← Book details Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 22

Sashe 8

Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amsa masa ta yi da "Lafiya lau." Yasa hannu a aljihun jallabiyar shi, ya ciro kuɗi ya irga dubu uku ya miƙawa malam Iliya yace "Gashi ayi cefane ko."
Da sauri malam Iliya ya amsa yana mai jin daÉ—i a ransa, ya shiga rattaba godiya da fatan alkhairi.

Cikin jin daÉ—i Al'amen yaja motar ya fita a gidan, iya wannan ya ishe shi farin ciki, yaga ana nuna masa shi mutumin kirki ne, babu abinda ke bashi nishad'i bayan haka.

Kai tsaye Family hause ya nufa, idanunun shi cike da mararin ganin Rahamah, yana hasasowa kan shi yadda zai ganta yana son wannan tsiwar tata, ba ƙaramin kyau take masa ba in tana yi, ga wani irin ƙamshi na musamman da ya ji yana tashi a jikin ta a Jiya da ya rungume ta. So ya ke ya ƙara shaƙar k'amshin, tunda ya ke bai taɓa jin turare me daɗi da kwantar da zuciya ba irin wanda ta yi amfani da shi.

Yana cikin tuƙin wayar shi ta shiga ƙara, ganin sunan dake yawo a jikin fuskar wayar, ya ja tsaki tare da katse kiran ya cigaba da tuƙin. A ransa yana jin, a yanzu ko kira nawa number za tayi ba zai ɗauka ba, dan baya buƙatar abinda zai ruguza masa wannan farin cikin nashi.

*****

*RAHAMAH*

Tunda na kulle ƙofar farlon, na nufi bedroom ɗina na shiga shima na kulle shi ina sauke ajiyar zuciya.
Sai da naji hankalina ya ɗan kwanta, sannan na nufi toilet da nufin nayi wanka. Ina fitowa wanka na duba cikin kayana na ɗauki doguwar rigar abaya baƙa, bayan na gama shafe-shafe na na saka rigar, ɗankwalin abayar na ɗaura a kaina nabi lafiyar gado dan Ni kaina nasan jikina na buƙatar hutu.

Cikin barcin da nake, kamar a mafarki naji ana bugun ƙofar sama-sama.
Tsaki naja na maida kaina na kwantar, ina faɗin "Duk nacin ka duk maitar ka zaka gaji da bugu ka tafi, dan ni ba mahaukaciya bace da zan buɗe maka ƙofa."

Ba'a daina bugun ƙofar ba, babu jimawa kuma wayata ta fara ringing.
A hankali na jawo ta dan duba wake kiran. Ganin sunan Aunty Fati na É—auki kiran cikin Muryar barci nace "Aunty Fati."

Daga can taja tsaki tace "Wai ba za ki zo ki buɗe ƙofar ba, ina ta faman bugun ƙofa kin barni a tsaye."

Zabura nayi na tashi ina mutstsuka idona, na lalubi ɗankwalin da tuni ya kunce ya yi nashi wajen na ɗaura. Na sauka a gadon na nufi Ƙofa na fita.

Ina buɗe kofar farlon, naga Aunty Fati tsaye sanye Cikin hijabi har ƙasa, hannun ta riƙe da basket ɗin abinci sai gefen ta Kamal yaranta na biyu hannun sa riƙe da wata leda.

Yana ganina ya yo kaina cikin murna tare da É—ane jikina, yana faÉ—in "Aunty Rahamahtah."
Nima ɗaukar shi nayi duk da babu laifi yana da nauyi, dan a ƙalla zai kai shekara bakwai ga shi kuma yana da ɗan jiki kaɗan. Cikin murrmushi nace "Kamal ɗina ya kake ina Islam?."

Kokawar sauka ya shiga yi yana faÉ—in "Aunty Islam na gida, wai ita ba zata biyo mu ba tayi fushi tunda Mami bata kaita Kaduna ba."

Jan hannun shi nayi muka nufi ciki ina faɗin "Ka ƙyale Islam, zamu gauraya ne ba bata da kirki, yarinya sai zuciya kamar tsohuwar kuturwa."

Aunty Fati dake biye damu a baya, ta aje kwandon hannun ta tace "Ai ni na fahimci ma baki ganni ba Rahamah, wato ta É—an ki kike kenan."

Juyowa nayi na kalle ta, dai-dai lokacin dana ɗora Kamal a kujerar farlon nace "Ki yi haƙuri Aunty Fati, ina kwana."

Sai da ta cire hijabin jikinta ta zauna sannan tace "Lafiya lau, ya kwanan me gidan da kewar Æ´an tafiya."

"Lafiya lau Aunty, kamar kin san har na fara kewar su Aunty Zulai."

"Ai dole ki yi, yanzu na kira suka ce min sun yi nisa da tafiya."
Cewar Aunty Fati kenan.

"Allah ya sauke su lafiya." Nace hakan tare da komawa kujerar kusa da ita, muka shiga firar zumunci.
Ta janyo basket ɗin da ta zo da shi, ta firfito min da abincin data kawo min, Indome ce ta mata dahuwar ruwa-ruwa dan tasan cima ta kenan, taji kayan haɗi sosai sai tashin ƙamshi take.
Sai ɗayar da ta soya dankalin turawa ba tare da tasa ƙwai ba,sai stew da tayi daban wadda taji hanta, sai damamen kunun tsamiya wanda yaji kayan ƙamshi.
Duk cima ta ce ta sani, amma yanzu iya indomen nake da buƙata, sai kunun dana sha kaɗan.

Muna cikin hira na tuna ban rufe ƙofa ba, na tashi da sauri na nufi Ƙofar zan rufe.
Sai naga wata mata na ƙoƙarin shigowa, hannun ta riƙe da kuloli guda biyu.

Ta kalle ni tare da sakar min murrmushi tace "Amarya kin tashi lafiya, ya kwanan baƙunta."

Da "Lafiya" na amsa tare da miƙa mata hannu dan amsar kayan hannun ta, dan a ƙalla zata iya kaiwa sa'ar Aunty Zulai a shekaru.

Cewa tayi na barshi, na matsa ta shiga farlon.
Bayan sun gaisa da Aunty fati ta juya ta tafi.
Bayan tafiyar ta ina ƙoƙarin rufe ƙofa Aunty Fati tace karna rufe, bansan wanda zai zo ba, in barta a buɗe tunda gidan ba mu kaɗai bane.

Badan naso ba na bar ƙofar a buɗe, dan bana so ta fahimci akwai matsala ne kawai, da rufe ƙofar zan yi kawai.

Muna cikin fira sai ga Al'amen ya turo ƙofar, da sallama ɗauke a bakin sa ya shigo, hannun sa riƙe da wata baƙar jaka.
Bayan sun gaisa da Aunty Fati, ya nufi bedroom É—ina kai tsaye.

Ganin ina zaune ban motsa ba, yasa Aunty Fati ta galla min harara tace "Ke dai kam Rahamah baki da wayo, kina kallon mijin ki ya dawo, babu sannu da zuwa babu amsar kayan hannun shi ki kai masa ɗaki, ya shiga ɗakin ma madadin ki bishi kin ƙara gyara zaman ki."

ÆŠan turo baki gaba nayi, cikin narke murya nace "Aunty ba sai na bishi bafa, kuma zan masa sannu da zuwa gani nayi fa kina nan, kawai sai na tashi na wani amshi kayan hannun sa na shiga É—aki dan rashin kunya."

Tsaki taja tace "Ki ji min munafuncin banza.Ni dake wa zai ji kunyar wani, ina ce in Kika zo gidana kina zaune nake tashi, na tarbi Abban Islam na kuma shige É—akin wani lokacin ma bana fitowa sai ya yi wanka. Shine ke zaki faÉ—a min wani kunya ki ke j..."

Maganar tace ta katse, sakamakon jin Muryar Al'amen da muka yi yana kiran sunana "Rahamah Rahamah, kina ina ne?."

Dukan mu muka ɗaga kai tare muka kalli ƙofar bedroom ɗina, Al'amen ne tsaye ya zuro kanshi bakin ƙofar yana kirana.

Ƙasa-ƙasa Aunty Fati tayi da Muryar ta tace "Ai sai ki tashi ki je, daga nan in za ki tafi ki kai masa abincin nan, tunda nasan ba cinyewa za ki yi ba."

Cikin jin haushi na tashi na nufi basket É—in na É—auka, ina gunguni ina komai na nufi bedroom É—in.
Yana ganin na taho ya koma ciki, ya zauna bakin gadon yana wani washe baki.
Ban yarda na shiga ɗakin baki ɗaya ba, na coge a bakin ƙofa tare da ajiye basket ɗin hannuna, cikin turo baki murya a cunkushe nace "Ga abinci nan in zaka ci." Na juya da zummar barin ɗakin.

Muryar shi ce ta dakatar dani, cikin mamaki na juyo ina kallon shi.

"Rahamahtah dan Allah kar ki tafi yanzu,ki dawo ki É—an zauna karki sa Aunty Fati ta zargi wani abu. Wallahi ban yi niyar yi miki komai ba, babu abinda zan miki Allah kin ji ma na rantse."

Ba dan ya ce baya son Aunty Fati ta zargi wani abu ba, wallahi ba zan dawo ba. Dan dai kawai nima bana son tasan akwai matsalar ne, dan in akwai abinda na tsana shine ace wata matsala ta ɓullo daga ɓangarena.
Nafi son komai mu yi shi tsakanin mu, in yaso in yaji gashi da kanshi zai fita harkata kowa ya yi harkar shi.

Ban yarda na zauna can ciki ba, daga kan kujerar madubi dake bakin ƙofa na zauna, ya kalle ni cikin tausasa murya yace "Dan Allah ki saki ranki Rahamahtah, ki zuba min abincin naci yau hanci komai ba."

Ina kumbura baki ina komai, na zuba masa soyayyen dankalin da miya, ba tare dana tambaye shi ba na zuba masa kunun cike da wani ƙaton kofi.

Saukowa ya yi daga gadon, fuskar shi É—auke da murrmushi yana faÉ—in "Kai amma Nagode, amma kin san bana shan kunun tsamiya dan dai kawai daga hannun ki ya fito shi yasa zan sha."
Ya ƙarasa maganar tare da zama Ƙasan carpet ɗin dake malale a ɗakin, ya wani irin bajewa yana nishi da ƙyar.
Dana kalle shi sai da dariya ta kusa kama ni, dan zaman da ya yi sai ya zamana tumbin nasa shima ya zauna abin shi daban, kowa na har kar shi kenan.

Harara na galla masa na ɗauke kaina, ba tare da ya ganni ba ya shiga danna ƙatuwar loma.
Dankalin ma, in ba gizo idanuna suka min ba, kusan uku-uku ya dinga haɗawa yana turawa a ƙaton bakin sa.

Abin mamaki wanda yace baya shan kunun tsamiya, sai gashi ya zuƙe kunun tas, harda su lashe baki yana faɗin "Wallahi kuma kinga wannan da daɗi, ai nayi zaton irin kunun nan ne mara daɗi da zaki ji tsami kawai, gashi wannan harda ƙamshin su citta ya ke yi."
Ya É—ago ya kalle ni yace "Ke kika dama mana hala?"

Haushi da takaici da suka kama ni, yasa ban bashi amsa ba na share shi, nayi kamar ban ji abinda yace ba.

Shi kanshi yasan na ji nayi banza da shi, dan haka ya jinjina kai a ranshi yana cewa _Zan lallaɓa ki har na cimma burina, yarinya sai iskanci kala-kala dan kinga kina da kyau, kuma ina lallaɓa ki._

Yana gama ci na tattara kwanukan na fita. Aunty Fati na ganina ta shiga murmushi, tana ta yabona wai ko Ni fa, yanzu da naje ba yafi ba, ai da ita zai wa kallon babbar banza.
Chapter 8 · 0% Book details