← Book details Ɗan Daba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 33

Sashe 19

Ɗan Daba Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sai da ya maida Leemat hotel suka ci abinci sannan ya wuce gun Oga Danee wanda ya aiko mota har hôtel aka zo aka ɗauke shi.
Da isar su suka tarar da Oga Danee a farfajiyar gidan zaune kan kujera ta alfarma Æ´an mata duk sun zagaye shi,kallo guda za ka yi mashi ka gane uban daba ne.
Murmurshi kan fuskar shi ya ke kallon Dawood ya na mai son karantar zuciyar shi sai ruf ta ke a liƙe bai ganin komi tamkar dai ta William.
Gun zama aka bashi tare da tura mashi hotunan Abbas "aiki biyu za ka yi nemo min Ɗana sai kuma kashe wani gwaggon biri mai taurin kai sai dai kafin nan ina son yayi maka cikaken bayani na inda ya aje *littafin sihirin* da ya wallafa"amsar hoton Abbas ɗin yayi ya duba sai kuma ya saka shi cikin rigar aljihu yace "yaushe aka ɗauke shi ?su waye aboka nan shi?wane wurare ya fiya zuwa?"Oga Danee ya miƙe tsaye yace " aikin banza duk ƙarfin sihirin da ke jikin ka ba zai yi maka aiki ba ne ?ko ba ka yi wanka da ruwan ba ne?"Oga Danee na gama faɗar haka jikin Dawood ya shiga karkarwa jijiyoyin kan shi duk suka fito raɗo-raɗo yayinda idon shi suka fara sauyawa zuwa wasu kala tamkar na zaki.
Cikin muryar basawa Dawood yace "an gama ƴallaɓai am ina son rakiyar wani"murmushi Oga Danee yayi ya ɗaga waya ya kira William cikin ƙanƙanan lokaci ya zo.
Gun da Dawood ke zaune ya sunne kai Oga Danee ya nuna yace "wannan za ka yiwa rakiya daga yau ka zamo abokin shi na aiki na san ba ƙaramin citta abun zai bada ba domin kuwa zuciyoyin ku duk a rufe su ke na san kau wannan karon zan yi nasara hhh".
Tun daga ƙafafun shi wanda suke cikin takalmi har izuwa kan shi da ke sunne William ya ke bin shi da kallo bai san ko miyasa ba ya ke jin faɗuwar gaba.
A ɓangaren Dawood ma haka ta ke,bugun zuciyar shi ne ke ƙaruwa yayinda kwanyar shi ke tariyo mashi wasu abubuwa tun na ƙurciyar shi.
"Dawood ga William babban yarona ne zai yi maka duk abinda kake buƙata,am William wannan shine babban yaron Oga Darma "murmurshin yaƙe William yayi ya na jin zuciyar na ƙara wuntsilawa saboda ambatar sunan Dawood da aka yi,daidaita nutsuwar shi yayi yace "Barka da zuwa garin Moumbay Boss da fatan za ka ji daɗin kasancewa a nan har ka gama aikin da ya kawo ka?"ɗagowa Dawood yayi ya zubawa William ido bai ce komi ba sai tashi da yayi ya mashi nuni da ya biyo bayan shi.
"Bi bayan shi ka gwada mashi gari sannan ka danne zuciyar ka dama Oga Darma yace haka ya ke da shegen jiji da kai da izza sai kace shine *ÆŠAN DABA* na farko"Oga Danee ya faÉ—a ya na kallon William da ya bi Dawood da ido,jinjina kai William yayi ya bi bayan shi.
Babur É—in da William ya zo bisan shi Dawood ya ja ya tsaya ya na mai jin haushin katse mashi tunani da William yayi.
A gaba William ya hau ya na mai tada babur É—in, Dawood ya hau ya na mai cewa "ina son ka kai ni gidan babban malamin Æ´an siddabaru na nan garin"dafa.
Madubin babur É—in William ya gyara ta yadda zai ganin Dawood da kyau saboda yadda zuciyar shi ke raya mashi wani abu na daban,suna tsaka da tafiya William ya É—an tsaya yace "gidan malamin siddabaru na nan Moumbay koko na India?"cike da jin haushi Dawood yace "ita Moumbay É—in cikin wane gari ta ke in ba India ba?kaji wani shashanci"William ya É—an murmusa yace "ai duk da haka yankin Kulkata shi mutane suka fi kira da India kasancewar nan É—in Capital ne"banza Dawood yayi da shi tamkar bai ji shi ba.
Ta miror ya ke ƙare mashi kallo kamannin Daddy ne sak suka bayyana a fuskar sabon *ƊAN DABAR* da ya kasance baƙo a gare su,amman inda Dawood ɗin mu ne ta yaya aka yi bai gane ni ba?kuma fah ba lalle ya gane ni ba tunda tun ina ɗan yaro marabin shi da ni,to amman miyasa bai nemi iyayen mu ba?tabbas akwai lauje cikin naɗi doli akwai wani abun na daban ga shi rufafiyar zuciya gare shi balle na gano wani abu"William ke maganar zuci ya na kallon Dawood ta miror wanda shi ma shi ɗin ya ke kallo.

"In ka gama tunanin mu je ka sauke ni hotel tunda na ga alama ba ka san aikin ka ba"cewar Dawood ya na duba agogon hannun shi,cigaba da tuƙin William ya yi ya kai shi gidan mai siddabaru sai dai cikin rashin Sa'a nan aka shaida masu rasuwar shi.

A bisa hanya Dawood ya tambayi William"a ina ne hanyar madafur?"wani uban burki William yayi babu shiri yace "mi za ka yi a can?"Dawood ya tanke fuska yace "a can Abbas ya ke cikin wani gidan gona dan haka kai ni za ka yi ka tawo min da shi"wani irin ƙwarewa William yayi yace "ya aka yi ka sani?"amsa ya bashi da "ƙarfin iko ne da sihiri"ba dan William ya so ba haka ya kai Dawood unguwar ba tare da ya yarda ya kai shi har ƙofar gidan ba.

Makulin gidan ya taɓe tare da shiga cikin gidan ba'a jima ba ya fito da Abbas wanda duk ya galabaita,a tsakiya suka sa shi suka wuce gidan Oga Danee.
Kawo Abbas ba ƙaramin ƙarawa Dawood matsayi ya yi ba a zuciyar Danee,cike da murna ya kira Oga Darma ya shaida mashi aiki yayi kyau da alamu kuma lokacin cin nasara ne yayi, Oga Darma yace "Ni na gaya maka yarona babban *ƊAN DABA* ne kuma mai sa'a yanzu abinda za'a yi nima zan zo Moumbay ɗin ina jiran wani abu ne da ya kammala za ka gan ni "
"To Allah kawo ka lafiya sai dai kar ka manta da ajiyata ya kamata ka ɗaukota saboda bai fi kwana goma ba shekarun BIRTHDAY ɗin za su cika"cewar Oga Danee,cike da dariyar mugunta Oga Darma yace "kar ka damu ka ƙaddara ma yanzu haka ta na garin Moumbay har an kawar da budurci buri ya kusa cika hhh" kasancewar Danee wawa ne sam bai gane komi ba sai sallama da yayi mashi.

Ya aje waya yace "William kai Boss masaukin shi sannan ka dawo akwai plan É—in da za mu shirya kafin zuwan Darma am Dawood ka tabbatar da ka bincike shi da kyau"kai Dawood ya jinjina.
Har cikin farfajiyar hotel ɗin William ya shiga da shi,haka kawai Dawood ya ji ya na son ƙulla alaƙa da William har ya juya babur yace "am ka shigo daga ciki ka ga inda na sauka"cike da murna ya bi bayan shi knowking yayi Leemat ta buɗe ɗakin ta waro ido ganin baƙuwar fuska,gaban William ya bada dam a zuci yace "mi ya kawo leemat nan kuma?miye alaƙarta da shi?".
"Ka ga inda na sauka nan al gobe ka zo tun da wuri sai mu wuce tare"kai kawai William ya jinjina yayi saurin fitowa.

Ko da ya shigo gida bai tsaya komi ba ya wuce cikin ɗakin shi,book ɗin sirrin shi ya ɗauko ya shiga bincike har ya kawo wata page inda aka rubuta *ƘADDARA ZUKATA BIYU* (My next book in shaa Allah).

```Yadda ƙaddarar ka da Siya ke manne da juna haka ma ta ɗan uwanka Dawood za ta kasance da ta ƴar uwar Siya, wannan ƙaddarorin sune nasarar mu da farko haɗuwar kowanen ku da ɗan uwan shi,na biyu ku ɗin garkuwar juna ne,na uku ta hanyar Dawood farin cikin ka zai dawo``` tsayawa yayi ya shiga nanata "farin cikina zai dawo,farin cikina zai dawo to kamar yaya fah ban gane ba?"da yaji kan shi ya ɗau zafi kawai ya shige toilet ya sakarwa kan shi shower.
Chapter 19 · 0% Book details