← Book details Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 22

Sashe 15

Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abin mamaki ganin Aunty Fati, sai ya fara washe baki ya shiga gaida ta.
Amsa masa ta yi babu yabo babu fallasa.

Sakin baki nayi kawai ina kallon salon makirci irin na wannan mutumin, ganin yadda ya ƙaraso kaina yana wani narke fuska, yana faɗin "Sannu Rahamatah. Ya jikin naki?."

Gaba É—aya kaina ya kulle, a zuciyata nace _Dama ba mata kaÉ—ai suka iya munafurci ba, harda maza kenan._

Ganin haka yasa Aunty Fati kallon shi tace "Ya kamata mu kaita asibiti, dan jikin nata ya yi zafi da yawa."

Cikin nuna damuwar data bayyana a fuskar shi sosai, ya miƙe yana faɗin "Ina zuwa bari na je na shirya."

Bayan tafiyar shi Aunty Fati ta kalle ni tace "Rahamah ki ka ce ya nuna bai san baki da lafiya ba, bayan gashi ya nuna damuwa akan ki sosai, ki ga harda abinci ya siyo mi ki."

Shiru na mata kawai, na ma rasa me zance mata.
Ban ga amfanin yi mata bayani ba, dan nasan bama zata fahimce Ni ba.
Tunda fuskar daya nuna mata ta kirki, tasa ta manta halin da ta zo ta same ni.

Ganin na yi shiru yasa tace "Ni dai ina faɗa mi ki Rahamah, ki ji tsoron Allah. Babu ruwan Allah da rashin son da kika ce bakya yiwa mutumin nan. Mijin ki ne, in kika ɓata masa Allah ba zai bar haƙƙin sa da kika ci ba. Saboda haka ki bi a hankali kin ji na faɗa miki."

Ganin Al'amen ya fito, dole tayi shiru.
Harda su Hijabina ya É—auko, yana ta rawar jiki yana jeramin sannu.
Aunty Fati ce ta taimaka min na tashi.

Yana ganin haka ya matso wai zai riƙe ni, tuna bala'in da nake shaƙa a jikin sa yasa na ƙwace na maida kaina jikin Aunty Fati.

Bai ce komai ba ya matsa, muka fita muka shiga mota yaja muka nufi asibiti.
Ina jikin Aunty Fati a kwance, ji nake kamar nace ta wuce dani gidan ta. Ko zan huta da rayuwa da wannan makirin mutumin me fuska biyu.

*_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍🏻✍🏻_*
[1/18, 07:15] Ummu Sultan Ceh3: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EJJOOxsRu8dKh9gocmSFuG

*BAƘAR ZUCIYA!.*

*_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_*

*_LITTAFIN KOWA YAƘI JI YA KAMMALA COMPLET GA DUK ME BUƘATA TA MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 09014644247_*

*PAGE 8️⃣*

Tun da muka baro asibitin, kuka kawai nake kamar wadda aka sanarwa da saƙon mutuwa.
Na fara kukan ne tun sa'ar da likita ya faÉ—i kalmar data tafi da É—an sauran farin cikin da ya rage min a rayuwa.
Ni Rahamah ni Rahamah, ace ina É—auke da ciki cikin ma na wannan mugun azzalumin. "Ya Allah." Na furta hakan a fili.

Na fuskanci daga shi uban gayya, da tunda aka sanar da samuwar cikin ya ke washe baki.
Da ita Aunty Fati da ke ta faman aikin lallashi, babu wanda ya fahimci kukan baƙin ciki nake.
Duk tunanin su farin ciki yasa nake kuka, saboda Aunty Fati ta sanni da shegen son yara.
Eh tabbas ina son yara a rayuwata, sai dai duk da irin son da nake musu, ban yi fatan samun haihuwa da wannan mutumin ba.
Wanda nake wa kallon mugu kuma azzalu, me halin dabbobi.

Sai gashi ashe ni ina tawa ne, Allah kuma na nashi Allah ya riga daya ƙaddara sai na samu rabo da shi.
Tunda gashi ina É—auke da cikin shi, har na tsawon sati biyu.

Ganin kukan yaƙi ƙarewa kamar ana daɗa tunzurani, Aunty Fati da ta fara zargin kukan ƙiyayyar cikin nake.
Ta É—an ture kaina daga jikin ta tace "Wai ke Rahamah haka ake yi fisabilillahi, dama in mace ta samu ciki kuka take ba farin ciki da addu'ar su rabu lafiya ba take?."

Maida kaina na ƙara yi kafaɗar ta, na cigaba da kukana kamar ba dani take magana ba.

Al'amen dake tuƙi kam zuciyar sa fes take, tun sa'ar da likita ya sanar da samuwar ciki ga Rahamah, ya ji wani daɗi ya ratsa shi.
Allah ya sani yana son ace yau shima ga ɗan shi an nuna ance ɗan Jagaba ne, koba komai hakan ƙarin daraja ne da kima a gare shi a matsayin sa na mutum na mutane.

Jin da ya yi Aunty Fati nawa Rahamah magana, hakan yasa ya juyo ya kalle su yana murmushi yace "Ki bar ta ta yi kukan farin ciki ne, kin san dama tace min tana addu'ar Allah yasa ta samu ciki kusa. Ashe ma abin ya na tare da ita bamu Sani ba."
Ya ƙarasa faɗar hakan yana kallona, dai-dai lokacin da na ɗago ina kallon shi, cikin mamakin jin ƙaryar da
min ido-da ido ba kunya bare tsoron Allah.
Idanun shi fes a cikin nawa, babu ko alamar kunya a ciki ko nuna ba haka bane.

Ji nayi kamar na buÉ—e baki na danna masa zagi, sai dai hakan ba tarbiyyar da aka É—ora ni a kai bace.
Wani munafikin murmushi ya sakar min, ya ɗauke kan shi ya cigaba da tuƙi kamar wani na Allah.

Harara nabi bayan shi da shi, babu shiri na nemi kukan da nake na rasa.
A zuciyata nake faÉ—in _Lallai wannan mutumin lamarin sa ya wuce_ _tunina, wani abin in ya shirya ko ni da nake mace bana tunanin zan iya shiryawa._

Mun sha kwantar gidan Aunty Fati kenan, maganar shi ta ratso kunne na yace "Am yawwa Aunty Fati, ina son dan Allah kiwa Rahamah magana.
Kar ta dinga shan maltina madara, da yawan cin ƙwai, dan tana da jarabar son ƙwai kullum sai ta soya taci.
Ni kuma bana son abinda zai jawo yaron cikin ta ya yi girman da har sai an mata aiki, kin san abubuwan nan na kumbura yara su yi girman da ya wuce misali."

Tunda ya fara magana Aunty Fati take kallon shi, a ranta take faÉ—in
_Ikon Allah yau naga abinda ya fi karfina, Ni Fatima. Cikin da bai kai ko wata ɗaya bane ake sawa doka har haka? To Allah ya jiƙan mu mu da muke shan ta kullum_
Nan ta tuna cikin Islama kullum bata da wata cima sai ƙwai, maltina kuma ita ta zama kamar ruwan shanta.
Kuma babu abinda ya same ta ko babyn, asalima Islam ba tayi wani girman ku zo mu gani ba, lafiya ta haifi Æ´ar ta ba tare da komai ba.

Jin dukan mu mun yi shiru, hakan yasa ya juyo yace " Aunty ki yi haƙuri fa, na faɗi hakan ne dan ki mata magana ta rage, gani nayi bai dace ace tana ci kullum ba.
Tunda har likitoci sun ce suna hura yaro."

Murmushin yaƙe Aunty Fati ta yi, ta kalle shi tace "Karka damu zan mata magana, amma ni a ganina abubuwan da ka lissafa babu abinda suke sa yaro, sai ƙarin lafiya da kuzari ko a asibiti likitoci na cewa a yawaita cin dafaffen ƙwai."

Nan da nan ya haÉ—e rai, cikin cunkushashshiyar murya alamar ranshi bai so tace hakan ba yace "Ni dai abinda nace kenan, ki faÉ—a mata bana so ta jamin aiki dan ba son aiki nake ba.
Gwara ta haifa da kanta kawai."

Bansan lokacin da na ja tsaki ba, da sauri ya juyo ya kalle ni daidai lokacin da muka ƙaraso ƙofar gidan Aunty Fati.

A bakin get ya yi parking gaba É—aya fuskar shi a haÉ—e, ba sai ji na yi Aunty Fati tace "Am Jagaba Ina so ka barta a nan ta É—an huta, in yaso zuwa dare sai ka biyo ka É—auke ta ku tafi."
Bata jira cewar shi ba, ta kama hannuna ta buÉ—e motar muka fita.
Raina fes, ji nake kamar an cire min ƙaya, dama ace in na shiga gidan ta ba zan ƙara komawa gidan shi.

Ganin har taja hannun ta, ba tare da ta jira izini daga gare shi ba, hakan ya ɓata masa rai.
Kamar yace bai yarda ba, ko me ya tuna sai ya washe baki yace "To shikenan Aunty, an jima dai daga anyi sallar Isha'i ta shiry, zan zo mu tafi.
Ban jira ya ƙarasa maganar shi ba, na zare hannuna ana Aunty Fati nayi gaba.
Ina jin su suna sallama, yana jaddada mata ta kula dani sosai, kar ta bari nayi abinda zai taɓa cikin jikina.

A zuciyata nace _Sarkin rashin kunya, ayi mutum babu ta ido ba kunya bare kara._

Shigowar Aunty Fati tuni na cire Hijabina, na baje a kan carpet ɗin dake malale a farlon, ina shan sanyin fankar dana ƙure.
Jina nake yau kamar na samu wani Æ´ancin kaina ne, kafin ya zo ya yanke min jin daÉ—i na ya maida ni cikin fursun É—in gidan shi.

Zama Aunty Fati tayi a kan kujerar dake gefen inda na kwanta, ta kalle ni tare da aje jakar ta wajen ƙafata tace "A gaskiya Rahamah kina fama, wannan mijin naki na fuskanci sam bashi da kunya, ki ga daga samun ciki har ya fara rawar jiki abinka da ba saban ba. To an daɗe ba'a yi aure ba, yanzu har ga shi za'a samu ɗan kai, ko wane likita ne yace masa ba'a cin ƙwai da shan maltina da madara in an samu ciki?."

Ɗan kama ƙafar kujerar da take kai nayi, na miƙe zaune tare da faɗin "Wash, na gaji wallahi."
Na juyo gaba É—aya na fuskance ta nace "Ke iya rashin kunya kika fahimta a tare da shi kenan?."

Jinjina min kai tayi tace "Ƙwarai Rahamah bashi da kunya, ko dan shi ɗin ba bahaushe bane oho?."

"Uhmm tunda abinda ki ka fahimta kenan, ina roƙon Allah ya bayyana sauran halayen shi, yadda kowa zai fahimce shi bama ke kaɗai ba."

Da sauri ta dafani, cikin nuna ƴar zaƙuwar ta da son in bata amsa tace "Waɗan ne irin halaye ya ke dasu Rahamah?."

Haka kawai naji na kasa ce mata komai, sai kawai na tsinci kaina da girgiza kai nace "Babu komai addu'a ce na yi, ina fatan kuma Allah ya amsa."

Ajiyar zuciya ta sauke, tare da jan tsaki tace "Har kin faÉ—ar min da gaba wallahi, nayi zaton wani abunne daban.
Allah ya shirya ki Rahmah, na fuskanci har yanzu akwai wauta a tare dake."
Chapter 15 · 0% Book details