← Book details Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 22

Sashe 9

Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni dai bance komai ba na koma na zauna, muka cigaba da firar mu.
Babu jimawa sai ga Al'amen ya fito, yana wata tafiya kamar bijimin sa. Haushi yasa na ɗauke kaina, ina addu'ar Allah yasa kar Aunty Fati ta kalle shi, dan sai naga kamar abincin da yaci yasa tumbin nasa ƙara bayyana.

Sai naga ashe ma tuni kallon shi take, a ranta tana faÉ—in _Ikon Allah. Ashe dai da suke wa Al'amen kallon me tumbi, dan basu ganshi kusa bane shi yasa. Sai yanzu ta lura da uban tumbin nasa kamar rumbu, ita kanta sai da tace Allah ya bawa Rahamah lafiya._

Sallama ya mana, akan zai je ya duba wani aiki da ya bada a masa, na ginin masallaci, daga nan zai je shagon shi sai ya dawo.

Aunty Fati ce ta bishi da addu'a.

Bayan tafiyar shi wuni guda muna tare da Aunty Fati, sai bayan la'asar ta tafi.
Gidan ya rage sauran Ni kaɗai, tunda nasan ba girki zan yi ba, sai kawai na shige ɗaki na ƙara kwanciya.

Da Magriba sai ga aiken abinci, wai in ji Hajiyar Al'amen. Dana buÉ—e da sauri na rufe, dan bana shiri da amala kwata-kwata a rayuwata.
Ita ce cike da kula a mulmule a leda, sai miyar ayayo da d'anyar kuɓewa da stew wadda aka zuba mata ganda da namomi manya-manya.
Miyar ce kaÉ—ai ta burgeni, sanin ba ci zanyi ba, sai kawai na ajiye a farlo na koma É—aki.

Tunda nasan na rufe ƙofar farlon, kai tsaye bayan nayi sallar isha'i na yi shirin barci cikin shigar doguwar riga har gwiwa, na sa hular net na bi jikina da turaren humra me ƙamshi na shafe, koda ina gida na riga dana saba in zan yi barci sai na shafa humra dan akwai ni da san ƙamshi.

Can cikin barci naji kamar motsin mutum ya shigo É—akin, cikin tsananin tsoro na tashi ina raba ido cikin duhu, na shiga laluben makunnar fitilar É—akin dake jikin gado.

Da ƙyar na kunna ɗakin ya gauraye da haske baki ɗaya, Al'amen na gani tsaye cikin shigar manyan kaya, hannun sa riƙe da ledoji.

Muna haÉ—a ido ya wani washe min baki, yana bin jikina da kallo kamar tsohon maye.
Lura da abinda ya ke kallo, da sauri na jawo bargo na lullu'be ƙirjina, zuciyata na wani irin bugawa, ina tambayar kaina _Ta ina ya shigo bayan nasan na kulle ƙofar?._

Ban gama tunani ba naji Muryar shi "Har kin fara barci kenan My Babynah, to ki tashi ki sakko tafa samu, dan kaji ne waÉ—anda suka linka na rannan a girma, sannan na haÉ—o miki da lemuka masu sanyi dan ki ji daÉ—in cin su."

Duk da irin tsoro da fargabar da nake ciki, hakan bai hana ni galla masa harara ba, ina jin takaicin maganar shi _Wai na tashi naci kaji sai kace ance masa mayya ce ni, dan tsabar rainin wayo irin nashi harda wai sun fi na rannan, ko an faÉ—a masa naci wancan ne bare wannan._

Maida kaina nayi gefe nace "Bana ci. Dan Allah na roƙe ka ka fita a ɗakin nan, in ka fita ka ja min ƙofar."

Dariya ya yi ya nufo bakin gadon, yana faÉ—in "Wanne irin na fita daga É—akin ki, bayan ni É—in mijin ki ne kuma sabon ango a daren nan."

Yana nufo gadon ina ja baya, ganin haka yasa ya fashe da dariya yace "Au Wai gudu ki ke? Ki kwantar da hankalin ki, komai a sannu nake so mu yi shi, bana son wannan tsoron da ki ke nunawa dan Allah."

Ganin bai hau gadon ba, ya tsaya ya aje ledar hannun sane, hakan yasa na sauke ajiyar zuciya ina ƙara ƙanƙame bargon dake jikina.

*09014644247*

*_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍🏻✍🏻_*

[1/18, 07:15] Ummu Sultan Ceh3: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EJJOOxsRu8dKh9gocmSFuG
*BAKAR ZUCIYA!.*

*_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍🏻✍🏻_*

*_LITTAFIN KOWA YAƘI JI YA KAMMALA COMPLET, GA MAI BUƘATA TA MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 09014644247_*

*PAGE 5️⃣*

Yana aje ledar, naga ya fara cire babbar rigar jikin sa. Da sauri na ɗauke kaina ganin yana ƙoƙarin cire rigar jikin sa.

Aiko ina juyowa nayi mugun gani, dan ya cire rigar daga shi sai dogon wando, da singlet, tumbin ya ƙara zazzagowa ƙasa.

Zama ya yi dirshan a ƙasan carpet ɗin, ya jawo ledojin daya shigo dasu ya fara fito da kayan ciki.
ÆŠauke kaina nayi, gaba É—aya zuciyata ta kasa nutsuwa, Ni kaÉ—ai nasan fargabar da nake ciki akan zaman shi a É—akina.
Har hararo halin da zan shiga nake, in na shiga hannun wannan azzalumin, daga ganin shi ba tausayi zai yi ba bare ayi maganar sassauci.

"Ki sakko ki ci fa, dan babu abinda ya dame ni, rashin cin da za ki yi ba zai hanani abinda zan yi ba."
Maganar shi ta sa na juyo, addu'o'i na fara ja a zuciyata kawai.
Ina neman tsari da wannan mutumin.
Sai dai addu'a ta bata amso ba, zama ya yi ya dinga haƙar naman kamar wanda bai taɓa cin nama ba, yana gama ci ya kora da madara me sanyin, tare da sakin gyatsa me ƙarfi babu Alhamdulillahi babu komai ya tashi tiɓi-tiɓi ya nufo gadon. Wani uban tsalle na buga da nufin sauka, sai dai na makaro tuni ya kakkane bakin gadon babu hanyar gudu.

Ina ji ina gani ya tarda ni, duk irin kiciniya da tirje-tirje nake da su cizo da yaƙushi a banza.
Yadda kuka san dutse, haka mutumin nan ya koma kamar wani mahaukacin kare ko kurma.
Kwata-kwata duk abinda nake bai san ina yi ba, dan gaba ɗaya kamar ba'a a hayyacin sa ya ke ba. Ina ji ina gani ya rabani da kayan jikina ba tare da tausayi ko imani ba ya fara ƙoƙarin cimma burin shi.

Tun ina kuka da ihu har sai da ƙarfina ya ƙare. Ban ƙara sanin inda kaina ya ke ba, sai da sanyin asuba ya buge ni na buɗe idona a hankali na sauke su akan fankar saman dake wulwulawa. Kaina naji ya wani irin sarawa kamar zai rabe biyu, a hankali na yunƙura da niyar tashi.
Wata irin azaba da raÉ—aÉ—i da naji yasa na koma na kwanta ba shiri, tare da fashewa da wani marayan kuka da duk wanda ya ji sai na bashi tausayi.

Uban munsharin da naji an fara saki, yasa na juya gefena a hankali.
Da sauri na runtse idanuna ina jin wata irin tsanar shi ƙyama takaici baƙin ciki, duk suka kama ni a lokaci guda.

Kwance ya ke babu komai a jikin shi, ya wani irin bajewa yana barci da sakin munshari, abin babu kyan gani.
Duk kuma kukan da nake bai ma san ina yi ba, dan da alama yana da nauyin barci.

Na daÉ—e ina kuka wai ko zai farka ya taimaka min, saboda a kunne na aka sallame sallar asuba, burina na samu na shiga toilet na yi wanka na gasa jikina na yi sallah.

Sai dai ina bai san ina yi ba, ganin haske ya fara shigowa ta window alamar gari ya fara wayewa, dole na fara jan jiki duk da irin raÉ—aÉ—in da nake ji na sauka gadon.
A zuciyata Allah ya isa kawai nake jerawa wannan azzalumin.
A haka da jan jiki na kai kaina toilet É—in, cikin dubara na tara ruwan zafi a kwamin wankan, na surka shi kaÉ—an.
Da ƙyar na zauna saboda zafin ruwan, amma bani da wata mafita bayan hakan, hakane zai sa naji dama-dama.
Sau uku ina canja ruwa, sai sannan naji dama-dama har na iya miƙewa tsaye.

Alwala na ɗauro ina tafiya a hankali na fito, cikin dubara nake komai har na zura doguwar riga, na sa hijabi na tada Sallah. Na daɗe zaune ina kai kukana wajen Allah, akan Allah ya zaɓa min abinda ya fi zama alkhairi a rayuwata.

Can naji motsi na juya na kalli gadon, shi na gani ya farka ya tashi zaune, kuma har lokacin bai suturta jikin shi ba, ko kunya ba ya ji shi gashi ba kaÉ—an ba.
Kauda kaina nayi na cigaba da azkhar É—ina, dan bai ganni ba da alama barcin bai gama sakin shi ba.

Ji nayi ya buga wani irin ihu, yana nuna ni.
Cikin tsoro na kalle shi, da sauri na ƙara kauda kaina ina kallon gefena ko yaga wani abin tsoro ne, dan har lokacin ba komai a jikin shi yana tsaye bakin gado.

"Baki da hankali baki jira ni ba ki ke sallah?."
Ya faÉ—i hakan yana nufo inda nake.

Cikin mamaki nake kallon shi, wanne irin in jira shi in zan yi sallah? Sai kace shi zan wa sallar.
Jin da nayi ya fincike dardumar da nake kai, har sai da nayi baya na faÉ—i, cikin jin zafi nace "Wash me na maka?."

Rufe ido ya yi ya fara faɗa "Ya za ki yi sallah ba tare da izinina ba, gashi yanzu kin ɓata min komai kin ɓata min aiki, wayyo Allah na wannan yarinyar baki da hankali wallahi."
Yana gama faɗin hakan ya wuce ni tiɓi-tiɓi ya ɗauki wayar shi dake gefen gado.

Sakin baki da hanci nayi ina kallon ikon Allah, wanne irin sai na jira shi zan yi sallah? Ban gama tunani ba naji ya danna kiran waya.

Cikin tashin hankalin dake shinfiɗe a fuskar shi ƙarara yace
"Hello Malam Barka da safiya." Jim kaɗan naji yace "Ina fa lafiya yarinyar nan ta ɓata mana aiki baki ɗaya."

Bansan me wancan yace ba naji yace "Kasan nauyin barcina fa Malam, to Wallahi sai farkawa nayi na ganta zaune har ta gama sallah, ta cuce ni wallahi."

Gaba É—aya ban fahimci abinda yake nufi ba, kaina duka ya É—aure, ina mamakin duk akan sallar da nayi ya shiga tashin hankali haka? Ko kuwa wani abin na masa daban da ya tashi hankalin sa?.

Da sauri naga ya aje wayar, ya juyo ya kalle ni a wani irin fusace ya yi ƙwafa ya nufi toilet a yadda ya ke bai ɗaura komai ba, ya banko ƙofar.
Chapter 9 · 0% Book details