Sashe 17
Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaki naja cikin ɗaga murya raina a matuƙar ɓace nace "Kar na ƙara cin wannan alfarma da kake faɗa, Haba Al'amen ka ji tsoron Allah mana, me ka ke nema a duniya a yanzu da Allah bai maka ba? Me za ka yi da dukiya bayan wadda ka tara ? Wanne irin son zuciya da son duniya ka saka wa ranka da har ka ɗauki shirka a matsayin. Aikin ka.
Me ka ke so? Me ye baka samu ba, Wallahi ka guji ranar da Allah zai kama ka akan ayyukan ka, shirka kwata-kwata ba abin yi bace, duk cikin Laifuka shirka ita ce babban zunubin da Allah baya yafewa me yin ta muddin bai tuba ba ya mutu a cikin ta, duka duniyar guda nawa ce, me zaka tara wanda ba'a tara irin shi a duniyar nan ba, anyi biliyoyin ka a kuÉ—i mulki kai komai ma, dan ba kai ka fara ba anyi fiye da kai, duka suna ina yanzu? Duk sun tafi in da zasu amshi sakamon ayyukan su."
Cikin fitar hayyaci na cigaba da magana ina hawaye, dan na daɗe abin na cimin tuwo a ƙwarya, a duk sa'ar da nayi niyar faɗa masa gaskiya sai na ji kamar an rufe min baki.
Yau ne Allah ya bani iko na ji har bakina ya buɗe "Ka ji tsoron Allah. Ka ji tsoron Allah ba dan komai ba sai dan mutuwa bata sallama, bayan nan ka tausaya min ka duba ɗan dake kwance a marata, bana san ya fito duniya ya tarda irin muggan halayen k.." Kuka ne ya ci ƙarfi na, na zube a kan gwiwowina na fashe da wani rikitaccen kuka wanda ke fitowa daga ƙasan zuciyata.
Yana tsaye riƙe da robar kamar wanda ya ji nasihar da aka masa, ƙasan ransa kuwa wani irin ɓacin raine kwance.
Shi yarinyar nan zata kalla tace yana aikata shirka, ina shirkar da ya ke aikatawa? Shi bai ɗauki duk abinda ya ke a matsayin shirka ba tunda sadaka ce ake bashi , sai ɗan abinda baza'a rasa ba a cewar shi neman arziƙin bata yadda ba'a yi.
Dan haka ya ja tsaki ya kalle ni da har lokacin ina zube a ƙasa ina kuka yace "Karki ƙara kira na da mushriki, saboda ban aikata shirka sadaka ce nake yi karki ƙara haramta min sadaka ki kira ta da shirka."
Yana gama faɗar haka, ya wuce ni ya ƙarasa cikin kitchen ɗin, da kanshi ya shiga wanke naman kan, babu shiri na bar masa kitchen ɗin ina kuka na nufi ɗakina.
Shawara na dinga yi da zuciyata, akan na kira Aunty Fati na sanar mata halin da ake ciki.
Wata zuciyar kuma tace _In kin faÉ—a kamar kin tonawa kanki asiri ne._
Sai nayi kamar na kira ta sai na fasa, a haka har aka kira azahar na tashi na nufi toilet, wanka nayi na É—auro alwala na tada Sallah.
Hayaniyar da na fara ji a farfajiyar gidan, yasa na shafa addu'ata cikin hanzari na leƙa window.
Cike da mamaki nake kallon Al'amen, wanda ke zaune a kan kujerar roba kusa da bakin get, yara ne da yawa a gaban shi, da alama yaran almajirai ne duba da irin shigar dake jikin su.
Ganin kamar yana miƙa musu abu, yasa na fito farlo wajen window na leƙa ta baya tunda dama part ɗina shine na farko.
Faten wake ne a gaban shi, da naman kan ragon daya yi Farfesun shi, cikin mamaki nake kallon yadda ya ke zuba musu a roba, in ya zuba musu sai ya zari nera hamsin hamsin, waÉ—anda ke kujerar gefen shi, sai ya haÉ—a da goro ya basu su amsa suna godiya su tafi.
Ji nayi kaina na wani irin sarawa, wanne irin abu kenan tunda nake ban taɓa ganin kwamachala irin wannan ba.
Kamar wadda aka mintsina na juya cikin hanzari na koma ɗaki, wayata na ɗauka na danna number aunty Fati, cikin kuka nace "Wallahi Wallahi Aunty na gama zama da mutumin nan, ni Kaduna zan tafi ba zan ƙara awa ɗaya a gidan shi ba."
Ina gama faÉ—in haka na yanke wayar, nayi wurgi da ita akan gadon na fashe da wani irin kuka me cin rai.
Ina kallon yadda take kirana naƙi ɗauka, ta jera min kira yafi goma data gaji ta daina kira.
A can kuwa hankalin Aunty Fati ba ƙaramin tashi ya yi ba, jin abinda ƙanwar tata tace.
Gashi taƙi ɗaukar kiran ta bare ta ji lafiya, ita kaɗai take faɗin "Na rasa gane me ke damun yarinyar nan, ayi mutum kamar me aljanu ko ƙiyayya hauka ce."
Dan ita yanayin maganganun da Rahamah take akan mijinta, bata fahimtar su tana bata abin a dunƙule bata fahimtar komai,
Iya abinda idanun ta suka gani da shi take amfani.
Dan haka ganin taƙi ɗaukar kiran, bisa dole ta kira mijinta tace zata gidan Rahamah ta duba ta bata jin daɗi.
Cewa ta jira shi ya zo ya kaita, ji take ba zata iya jira ba, haka ta tattara yaran ta kaisu gidan dake jikin nata, Matar gidan nada mutumci sosai, suna zumunci da ita ita ma bahaushiya ce.
Ganin yadda Aunty Fatin ke ta sauri yasa tace "Ni kuwa Maman Islam ina za ki haka? Naga kamar bakya tare da nutsuwar ki."
Da ya ke wani lokacin suna É—an tattauna matsalolin dake damun su, sai ta É—an ja tsaki tana tafiya tace "Ki bari na dawo Aunty Zainab zan faÉ—a miki."
Da yake ta girme mata, shi yasa take kiran ta da Aunty.
Mashin ta tara, dan bata jin zata iya tsayawa ta jira mijin ta da yace zai dawo ya kaita.
Asalima bata so yasan me ke tafiya a gidan ƙanwar tata.
Ina zaune a inda nake ko motsawa banyi ba, naji sallamar Aunty Fati.
Kwanciyata nayi na juyawa ƙofar shigowa baya.
Yanzu Al'amen ya shigo muka gama cashewa da shi, na tata masa rashin mutuncina, ya fita ranshi a matuƙar ɓace, wai ashe yana ƙoƙarin shigowa ya ji ina waya da Aunty Fati, shine wai me yasa zan kirata? Na kira ta nace Babu komai karta zo, shine nace ba zan kira ba harda mari na ya yi ƙarshe, ya fice yana faɗar maganganu.
***
*AL'AMEN.*
Ba ƙaramin tashi hankalin sa ya yi ba, lokacin da ya zo ya tarda Rahamah na waya da Aunty Fati tana faɗin zata bar gidan shi.
Tambayar kan shi ya shiga yi _Taya haka ta kasance? bayan Malam ya tabbatar masa ta shigo gidan sa kenan babu fita, ita ce makullin arziƙin sa ya riga daya mallake masa ita ba zata iya zuwa ko'ina ba._
Shine yanzu ya ji tana batun tafiya, da sauri ya shiga ya ce ta kira tace karta zo, da taƙi shine ya mare ta ya fita ranshi a ɓace.
Bai zarce ko ina ba sai gidan Malam Mustapha, kiran shi ya yi a waya, sai gashi ya fito yana wani ƙoƙƙobarewa.
Ko gaisawa ba su yi ba ya kora masa bayani, cikin mamaki da ya kama Mustapha yace "Kana nufin ta fara maganar rabuwa? Lallai akwai aiki a gaban mu, na faÉ—a maka yarinyar nan nada aljanu baka yarda ba, gashi yanzu suna neman juya mata tunani su cuce mu.
Bayan kasan ita ce ƙarfin arziƙin ka, bari na shiga gida na fito dole a rufe mata baki karta ja mana aiki."
Yana gama faɗin haka ya juya ya shiga gida, dawowa ya yi hannun sa riƙe da wani magani.
Miƙawa Al'amen ya yi yace "Ungo wuce muje ka samu kuɗi ƴan nera goma-goma sai a barbaɗa maganin, in dai anyi haka sai a raba su ga yara na kan hanya.
Ana yi ba zata iya tona maka asiri ba, ko ta yi niya bakinta zai yi nauyi.
Haka kuwa suka yi, suka fita ya samo canjin a wajen wani me shago dake aje masa canji musamman, sun yi Sa'a an taso yara Æ´an makaranta, haka suka dinga raba musu kuÉ—in nan suna gamawa suka juya.
Ya cewa Al'amen "Kafin ka koma gida yanzu ba anjima ba, ka kira Iyayen ta ka gaishe su ka É—an tura musu wani abu ta account É—in yayanta, tunda kace shi kaÉ—ai ka ke da shi kuma in kace zaka tura suna hanawa, karka faÉ—a musu sai ka tura, sai kace a rabawa yara ba su ka bawa ba."
Tsaki Al'amen yaja yace "Kasan abinda ke ƙona min rai da mutanen nan, da zarar nace na tura kuɗi sai su ce basa so, su fatan su na riƙe musu ƴar su amana da gaskiya."
Cikin nuna ƴar damuwa yace "Gaskiya Malam ina tsoron ranar da zasu san halina, har ga Allah na fara ƙaunar Rahamah dan yarinyar ta kai a sota, kawai dai son da nake mata ba zai hana in gudanar da manufofina ba."
ÆŠan dafa shi Malam Mustapha ya yi yace "Karka damu dan so dama nasan zaka iya son ta, amma ka bi a hankali kar ya sa ka fara taka sharruÉ—an da na kafa maka.
Batun iyayen ta ka aje shi a gefe, su waÉ—an nan kasan basu damu da duniya ba na riga dana gama rufe bakin su, kar ka yi fargaba akan asirin ka zai tonu, muddin ina tare da kai hakan ba zata faru ba."
Sai lokacin Al'amen ya ji hankalin sa ya É—an kwanta, nan Mustapha yace masa, ya wuce ya koma wajen hidimar sa, babu abinda zai faru.
Haka ya sauke shi a ƙofar gidan shi, ya juya yana sauke ajiyar zuciya ya kama hanyar kasuwa.
***
*RAHAMAH.*
Tambayar duniya Aunty Fati ta min, akan na faÉ—a mata matsala ta na kira ta na tada mata hankali.
Babu abinda nake sai kuka, naƙi furta mata komai sai cewa da nake "Wallahi na gama zama da shi tafiya zan yi, gashi dai ina son in faɗa amma na kasa.
Ƙarshe haushi na bawa Aunty Fati, ta miƙe tace "Rahamah ni zan tafi, Allah ya yaye miki abinda ke damun ki, zan kira su Abba na faɗa musu ga irin iskancin da ki ke wa mijin ki, in yaso in wani abun ne nasan su ba zaki ɓoye musu ba.