gamsu iya gamsu kyaututtukan da ya yiwa Asabe ba su lisafuwa ciki kuwa har da gidan da suke ciki😹.
Gefe ya koma ya na mayar da numfashi tare da ƙura mata ido sai ya ga tamkar an sauya mashi Asaben shi,yadda ya jita da ni'ima kamar lokacin da ta na amarya ga wani sihirtacen ƙamshi da ta ke fitarwa,ta na ƙoƙarin tashi ya ruƙo hannunta tare da mayar da ita yayi mata rumfa( Ni kuma nace bari nayi gaba tunda na ga alamu abun ba mai ƙarewa ba ne su Muntari an samu yadda ake so😹Ni India zan koma)

***India

A gaggauce ya ke shiryawa yayinda da Daddy, Oga Darma da William ke gefen shi ko wane da abinda ya ke gaya mashi.
William yace "please ka bari na raka ka kaji?"Dawood ya kalle shi yace "no kayi zaman ka dama ba wata isassar lafiya ne da kai ba in uwannan Mayun suka gan ka ka da fitowa da ranka ai sai ta"murmushi William yayi yace "to ai kafi ni kyawu kuma fah naji sauƙi ban jin komi yanzu kawai raɗaɗi ne marar cutarwa"dariya duk suka yi mashi Daddy yace "William ina ka taɓa ganin an ce raɗaɗi kuma ace bai cutarwa?kawai kayi haƙuri ya tafi shi ɗaya in sha Allah zai dawo cikin ƙoshin lafiya kuma da nasara" Oga Darma ya karɓe zancen da cewa "tabbas domin kuwa Dawood ɗina jarumi ne"murmushi kawai Dawood yayi yace "ok zan tafi sai na dawo" "fatan nasara"suka faɗa a tare Oga Darma na seta allon sihirin shi izuwa Masarautar Mayu.

A hankali ya ke taka step ɗin yayinda ya ke gyara zaman agogon hannun shi,ƙafar fita ya nufa yayi tamkar bai ganta ba.Da gudu taje ta rungume shi tare da fashewa da kuka,lumshe ido ya na jin zuciyar shi na dokawa a fili ya furta "ya Allah"domin tun tuni ya yarda Leemat ce raunin shi tun lokacin da ta harare shi haɗe da yi mashi gwalo ya fita harakarta ya na shareta cikin ƙarfin hali.
Hannuwanta ya riƙe uwanda ta zagaye cikin ya da su kafin ya juyo ta izuwa gaban shi,ido ya tsura mata yadda ta ke zubar da hawaye kamar wata ƙaramar yarinya.
Rasa abinda zai yi ya yi kawai sai ya kai bakin shi kan nata ya na mai tura tongue ɗin shi caraf ta riƙe ta shiga tsutsa,wani irin azababen sonta ne ke fuzgar shi mai haɗe da feeling ba dan ya so ba ya cire bakin shi ya maida duban shi gareta sai ajiyar zuciya ta ke saukewa.Ba tare da yace mata komi ba ya raɓa ta gefenta ya wuce,babur ya hau tare da saka hular kwano ya bashi huta.Wawuyar ajiyar zuciya ta sauke ta na juyowa suka haɗa ido da Maman da Momy uwanda suke tsaye suna kallon ikon Allah😂,sunne kai Leemat tayi ta na wasa da yatsunta "ki je ki ɗauki David kar yayi kuka mu za mu shiga kitchen"cewar Mama ta na murmurshi.
Sumi-sumi ta wuce ɗaki ta tsaya kallon little Dawood wanda ake kira da David,har ƙasan ranta ta ke jin son yaron ko dan ya na da sunan masoyinta ne oho.

Tun kafin Dawood ya ƙaraso jama'ar Masarauta suka tsaya cirko-cirko kamar wasu zakaru suna kallon shi,kashe babur ɗin yayi ya na kallonsu.Maza da mata ne yara da kuma ƙanƙana nasaru,baƙar fata da kuma larabawa kowane ya na haɗiyar yawu wanda kallo guda za ka yi masu ka gane sun amsa sunan MAYU.
Ba tare da É—ar ko shakka ba Dawood ya cire hular kwanon ya nufi hanyar da ya ke tunanin ita ce za ta sadaka da cikin Palais É—in.
Wasu dakaru majiya ƙarfi ne suka zaburo tare da tare Dawood, murmurshi yayi ya rikiɗe ya koma kalar su ya fara yi masu magana ta ido kamar yadda Mayu kan yi dan ba kowane lokaci suke magana da baki ba.
Da sauri suka bashi hanya suna wasa baki É—aya daga cikin su yace "ashe duk mu ne bari nayi maka iso gun shugaba"murmurshi Dawood yayi ya na mai take mashi baya har suka isa cikin wani É—aki inda anan ne faÉ—ar SARKI DANEE SHUGABAN MAYU ta ke.
Ido cikin ido suke kallon juna kafin Oga Danee ya saki murmurshi ya yiwa Dawood alama da hannu ƙaraso mana,ƙarasawa yayi ya zo daf da shi miƙewa DANEE yayi yace "maraba da shigowa Masarautar Mayu,masarautar da in aka shigo ba'a fita hahaha"ya ƙarashe maganar ya na kecewa da wata irin dariya, Dawood ya tai yayi magana sai ganin wata sarƙa yayi ta dabaibaye shi ta na mai yin sama da shi.....

*Kuyi haƙuri a gaskiya ban samu damar yi maku Posting sau biyu a rana saboda yanayin ciwona da ya tashi,banda lafiya ina fama da Jinnu ina barar addu'ar ku Allah ya bani ikon yaƙarsu su ida ficewa daga jikina*🙏🏻

Comment and share Please

Jikar Rabo ce 😎
*ÆŠAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

*BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES*👇🏽

*500MB* 200

*1GB* 300

*2GB* 600

*3GB* 900

*6GB* 1800

(CHECKING BALANCE * 461*4# )

VALIDITY : 1 MONTH

For more enquiry Call or Whatsapp this number: *08066268951*

*PAGE 49-50*

Ƙoƙarin fita ya ke daga ragar amman ya cuttura ya na shirin fara karanta formules ɗin tsafi wasu manyan ƙatti suka zo suka ja shi,babu yadda Dawood ya iya doli ya bi su izuwa wani ɗaki mai shegen duhu.A ciki suka jefa shi suka rufe ƙofar da wani narkeken kwaɗo,tsafi da siddabarun duniya Dawood yayi amman ya ƙi yi abinda kuma bai sani ba Palais ɗin Oga Danee arnan aljannu ne cikinta uwanda suka sha sihiri shekaru dubanai da suka wuce da zarar mutum ya taka ƙafar shi ciki to fah shikenan asirin jikin shi zai fita ne ya koma ga uwannan aljannu.
Su Oga Darma da ke can suna kallon allon sihiri a gaban idon su wani abu kamar ruwa ya shiga fita daga jikin Dawood ya na shigewa cikin ƙarƙashin ƙasa, wannan ya dugunzuma hankalin su ashe duk yadda suka yi tunanin Oga Danee ya wuce nan.
Miƙewa William yayi yace "Ni zan je na tawo da shi ba zan bi ta ƙofa ba"Oga Darma ya girgiza kai yace "zuwan ka ba shine solution ba domin kuwa in ka shiga ba ta ƙofa ba doli a ta ƙofa za ka biyo domin an shinfiɗawa Palais ɗin matakan tsaro ta yadda ba'a abu biyu duk waje ɗaya"William yace "kar ku damu in dai na samu na fito da shi fitowar bai wuya"Daddy ya ɗaga masu hannu alamun su dakata ya yi tunani.
Allon sihirin ya duba can ya ɗago kai ya kalle su yace "da buƙatar mu canza salon farauta, William ka bi ta ɓarauniyar hanya ka kuɓutar da Dawood mu kuma za mu je mu tsaya tsakiyar farfajiyar Masarautar mu janyo hankalin Danee ta yadda zai fito ya na fitowa kawai sai Michel yayi cikin shi ya cije shi ta yadda jini zai fito ka ga jinin na taɓa bakin Michel zai dawo a mutum sauran sihirin da ke jikin shi kuwa sai ya wuce Palais dan ya fita daga gare shi ya koma gun aljannun"ko da Daddy ya faɗi haka habshi Michel yayi wanda ke gefen su zaune alamun jinjinawa basira irin ta Daddy,ba su wani ɓata lokaci ba kuwa duk suka fita Michel na gefen su cikin mota.
Ana zuwa bakin Masarauta William ya ɓace ɓat bai dira ko ina ba sai ɗakin da aka rufe Dawood,ɗakin ne ya ɗauki haske kamar an sa ampoule nan kuwa duk cikin shirin William ne.Da murmurshi ya rungume ɗan uwan shi tare da tambayar shi ya aka yi ya shigo,nan William ya shaida mashi plan ɗin su ba'a kau ɗau lokaci ba suka jiyo muryar Oga Darma ya na ƙwalawa Danee kira.
Chapter 30 · 0% Book details