Sashe 24
Ɗan Daba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Zaune ta ke tsakiyar gado ta rafka uban tagumi hawaye na tsiyaya a kan kyakkyawar fuskar ta,ba ka jin komi ɗakin sai sautin ƙira'a Abdullahi Matrood.
"Badiya yanzu ke sabida Allah tabi'ar da kika ɗaukarwa kan ki kenan?kullum kuka sai kace wacce ta rasa uwa da uba?amman kin san wannan ba hanyar ɓullewa ba ce kullum tunani in kuma an tambaye ki kice babu komi"cewar Moma da shigowarta kenan.Badiya ta ɗaga kai ta kalli mahaifiyarta cike da tausayin halin da Moma kan shiga in ta ganta cikin damuwa, murmushi ta ƙirƙiro tace "laaa Moma babu fah komi ni ban ma san lokacin da hawayen suka zubo ba"tayi maganar ta na mai tashi ta shige toilet tari tayi nan take jini ya fito daga bakinta ta kurkure baki ta wanke fuskarta sannan ta fito.
Mai ta murza a fuska sannan ta fito,duk familyn sun hallara kan dining suna breakfast kujera ta ja ta zauna ta gaishe da Dad sannan yayunta uwanda suka kasance duk maza.
Dad ya tsaya da cin abincin da ya ke yace "Diya na kula tunda wannan abun ya faru ba ki sake yin walwala ba,na tambaye ki kin ce bai yi maki komi ba to damuwar ta mice ce? amman babu komi gama cin abinci zan kira docter Maryam ta duba min ke"tari Diya ta shiga yi jin wai a dubata,ɗan tea ɗin da ta sha ta maido sai kuwa gudaje-gudajen jini cike da tashin hankali duk suka yo gun ta tarin kuma ya ƙi tsayawa.
Babu ɓata lokaci Dr Maryam ta amsa kiran Dad,teste ɗin ciki tayi mata duk da ta duba she is Virgin sannan ta ɗibi jininta ta tafi da shi asibiti dan yin exam.
Kanta Moma ke shafawa cike da tausayi Ibrahim, Mustapha da Omar kuwa tuni sun wuce gun aikin su yayinda Dad ke saffah da marwah hankali duk a tashe dan kaf ɗiyan shi ya fi son Diya ƙila kuma hakan bai rasa nasaba da ita kaɗai ce mace.
Babu jimawa Dr Maryam ta dawo riƙe da farar takarda bayani ta fara yiwa Dad da tsureta da ido ko ƙyaftawa bai yi "a gaskiya nayi mamakin yadda aka yi ƴar ƙanƙanuwar yarinya da ba ta fi 17years ba ace ta kamu da hawan jini ba,amman da sauƙi kar ku tada hankalin ku zan ɗorata kan magani in shaa Allah za'a dace"karɓar ledar maganin tayi ta aje kusan Diya wacce ke barci saboda ƙarin ruwan da aka yi mata.
Dad kuwa zaman ƴan bori yayi sai kace wata mace ya fara share ƙwalla "son zuciya ya kai ni ya baro yanzu ga ɗiyata a haɗari ƙila sai da suka firgitata abun ya zame mata psychique"Dad ke maganar zuci.
Haka suka cigaba da gadin ta har ta farka daga barci, Dad ya zauna gefenta ya kamo hannunta "Diya na faɗa min mi ke maki ciwo yanzu? "Kai ta girgiza alamun babu sai ya cigaba da cewa "to faɗa min minene ya saka ki damuwa har kika shiga wannan hali?Dr tace za ki iya samun sauƙin ciwon"da mamakin Dad sai ya ga Diya ta lumshe ido ta na murmurshi sototo yayi ya na kallon Moma wacce ta ke shaye da mamaki.
"Tsarin zubin shi,yanayin tafiyar shi,salon maganar shi,tausayin shi,tsoron Allah shi duk sun yi min ina son shi Dad ka nemo min shi" "wa kenan?"Dad da Moma suka faɗa a tare saurin buɗe ido tayi ta na kallon su sai ta farga ashe a fili ne tayi maganai ba a zuci ba.Miƙewa zaune tayi tace "zan sha jus"Moma ta tai ta ɗauko mata,ta na sha ta na tunanin abinda za ta ce dan kuwa ba za ta iya faɗawa iyayenta *ƊAN DABA* ta ke so.
Cikin son kawar da zancen tace "Dad ya kamata fah a gyara min takarduna ina son yin karatun likitanci,déjà Nadiya har ta gama shirinta"ta na yin maganar ne cikin Shagwaɓa da son nuna ita yanzu babu abinda ke damunta.Ajiyar zuciya Dad ya sauke yace "to babu matsala zan duba lamarin"ihu tayi ta rungume Dad ta na godiya kafin ta fara taka rawar murna dan tun can farko ta yiwa Dad magana amman ya ƙi amincewa.
Wayarta ta É—auko ta kira Nadiya wacce ta kasance Æ´a ga ciyaman na Maradi kuma abokin Dad ne,da murnarta ta shaidawa Nadiya kafin tace "zan zo zuwa marice ki yi min frite irin suyar ki ni ke so tom kar ki ba Æ´an aiki"yadda ta ke nishaÉ—i ya sa Dad da Moma sakin jikin su.
Wuraren ƙarfe biyar na marice Diya ta shirya draber ya kaita gidan su Nadiya wanda ya ke ADS,ta na cin frite suna hira tare da tsara yadda komi zai kasance."to wai yanzu da kayan mu na atamfa za mu je ne?"Nadiya ke magana,Diya ta tuntsire da dariya tace "kin ji banza a India za ki saka kayan atamfa hum lalle shopping za mu je mu yi na riga da wando,abaya da sahari"suka taɓa suna murna Nadiya tace "haka za ayi".
Cikin kwanaki ƙalilan aka shirya masu tafiya zuwa India wajen karatu,magunuka tamkar Diya za ta buɗe wata pharmacie haka Dad ya saya mata su.
"Diya ki kula da kan ki da lafiyar ki kar ki gani dan ban kusa da ke ki zama shashasha,banda kula samari ki yi abinda ya kai ki"cewar Moma ta na mai riƙe da hannun Diya wacce ke ɗokin tafiyar,kiss ta yiwa Moma a kumatu tace "in shaa Allah Momana sai na dawo"nan dai mutane suka fara shiga jirgin.
***
Ya kurɓi cofee ɗin ya dubeta tare da ɗaga mata gira ɗaya yace "ya ki sha mana"tayi murmurshi tace "zafi shiyasa,am kace mu haɗu a nan Plaza"Jasmine ta faɗa ta na mai bashi dukan hankalinta Nas ya ɗan murmusa ya na juya cokali cikin cofee ɗin yace "Yes ina son mu magana ne sérieusement shiyasa na ga da buƙatar keɓewa ta yadda za mu fahimci juna sosai"Jasmine ta gyara zama tace "to ina jin ka "Nas yace "am maganar gaskiya tun ranar da na ɗora idona kan ki naji kin yi min ina son ki da aure ban so kuma ya ɗauki lokaci Daddyna ya kusa dawowa na san kuma doli ya ƙara min maganar aure yaya kin shirya zaki aure ni ?"wani irin gudu zuciyar Jasmine ta fara ta ma rasa mi za tace ita tayi tunanin yadda za ku rinƙa haɗuwa suna cashe ayar su zai yi mata sai gashi ya zo da maganar aure,cikin daburcewa tace "aure?am ka na fah tarayya da Mamina ta yaya kuma za mu yi aure?"ya ɗage kafaɗu yace "so what dan ina tarayya da Mami?zina daban aure daban dan haka kar ki ma damu kan ki in dai dan wannan ne"Jasmine tace "to amman ka na ganin Mami za ta yarda da auren?"murmushi yayi yace "no kar ki damu ai duk na shirya komi iyayen bogi zan samo a matsayin iyayen ki kin ga ana ɗaura mana aure za mu bar ƙasar kwata-kwata mu je can mu sha amarcin mu"saurin rufe ido Jasmine tayi wai kunya🙄Nas kuwa ji ya ke kamar ya haɗe ta dan so tun ranar da ya tarar da su a falo suna barci ita da Laila lokacin da suka je club ya ji Jasmine ta kwanta mashi a rai.
Cofee É—in suka sha kafi su fara cin chawarma suna yin komi ne tamkar masoyan da suka daÉ—e cikin soyayyar juna,haka kawai Jasmine taji mutu karaba ita Nas tare da yi mashi babban gurbi cikin zuciyarta ko dan shine saurayi na farko da yayi mata maganar aure?oho.
Jasmine tayi mamakin ganin dalleliyar motar da Nas ke hawa dan a yadda ya ke zuwa gidan ba za kace ya na da kuɗi ba,shi yayi draving nata har gida a mota sai da Nas ya ɗan rage zafi ita ma ba ta wani hana shi ba.Kasancewar motar irin mai baƙin glash ce babu wanda ya san wainar da su ke toyawa,cire bakin shi yayi daga nata ya na sauke numfashi yace "baby est ce que tu es vierge?"Kai ta ɗaga mashi tace "eh Virgin ce ni miyasa kayi min wannan tambayar?"ya shafi kumatun ta yace "kawai na tambaya ne yadda kika iya kissing haka in sex ma haka ne ai babu kanta na san kingi ne za'a ban"ya ida maganar ya na ɗaga gira Jasmine kuwa har ƙasan ranta taji babu daɗi.Ganin haka ya sa Nas cewa "ke babu fah komi wasa ni ke,ai ni ke ni ke so"murmushin yaƙe tayi kafin ta kimtsa tayi mashi sallama.Ya na kallonta har ta shige gida ya tuntsire da dariya yace "hegiya ni zan auren ƴar duniya duk an ƙwaƙule ki a club ai ni sabuwa dal a leda zan aura ƴar shila wacce komi ni zan koya mata".
Jasmine na shiga gida ta tarar da Mami a falo ta na shan tsamiya gefenta kuma ƙaton tray ne cike da rake sai kwalshi,kai kawai ta jinjina ta shige ɗaki toilet ta shige tayi wanka tare da gasa jikinta sosai ta yadda wai Nas ba zai gane ita ba Virgin ba cece.