← Book details Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 22

Sashe 11

Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu dai ba wannan ke Amaryar mu wajen ki na zo takanas, nasan baki Sanni ba tunda yau kika fara gani na.
Ni sunana Malam Mustafa, Ni ne ke kula da duk wasu harkoki na cigaban kasuwancin mijin ki, Alhamdulillahi kuma ina alfahari da hakan, tunda kullum yana ƙara ganin buɗi da yalwa a cikin kasuwancin nasa dan yana taimako sosai a ciki."

Gaba ɗaya maganganun sa ƙara tsunduma ni cikin kogin tunani suka yi, magana ya cigaba da yi "To yanzu kin take wani Sharaɗin mu ne yau, amma bisa dole mun miki uzuri sakamakon rashin sani ne ya jawo hakan.
Ya kamata ace kafin ki yi sallah ki nemi izinin mijin ki, ya faÉ—a miki yadda za ki yi, sai kika kalli gabas kai tsaye ba tare da cika umarnin mu.
Ya kamata ace kin fara kallon arewa tukun, sannan ki ja carbi akwai addu'o'in dana koyar da shi, in ya koya miki sai ki yi su. To daga nan zaki iya sallar ki ki kalli gabas harma da sauran ibadun ki, muna dai so ace ita wadda ake kallon arewa É—in kika fara."

Gaba É—aya ji nayi jikina na wani irin rawa, nan da nan zuciyata ta fara min zafi. BuÉ—e baki na nayi da nufin sauke masa kwandon fitsara daga shi har wanda ya kawo shi. Sai dai muna haÉ—a ido jikina ya yi wani irin lak'was kamar an watsa min ruwa, yadda kuka san an sa makulli an kulle min baki gaba É—aya na kasa magana.
Sai faman raba ido da nake, zuciyata na wani irin zafi kamar ana hura min wuta a cikin ta.

*_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰 ✍🏻✍🏻_*
[1/18, 07:15] Ummu Sultan Ceh3: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EJJOOxsRu8dKh9gocmSFuG
*BAƘAR ZUCIYA!.*

*_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍🏻✍🏻_*

*_LITTAFIN KOWA YAƘI JI YA KAMMALA COMPLET GA DUK ME BUƘATA TA MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 09014644247_*

*PAGE6️⃣*

A Hankali nake bin su da kallo dukan su, ina sauraren bayanin da mutumin da ya kira kan shi da Malam ya ke.

"Kina jina Amarya. Yanzu tunda kin riga da kin ɓata mana cikin rashin sani, ki tashi ki yi alwala ki zo ki yi sallar a gaban mu, dan karki yi kuskure komai zai yi daidai."

Jinjina kai Al'amen ya yi, ya kalle ni ganin ban motsa ba har lokacin. Ya kama hannaye na duka biyun, yana bin fuskata da kallo cikin son na kalle shi yace "Rahamah ki tashi ki je ki yi alwala ki zo ki yi sallar kin ji."

Kauda kaina nayi ba tare dana kalle shi ba, so nake na buÉ—e baki na na ci musu mutumci, na faÉ—a musu su ji tsoron Allah amma na kasa hakan.
Bana jin duk abinda zai faru, zasu iya rinjayata na biye musu na aikata shirka, dan ni iya fahimta ta kenan shirka Al'amen ya ke aikatawa saboda neman duniya.

Cigaba ya yi da magana cikin lallashina "Rahamatah ki tashi ki je Please, ko ba kya son ki cigaba da more rayuwa ne?."

Yi nayi kamar ba da ni ya ke magana ba, a zuciyata nace _More rayuwa a ina? Mugu kawai cutar da rayuwa dai._
Daga ƙarshe da naga sun min rubdugu akan na tashi na yo alwala, sai na zare hannuna cikin nashi, na miƙe tsaye ba tare dana kalle su ba nace "Babu alwalar da zan yi na zo, ku cire rai zaku iya dilmiyar dani ni Rahamah bana haɗa Allah da kowa."
Ina gama faɗin haka na wuce bedroom na kulle ƙofar na bar mukullin a jiki, bakin gado na zauna ina sauke ajiyar zuciya.
Iya wannan maganar da na faɗa musu, ba ƙaramin ƙoƙari nayi ba wajen dakewa, ina faɗar maganar zuciyata na wani irin bugawar tsoron su duka biyun. Ni kaina nasan Allah ne ya bani iko kawai na iya faɗa.

Al'amen cike da tashin hankali ya fara kiran "Rahamah Rahamah! Ki dawo fa." Ya tashi da ƙyar ya bi bayan ta kafin ya ƙarasa ta rufe ƙofar.

Bugun ƙofar ya shiga kamar zai ɓalla ta, yana faɗin na zo na buɗe ko raina ya ɓaci.
Ina ji nayi shiru na ƙyale shi, ko me zai yi sai dai ya yi amma ba zan buɗe ƙofar nan ba Wallahi.

Ina jin lokacin da Mustapha ya zo bakin ƙofar, yana faɗin "Jagaba ƙyale ta, mu mata uzuri a bita a sannu watarana da kanta za ta yi ba sai ka sata ba, kaga taho mu tafi ka ji."

Da ƙyar ya janye Al'amen wanda ranshi ya kai ƙololuwar wajen ɓaci.
Ina jin shi yana faÉ—in "Za ki san ni kika wa gardama ai ba'a É—akin za ki dauwama."

Tsaki naja a zuciyata ina neman tsari daga sharrin su. Dai-dai nan na ji kiran sallar magriba, tashi nayi na É—auro alwala na tada Sallah.
Na daÉ—e ina addu'o'i akan Allah ya tsare ni daga kaidin Al'amen.

Dan na fuskanci dole sai na tashi tsaye da addu'a, wannan abin nashi ba lafiya ba, dole akwai wata ƙullalliya a ƙasa.
Amma nasan Allah shine kaÉ—ai zai yi maganin duk wani shirin su.
A fahimta ta kenan Aurena ma da Al'amen ya yi, bisa umarnin wannan mushrikin ne kenan? Danƙari ashe akwai matsala kenan da jan aiki a gabana.

Na daɗe zaune ina kaiwa Allah mai kowa mai komai kukana, har sai da aka kira sallar Isha'i na yi tare da shafa'i da wuturi. Ina jin yunwa amma naƙi fita saboda bana son ko ganin shi nayi bare wani abu ya haɗa mu.
Haka nayi wanka na É—aura alwala tare da shirin barci, nayi duk addu'o'in da annabinmu (S,a,w) ya koyar na shafe jikina na kwanta ina jin zuciyata cikin wani irin yanayi.

*****

*AL'AMEN*

Ranshi a matuƙar ɓace ya ke da abinda Rahamah ta masa, da ƙyar Malam Mustapha ya rarrashe shi suka fita.
Dama da motar Al'amen É—in suka zo, dan haka suka shiga dan ya maida Malam gida.

A hanya Al'amen dake tuƙi cikin fushi ya kalli Malam Mustapha yace "Na rantse da Allah kai ka dakatar dani, da sai yarinyar nan ta gane kuren ta."

Dafa kafaÉ—ar shi Mustapha ya yi yace "Kai matsalata da kai baka bin komai a sannu, karka manta ni ne wanda na shawo kan komai har ka samu ka auri yarinyar nan. Ko dai ka manta aikina ne, kar ka bari fushi ya jagoranci lamarin ka da yarinyar nan. Dan na fuskanci tana da É—an motsi a kanta, dan yadda ta mana yanzu alamu sun nuna ba ita kaÉ—ai bace. Zai iya yiwuwa tana da aljanu dan wannan kwallin dana sa a idona, babu halittar da zan kalla da shi bayan aljanu in basu umarni su take.
Dan haka yanzu mu je ga aiki na gaba, ita zamu dawo kanta."

Sai lokacin Al'amen ya ɗan ji dama-dama. Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Malam Mustapha yace "Amma kana ganin in aljanu ne da ita ba zasu dinga ɓata mana aiki ba?."

Jinjina kai malam Mustapha ya yi yace "Eh to gaskiya ban tabbatar su É—in bane, dan zargi nake ka bari na gama tabbatarwa tukun in ya so sai na duba naga waÉ—anne irin aljanu ne kafin na tantance komai."

Maida kan shi ya yi ya cigaba da tuƙin yana faɗin "Shikenan in ka yi binciken maji. Maganar ɗaya aikin na riga da na samu yarinyar tuni, yanzu haka anjima zan je sabon gida dan mun yi da Bukar zai kawo ta anjima, matsala ɗaya ce kawai bana son nayi dare a waje tunda kaga yarinyar nan na nan.
Gasu Hajiyar mu, bana so su zargi wani abu suga ban dawo da wuri ba."

Gyara zaman shi Mustapha ya yi yace "To me zai hana zuwa gobe ka tattara ta ku koma sabon gidan, kaga sai ka fi samun sakewa, tunda can a kwai É—akuna da sashin da ba kowa ma.
Dan gaskiya aikin mu na buƙatar lokaci."

Nan da nan ya yi na'am da wannan shawarar, ya amsa da "Hakan ya yi." Daidai lokacin da suka iso ƙofar gidan Malam Mustapha, gidane ƙarami irin na masu ƙaramin karfi, yana sauke shi ya buɗe ƴar ƙaramar ƙofar gidan ya shige. Al'amen ya juya kan motar ya ɗauki hanyar sabon gidan shi.

Koda ya shigar da motar, bayan sun gaisa da me gadin shi. Kai tsaye ya nufi ƙofar babban farlon shi.

Zaune ya tarda wani mutumi baƙi dogo,bashi da jiki kwata kwata irin siraran mutanen nan ne.
Gefen kujerar da ya ke kai, wata mace ce zaune tana da ɗan jiki kaɗan a ƙalla zata kai shekara talatin, fara ce amma daga gani farin mai ne.
Idanun ta a tsatstsaye suke daga gani irin marasa kunyar matan nan ne, sai faman taunar cingum take tana wani kwarkwasa.
Sanye take da wasu irin riga da sket na atamfa, waÉ—an da aka musu wani shegen É—inki duk kusan jikin ta a waje ya ke.

Hannu Al'amen ya miƙawa mutumin, wanda na ji ya kira da Bukar. Idanun shi akan yarinyar da ita ma ta ƙure shi da ido.

Bayan sun gaisa, Bukar ya miƙe yana nuna yarinyar yace "Gata nan dai Jagaba, nasan duk wani abu da kake buƙata zaka samu a gare ta, dan Sa'a bata da matsala ƙwararriya ce ta gaske."

Dariya Al'amen ya yi yana wani bin matar da kallon ƙasan ido, ya kalli Bukar tare da miƙa masa hannu suka ƙara gaisawa yace "To ka kyauta sosai, ta yi min nima kuma yadda nake so." Yasa hannu a aljihun sa ya ƙirga kuɗi dubu ashirin ya bawa Bukar.

Amsa ya yi yana washe baki, ya yi godiya ya juya tare da cewa yarinyar sai sun haÉ—u, ya fice daga farlon.

Al'amen kam nufar ta ya yi ya miƙa mata hannu, babu musu ta bashi nata tana wani irin kwarkwasa.
Kai tsaye saman bene suka nufa, ɗakin farko ya kaita ya rufe ƙofar.

***

*RAHAMAH.*

Can cikin barci na ji kamar ana shafa ni, zabura na yi na tashi zaune ina zazzare ido cikin duhun É—akin.
Ji nayi an ƙara kamo ni, ba sai an faɗa min ba, nasan Al'amen ne.
Sai dai ina mamakin yadda ya ke shigo min ɗaki, koda kuwa na rufe ƙofar na bar makullin.
Chapter 11 · 0% Book details