Sashe 10
Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na daÉ—e zaune yadda kuka san wadda aka dasa a wajen, gaba É—aya ban san dame zan kira abinda ya faru yanzu ba.
Har ya fito toilet ɗin ɗaure da towel a ƙugun shi, jikin sa sai maiƙo ya ke kamar ba wanka ya yi ba watsa ruwa ya yi.
Haka ya nufi kan gado, cikin mamaki naga ya É—auki kayan da ya cire jiya ya saka ba tare da ya goge jikin sa ba.
Yana sawa ya É—auki dardumar da ya yi cilli da ita, ya shimfiÉ—a cikin mamaki nake kallon shi ganin ba gabas ya kalla ba kuma ya tada Sallah.
Sai da ya yi raka'a biyu, ya daÉ—e bai É—ago ba.
Ba tare da sallama ba naga ya jawo wani dogon carbi ya fara ja.
In ba ƙarya nayi ba, ya fi awa yana zaune, dan ƙarshe tashi nayi na koma kan gado saboda yadda jikina ke amsawa, ga wani irin zazzaɓi da ke son rufe ni.
Duk da kuwa tarin yunwar da nake ji, amma nafi buƙatar hutu akan abincin.
Gani nayi ya ƙara tashi ya juya dardumar gabas, ya tada Sallah normal kamar yadda ake yi, ya yi sallama ya zauna cikin mamaki naga harda Alqur'ani ya ɗauka, tiryan-tiryan naji ya fara karatun Alqur'ani, babu ɓata ko gyara yana fitar da kowanne harafi dai-dai, sai dai salon karatun nashi Irin na yarabawa ne, yana yi ne kamar waƙa-waƙa.
Rasa wanne matsayi ya kamata na aje shi nayi, to ita waccan sallar da ya yi ya sunan ta? da uban carbin da ya dinga ja duk da ban san abinda ya ke cewa ba. Dan bakin sa ne kaÉ—ai ya ke motsi.
Yana gama karatu ya É—aga hannu ya yi addu'a ya shafa, ya tashi ya naÉ—e dardumar ya maida ta wajen ta.
Ganin ya nufo gadon nayi saurin runtse idanuna kamar mai barci.
Zama ya yi a gefen gadon, ya yi murrmushi me sauti tamkar bashi ba yace "Dama kin daina wahalar da kanki kin tashi, ba wani abu zan miki ba buƙatar hakan bata taso ba."
Ya ɗan ja bargon dana rufe rabin ƙafata dashi.
Da sauri na zabura na tashi ina zare ido. Ya kalle ni tare da fashewa da dariya abin takaici, ya shiga nuna ni yana faÉ—in "Matsoraciya wato yanzu kin banbance aya da tsakuwa kenan? Ni kinga fita zan yi, kuma ba daÉ—ewa zan yi ba dan haka in akwai abinda ki ke son ci ki faÉ—a min, sai na taho miki dashi dan nasan ba iya shiga kitchen za ki yi ba.
Kuma ki kasance cikin shiri dan muna da babban baƙo yau a gidannan, bana son ki yi wani abu da zai ɓata min rai ko ki ja min wata asarar kin ji na faɗa miki."
Gaba É—aya ban fahimci zan cen saba, sakamakon yadda ya yi maganar ta yadda ba zan fahimta É—in ba.
Dan ni ban fahimci asarar da ya ke nufi na ja masa ba, bare har na ƙara yanzu.
Dan haka na ja tsaki cike da tsiwa nace " Kai ka jiyo mugu azzalumi kawai, kuma abinci bana ci ka barni yunwar ta min abinda zata min."
Cikin fusata ya kawo hannu kamar zai dake ni, ko me ya tuna sai ya dunƙule hannun tare da cije baki cikin kakkausar murya yace "Daraja ɗaya ki ka ci, ke ɗin baƙuwa ce bayan haka jiya da daddare kin bani nishad'i duk da ba yadda na saba samu bane, amma sa'ar ki ɗaya na same ki da mutumcin ki. Da sannu za ki san ko ni waye, watarana ko an baki kuɗi akan ki min rashin kunya ba za ki min ba."
Yana gama faɗin haka ya miƙe, fuska a ɗaure ya fita daga ɗakin tare da bugo ƙofar.
Tsaki naja nabi bayan shi da harara, na maida kaina na kwantar ina jin tsanar shi na ƙara samun wajen zama a zuciyata.
****
Barci ne ya ɗauke ni mai nauyin gaske. Wata azababbiyar yunwa ce ta tashe ni yadda kuka san babu ƴaƴan hanji a ciki na. Da ƙyar na yunƙura na tashi ina jin ciwo a jikina har lokacin, na sauka gadon da dubara na nufi toilet, fitsari na yi na wanke fuskata na fito ina tafiya a hankali jikina duk ciwo ya ke min.
Farlo na fita, a buɗe na tarda ƙofar farlon naja tsaki na je na rufe.
Sai lokacin hankalina ya kai wajen Dining table sai naga kulolin abinci har biyu, sakamakon yunwar da nake ji sai naji wani daÉ—i a raina.
Ina buɗewa naga shinkafa ce fara, sai wake dafaffe ɗaya ƙaramar kular miya ce da ganda da kifi.
A zuciya nake faÉ—in
_Da sanyin safiyar nan aka dafa shinkafa_
Sai da na kalli agogo naga har É—aya ta gota, ashe barci nasha haka ban sani ba.
Kitchen na shiga na É—auki filet, na zuba shinkafar na sa iya kifin dan ganda bata wani dame Ni ba.
Ba dan daÉ—i ba naci abincin, dan miyar bata min yadda nake so ba.
Bayan na gama na wuce ɗaki, sai da na ƙara wanka na gasa jikina sosai na ɗaura alwala na fito. Sallah nayi na ɗan tattara ɗakin zuwa farlon.
Ban damu da wata kwalliya ba, dan banga abinda zan wa kwalliya ba duk da irin son gayuna kuwa.
Iya riga da sket na atamfa nasa abuna, ko É—aurin É—an kwallin ban wani tsaya ba kaina wahala ba haka na coke shi.
Wayata na É—auko na dawo farlo na zauna, sai na tarda miss call da yawa, harda na su Aunty Zulai da Abbanmu sai Mama Hajara ita ma kira biyu na gani nata.
Wata irin kunya na ji ta kamani, ban kyauta ba tunda su Aunty Zulai suka tafi da na kira sau ɗaya suka ce suna ilori ban ƙara kira ba.
Haka su Abbanmu tunda aka kawo ni, ban kira kowa ba, to ina naga kwanciyar hankali ma.
Kiran Abbanmu na fara yi, na gaida shi cike da ladabi. Ya amsa min yana faÉ—in "Babu kiran gida Rahamah, ko baki ji kewar mu ba?."
Idanuna ne naji sun ciki da ƙwalla, murya na rawa nace "Ka yi haƙuri Abba, fatan duk kuna lafiya yasu Amminmu da Mama Hajara, da su Yakubu da Ummi da Aminatu."
Amsa min ya yi kowa lafiya, nan ya shiga yi min nasiha akan zaman aure. Cikin mamaki sai naji yace "Al'amen ya kira ni yau, yana ta jera godiya, har ya turawa Baba Usman kuɗi har dubu ɗari uku wai a rabawa duka dangin mu, ya yaba da tarbiyyar ki da hankalin ki. Rahamah dan Allah na roƙe ki ki riƙe mijin ki hannu bibbiyu, daga gani mutumin kirki ne, kuɗin shi bai taɓa burge ni ba Rahamah, karki zauna da shi dan dukiyar shi ki zauna da shi dan Allah.
In sha Allahu ba za ki yi nadamar auren shi ba."
Ni dai sauraren Abba kawai, a zuciyata ina faÉ—in _Abba baku san wa kuka aura min bane._
Nan ya gama min nasiha, ya ƙara da ban haƙuri da lallashi akan zaman kaɗaici ya kuma ce baya son ya ji ance ga matsala daga ɓangarena.
Ina sallama da Abba nabi sauran kiran, nasha ƙorafi wajen Aunty Zulai akan ban kira ba.
Na dai bata haƙuri wannan ta wuce, na kira su Amminmu da ƙannena muka gaisa.
Ana kiran la'asar Islam É—in Aunty Fati ta shigo, bayan ta gaida ni ta bani abincin da Aunty Fati ta aiko ta kawo min.
Da ya ke bata wani sakewa dani, bata jima ba ta tafi abinta.
Kaiwa kitchen nayi ina jin daÉ—i, na huta da cin abincin waÉ—an can mutanen.
Wajajen magriba sai ga sallamar Al'amen, cikin mamaki nake kallon bayan shi ganin shi tare da wani mutumi sun shigo farlon kai tsaye ba tare da neman izini ba.
A rikice na fara neman É—ankwalina na É—aura, na haÉ—e rai sosai ganin mutumin ya zauna a kujerar dake fuskantar tawa, ya wani zuba min ido dake cike da kwalli kamar tsohon boka, ga wani uban carbi fari sai faman ja ya ke yana mui-mui da baki.
Kujerar da nake kai Al'amen ya zauna.
Ya wani É—ora min jabgegen hannun sa a kafaÉ—a, ya matso da fuskar shi saitin tawa yana wani lumshe ido shi a lallai sai ya nuna min love.
A takure nake sosai, dan kusan rabin cinyar shi akan tawa take. Dan kujerar me biyu ce shi kaɗai ma ya isa ya cinye ta. Kauda kaina nake ta faman yi, dan in ba ƙarya hanci na ya min ba kamar ina jiyo wari-wari na tashi a hammatar shi.
Ga ya kawo bakin sa dai-dai fuskata yana magana, sai feshin yawu ya ke min, iskar dake fita a bakin sa kanta na min wani irin wari wari.
Gaba É—aya zaman wajen a takure nake.
Gyaran murya mutumin ya yi yana wani ƙasa-ƙasa da ido yace "Jagaba a ɗan rage haka mana, bari mu gama magana in ya so in na tafi ayi soyayyar ko."
Ya ƙarasa maganar cikin ƴar ƙaramar dariya.
Washe baki Al'amen ya yi, babu zato naji ya yi kin kiss gefen kumatuna ya sake ni yana gyara zaman shi yace "Ai yarinyar ce Malam ke sa na rasa nutsuwata."
Dariya ya yi kaɗan ya gyara zaman hiramin shi, ya shiga ƙare min kallo yace "Ai babu laifi naga Kyakykyawace dai-dai da yadda nace maka."
Gaba É—aya rasa tunanin da ya kamata nayi nayi, anya Al'amen yasan meye Musulunci kuwa? In ya sani me yasa ya ke abubuwa kamar jahili, Ni kaina duka ya É—aure na rasa a wanne matsayi zan sa shi, wasu abubuwa nake gani a tare da shi, tun safiyar yau har zuwa yanzu waÉ—an da basu yi kama da koyarwar addinin Musulunci ba.
Tun daga kan ihun da ya min akan nayi Sallah, zuwa sallar da shi ya yi ba tare da ya kalli gabas ba. Zuwa wayar da ya yi da maganganun da ya faɗa min na karna ƙara ja masa asara. Sannan ga shigo min gida da ya yi kai tsaye da wannan mutumin da sam bai min kama da mutanen kirki ba, kama ya ke min da irin malaman tsubbu ɗin nan.