Sashe 20
Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaki naja na dafa kujerar bakin ƙofa, na tafa hannayena da ƙarfi dan naga kamar bai san da shigowata ba.
Wata irin zabura ya yi, ya fara yunƙurin tashi zaune, ganina tsaye yasa ya washe baki yana faɗin "A'a baƙuwa nake da yau kenan? A me yasa baki shigo ba ƙaraso mana Rahamahtah."
Hararar kawai nake auna masa cike da jin haushi, sai wani washe dargajejen bakin sa ya ke kamar ganda.
Miƙo min hannu ya yi yana faɗin "Kin ga zo nan, waya taɓa ki naga kin shigo kina harara haka ko dai na zo ne, zo ki kama ni mu je bedroom naji matsalar taki a nutse."
Ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin miƙewa tsaye.
Ɗaga masa hannu nayi, zuciyata na min wani irin zafin ƙiyayyar shi nace "Dan Allah kaga dakata, ba abin da ya kawo ni wajen ka kenan ba, Allah ya min tsari da hakan ina neman tsari da ranar da zan kawo kaina gare ka.
Na zo ne na ji wa kake shirin kawo min farlona, naga ansa kaya Anisa tace budurwa zaka kawo min mu zauna tare, duk faÉ—in gidannan ka rasa ina zaka aje ta sai farlona."
Na ƙarasa cikin karaji, ji nake zuciyata kamar zata faso ƙirjina ta fito.
Miƙewa tsaye ya yi, ya shiga bina da wani ƙasƙantaccen kallo, sai da gabana ya faɗi dan ya koma min ainahin Al'amen ɗin dana sani tun na baya, amma gudun yaga kasawata yasa na dake ina bin shi da harara.
Takowa ya fara sai da ya kusa ƙarasowa inda nake, ya min nuni da ƙofa ranshi a matuƙar ɓace yace "Fice min a nan, Ni zaki kalla ki nemi tsari da zuwa gare ni? Me ma kika ɗauke ni ne Rahamah? To bari kiji da na ƙyale ki saboda ban ɗauki son ki gare ni wani abu ba, amma tunda har tsaurin idon ki ya kai ki zo wajena ki faɗa min haka, to Wallahi sai kin yi nadamar faɗar kalmomin da kika jefe ni dasu, kuma in kina ganin ba zaki iya zama da wata a farlon ki ba, sai ki ƙara gaba ban tilasta ki ki zauna dole ba."
Yana gama faÉ—ar haka, ya juya zai shige bedroom É—in sa na farlo.
Da sauri nasha gaban shi nace "Wallahi baka isa ka min wani abu ba, bayan nan zama nace ba zan zauna da wata a farlo na ba, kasan yadda zaka yi da ita amma ba wajena zata zauna ba."
"Bani hanya na wuce."
Shine abinda yace min cikin tsawa.
Ƙin matsawa nayi na ƙara tare hanya, nace sai ya wuce munje yasa an kwashe kayan an fitar.
Babu zato naji ya sa hannu ya hankaÉ—a ni baya, wata irin faÉ—uwa nayi Allah yasa na sa hannu na tare cikina, da kan cikin zan faÉ—a.
Ba tare da damuwa da abinda ya aikata ba, ya wuce ɗakin sa rai a ɓace.
Da ƙyar na yunƙura na tashi, sai na nemi kukan ma na rasa, ashe Al'amen bashi da hankali bai duba cikin jikina ba ya ture ni? Ina ɗingishi ina komai na nufi sashina, ni kaɗai nasan meke damun zuciyata.
***
*AL'AMEN.*
Haƙiƙa kalmar Rahamah da tace Allah ya kiyaye ta so shi, ta buge shi ba kaɗan ba. Me ta ɗauke shi kenan? Bai kai a soshi ba ko me?.
Tsayawa yayi a gaban madubi yana kallon kanshi, a hankali ya ke kallon kanshi tun daga fuskar shi, zuwa gangar jikin sa.
Shi kanshi yasan in ba kuÉ—i ba, ko abinda ake cewa so hana ganin laifi, to babu kyakykyawar mace kamar Rahamah da zata so mutum kamar shi.
Ya daɗe yana tsaye ƙarshe ya wuce ya ɗauki wayar shi, Number Mustapha ya kira ya faɗa masa duk abinda ke faruwa,
Ranshi na masa ciwo.
Daga can Mustapha yace "Gaskiya bata kyauta ba, shi yasa tun farko nace ka bari a mallake maka zuciyar ta, yadda bata isa ta tsallake maganar ka ba koda kuwa iyayen ta zasu tsaya suyi magana, in kayi taka to ita zata bi.
Amma ka ce a'a, gashi yanzu abin ya fara damun ka, tunda kaima kasan badan mun rufe bakin kowa ba da ko auren ba za'a baka ba bare ita ta zauna da kai."
Jinjina kai ya yi kamar Mustapha na gaban shi yace "Ai yanzu ya zama dole ta gane kuren ta, dole na azabtar da zuciyarta da rayuwar ta, so nake ta yi nadamar abinda ta aikata min, so nake ta dawo tamkar baiwa a gare ni, so nake duk wani abu in na ce shi za tayi, ina son na lalata rayuwar ta na ruguza farin cikin ta na ɗai-ɗai ta duk wani kyau da take taƙama dashi, ƙarshe ta dawo komai sai nace za tayi, ina son taji in babu ni ba zata iya rayuwa ba, ina son ka sa mata wani irin zazzafan sona a ranta wanda duk bugun numfashin ta, ya dinga hauhawa yana ƙaruwa.
Sai ta yi nadamar abinda ta min, a lokacin da nadamar ba zata amfanar da ita ba."
Jinjina kai Mustapha ya yi yana wata dariya yace "Da kyau, yanzu na yarda Jagaba ne a gabana, karka damu zan birkita tunanin ta da duk wata nutsuwar ta, sai ta dawo tamkar yadda kake son ta zama."
Ya É—an numfasa ya cigaba da magana "Yanzu abinda nake so da kai, dama kasan nace zan yi bincike akan mafitar kasuwancin ka."
"Eh mun yi haka, yanzu wacce mafita ka samo mana?."
Cewar Al'amen kenan, da yake jin ran shi fes jin batun, za'a sawa Rahamah son shi.
"To gaskiyar magana, iya binciken da nayi mafita ɗaya na hango, dole ne ka ƙara aure muddin kana son sirri, kuma ba wata zaka aura ba sai bazawara me ƴaƴa uku, kuma ta kasance me jiki a ƙalla ta fika jiki, sannan bayan ita dole ka dinga aure-aure a kai-akai, ta ukun ba'a so ta daɗe a gidan ka, sauran kuma zaka barsu amma duk wadda ta nemi tada ma hankali ka kore ta, sai kuma wani aure da zaka yi wanda shi zai kasance na biyar, ba wata zaka aura ba sai wadda take da kusanci da Rahamah sosai, dole dai wadda ta san Rahamah."
Da sauri Al'amen ya tari numfashin sa yace "Kana nufin sai na auri mataye da yawa har haka? Ta yaya za'a bani auren mata bayan an san ina saki, bayan nan me mutanen gari zasu É—auke ni? Kana ganin hakan ba matsala bane?."
"Ai mafitar kenan, dole kuma in kana son dukiyar ka ta É—ore sai kayi haka, dan ina hango fitintunu da yawa a gaban ka, in baka tashi tsaye ba sai ka dawo baka da ko sisi, maganar mutanen gari ka bar min komai a hannuna, babu me zargin ka kowa yabon ka zai na yi, in kaga an fara surutu kai ka so saboda haka ka rage yawan fushi kaima."
"Shikenan zan rage fushin, amma baka ganin taso da Maganar aure na yanzu ba zai zama cece kuce ba?."
Cewar Al'amen kenan.
"Eh to in kana ganin zai zama tuhuma gare ka, zai fi kyau ka tura ita Rahamah ɗin gidan yayarta, tunda dama kace tace ba zata zauna da Shukhra ba, in yaso sai na dakata da aikin da zan yi a kanta har sai bayan ka ƙara auren ka, a yadda take jin ƙiyayyar ka yanzu in ta tafi zata ce ba zata dawo ba.
Kaga sai ka fake da wannan ka ƙara auren ka, in yaso sai mu aiwatar da aikin mu cikin sauƙi, yadda zata dawo gare ka da ƙafarta tana neman yafiyar ka akan ka maida ta, kaga sai ka murza kambun sarautar ka yadda kake so."
Nan da nan Al'amen ya ji ya yi na'am da shawarar Mustapha, nan dai suka cigaba da tsara yadda zasu yi komai ba tare da an zarge su ba.
Daga ƙarshe ya ce, ya bawa Malam Mustapha wuƙa da nama, ya nemo masa bazawar irin wadda yace ana so, wato me jiki kuma me ƴaƴa uku.
Zuciyar Al'amen fes ya shige toilet, wanka ya fesa ya fito ya sa kaya harda su turare, kai tsaye sashin Rahamah ya shiga.
Bai ganta a farlo ba, dan haka ya wuce bedroom É—in ta kai tsaye.
Zaune nake bakin gado, na yi tagumi ina ta faman aikin nawa wato tunani, _Yanzu in nace zan bar gidan nan ma ina zani? Komawata Kaduna a wannan halin wani surutu zai zamewa iyayena, za'a ce na ƙi zaman aure duka wata nawa, sannan da cikin jikina zan kama hanya na tafi kenan? In naje aka tambaye ni me zance musu? Ni da ba iya magana nake ba ko an tambaye ni._
Ina nan ina zaune, in sak'a wancan in kwance komai nayi tunani naga ba mafita bace.
Shigowar sa da na ji yasa na ɗago na kalle shi, yana tsaye bakin ƙofa fuskar shi a haɗe ya dafe k'yauren yana kallona.
HaÉ—a ido muka yi, da sauri na É—auke kaina ina jin wata tsanar shi na taso min.
Cike da gadara ya fara magana "Ki tashi ki É—ora girki, dan yanzu zan je na dawo da Shukhra, bana so ta zo ta tarda gidan babu abinci tayi zaton banyi dacen mata ba, tunda ita bata aure ni ba abin ya zama abin dariya."
Ko motsawa ban yi ba, ina zaune kamar ba dani ya ke magana ba, ji nake kamar na tashi na zazzage shi ko zan ji sanyi a raina.
Magana ya ƙara yi cikin faɗa yace "Wai ina magana kin share ni, wato rainin dake tsakanin mu dake ya dawo kenan, sai anyi magana kice bakya sona bayan ga kishi nan kina yi ƙiri-ƙiri."